Chapter 23

580 55 2
                                    

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by  Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 23

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Fally ganin duka 'ya'yanshi kwance ba a hayyacinsu ba, ji yayi kasa ta kasa daukanshi, ya kasa yin numfashi da kyau, iskar shaka na neman ta gagareshi. Ya amince da wadda sam bai kamata ya yarda da ita ba. A cikin ransa yace ta yaya na yarda da wannan matar, matar da ita tayi sanadin mutuwar mahaifiyata. A yanzu ya gane irin kuskuren da ya tabka.

A daidai lokacin ne suka dunguma zuwa asibitin kauyen, Jinah bata daina kuka ba, duk tabi ta firgice, suna zuwa likitoci suka sanar dasu yaran suna numfashi.

Kallon Fally Jinah tayi anan ta tuna da hakurin da yake bata dazu.

-Fally me ka aikata ne?

Ta tambayeshi da alamun tuhuma.

-Ina son ki dawo gareni ne, mu sake raya soyayyar mu, ina son mu koma kamar da ne.

-Fally ka fada min, me ka aikata? Wannan karon muryar Jinah cike take da zafi da kuma rashin tsoro.

-Dole mu hakura da daya daga cikin su, Hindu....

-Innalillahi Fally! Me yasa ita? Ta yaya kayi hakan? Ka maido min da yarana Fally! Ba ruwana da koma me zaka yi, ni yarana kawai nake so!

Jinah ta fada kafin ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kokarin rungumeta Fally yayi amma ta goce tareda furta :

-Ka tafi, kada ka kara sako kafar ka anan, ba tare da ka dawo min da yarana ba! Bana kaunar ganin ka kafin nan!

Bai yi wata-wata ba ya bace daga wurin, zuciyarshi na kuna ganin zai rasa daya daga cikin 'ya'yansa gashi kuma zai rasa wadda yake yaruwa domin ta, bayan duk wasu wahalhalu da yasha a baya da sadaukarwar da yayi. Yanke shawarar yaje yaga Hindu yayi, sai dai wata matsalar bai ma san ko ta yaya zai ganinta ba. Koma dai meye zai yi iya kokarinsa yaga ya nemota ta karya abinda tayi. To kuma idan yayi hakan su zasu rayu ne? Tambayar da yayi wa kanshi kenan. Koma dai meye  zai je ya nemi Hindu ta san abinda zata yi.

Jinah ce zaune kan benci dake madakatar jiran likita kamar jaririn da yake jiran a haifeshi haka take. Taci kuka iya kuka ta yanda har idanun nata sun kafe babu ko digon hawaye. Duk dakikar da zata shude,sai taji wani abu ya soki zuciyarta.

-Zasu tashi.

Abinda Sarah da su Abdul ke ta maimaita mata kenan, domin likitoci sun tabbatar masu da yan biyu ba mutuwa suka yi ba, sun fita hayyacinsu ne, kuma likitocin na sa ran cetonsu. Ita kuwa Jinah tasan ba zasu iya yin komai ba domin ba kamar kowanne irin ciwo bane.

Kamar an tsikareta ta mike tare da fita daga asibitin. Da gudu Sarah tabi bayanta, ta tsayar da ita.

-Ina zaki je ne?

-Kar ki damu Sarah, yanzu na dawo, kawai ina son na samu natsuwa ne.

-Bari na rakaki.

-A'a dan Allah, ni kadai nake son tafiya.

-Amma...

-Dan Allah...

-Shikenan kar ki dade.

 JINAH (Matar Aljani)Where stories live. Discover now