Chapter 7

1K 76 2
                                    

A kullum dan adam yana da mafarkai wanda yake da burin wata rana su zama gaske, haka dan adam, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a rayuwarsa wadanda zai yi burin a ce mafarki ne yake.

Wannan shine abinda Dauda yayi burin a ce mafarki yake, da ganin wannan rana dan uwansa a kan matarsa.

Sanadin ranar da ake yi mai zafi da sanya kishi, Dauda ya ajiye aikin da yake yi, ya nufi cikin rumfar hutu dake cikin masana'antar domin samun ruwan da zai jika makoshinsa. Yayi mamaki na rashin ganin Idrisa, bai kawo komai ba a ransa yaje yasha ruwa ya cigaba da aikinsa. Tunawa yayi da abinda ya faru tsakanin shi da Idrisa, da alwashin da Idrisa yasha na sai yayi masa abinda har ya mutu ba zai manta dashi ba. "Tabbas zai iya aikata abinda yayi niya." ya fada a zuciyarshi. Tunawa yayi da ya ganshi lokacin da yake fita daga masana'antar, alhali kuma lokacin tashi daga aiki bai yi ba. "Jinah!" yada cikin tashin hankali, bai tsaya wani dogon tunani ba yaje ya fadawa mahaifinsa zai je gida.

Lokacin da yazo gida ya nemi Jinah ko'ina bai ganta ba, haka shima Idrisa bai ganshi ba. Tunani kala-kala yayi tayi, ga kuma zuciyasa dake tsananta buguwa. Dakin Idrisa ya nufa, ya tarar da dakin a kulle. Juyawa yayi da niyyar dubawa makota, amma sai ya fasa da ya tuna babu inda Jinah take zuwa. Yana nan tsaye bakin kofar dakin Idrisan, sai ga Surayya 'yar yayarshi.

-Surayya baki ga Jinah ba?

-A'a ban ganta ba!

-Kawunki fah Idrisa?

-Dazu na ganshi ya shiga dakinsa.

-Yauwa to jeka abinka.

Ya fada kafin ya nufi dakin auntinshi wadda ke da duk wani sifayen yan makullayen dakunan gidan. Kusan sau biyar yana kwankwasa kofar kafin ta bude, fuskarta alamar bacci.

-Ya aka yi ne?
Ta fada cikin yanayin bacin rai da tunanin ko wasar da Dauda ya saba yi mata ne. Dan idan yayi niyyar yi mata shakiyanci, da ya bubbuga mata kofa ta bude, sai yace mata ai yayi makuwar daki ne. Murmushi yayi da ya fahimci abinda take nufi.

-Baba ne ya aikoni daukan kayan aiki da suke dakin Idrisa, sai dai na manta ban karbo makullin dakin ba, shine nake son ki bani na hannunki na bude.

Yayi mata karya, ita kuwa bata yi tunanin komai ba ta dauko masa makullin. Yaje ya bude kofar gabansa na dukan uku-uku. Jiri ne ya debeshi, Da sauri ya koma ya rufe kofar, kafafuwansa kasa daukanshi suka yi, ja da baya yayi ya jingina da bango.
Bai taba tunanin tsanar da Idrisa ke nuna masa zai kai ya iya aikatawa matarsa wannan danyen aiki ba. Karasawa yayi, kokarin ture Idrisa yayi daga bisa gadon, ya girgiza ganin Idrisa ya fado kasa kamar gawa. Dan tun farko bai lura Idrisa bai motsi ba. Wani mugun kunci ne ya turnukeshi ganin matarshi ba kaya, jikin da ya dade yana mafarkin gani amma bai taba tunanin a irin wannan yanayin ba. Idanun Jinah a rufe suke, alamar tana bacci, anan ya fahimci sumar da ita ne Idrisa yayi, kayanta ya saka mata sannan ya dauketa ya kaita har  dakinsu ya shimfideta kan gado.

Komawa yayi dakin dan uwan nashi da har yanzu yake kwance a kasa. Nan fah hankalinshi ya tashi, kunnensa ya kara a kirjin Idrisa anan yaji zuciyarshi bata bugawa. A hankali ya sakama dan uwan nashi wando, sannan ya ya barshi anan kwance. Bai rufe dakin ba, yaje ya kaiwa auntynshi makullin.

Kada Ashanti (godiyarshi) yayi, nesa da gida. Yayi hakan ne ko zai manta tare da rage damuwar abinda ya faru. Abinda dan uwansa yayi ko yake kokarin yiwa matarshi, ko kuma mutuwar dan uwan nashi bai san wane ne yafi masa ciwo ba.

Bayan yayi tafiya mai nisa, ya juya ya koma gida. Tarar da gidan yayi makil da mutane, dan kusan kowa yana nan, sai dai abinda ya bashi mamaki babu alamun an yi mutuwa a gidan, sauke ajiyar zuciya dan yana tunanin wata kil Idrisa ba mutuwa yayi ba. Daki ya nufa dan ganin ko Jinah ta farka. Tarar da ita yayi ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gado, sam baya jin dadin ganin matarshi kuma abar kaunarshi cikin damuwa.

 JINAH (Matar Aljani)Where stories live. Discover now