9&10

385 23 19
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     *MR ARROGANT*
  _The story about young police man_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

      *STORY AND WRITTEN*
                _BY_
           *REAL ESHAA ~*

               *WATTPAD*
                  _Realeshaa_

*FREEDOM  ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

    *PAGE 9&10*🖊️

___________________📖Cikin takun 'kasaita yashiga sashen su batare dayayi sallama ba direct parlour ta yanufa zaune yasa mesu ita da salim,salman, se aysha,dakuma laila dasauri aysha tace inayini ya MD "lfy ya'amsa ata'kaice" salman dake kusa dashi yami'ka masa hannu sukayi musabaha.Aransu kuwa tunani suke meya kawoshi sashen sun sande nan  bawajen zuwansa bane"inna kuwa cikinta ba'karamin 'duran ruwa yayiba dan tasan zuwan natane ta tabbata wannan sakaran yarinyar tace ita tagani lokacin da haya'ki yatashi a'dakin Abbu  duk sanda yasa wannan shegiyar glass din nasa ba mutunci bane dashi hakama ya ya'kare bare yasa wannan eye glass din.Katse mata tunani yayi dacewa meyesa kika sakawa abbu haya'ki a'daki??bayan kinsa bayaso kuma meye hujjarki na sanyawar? ya'fada yana murtu'ke fuskarsa wanda babu alamun rahma acikinta tamkar na wanda aka aikowa da sa'kon mutuwa uwarshi.


"In banda 'kugi babu abinda cikin inna keyi ga zufa dake zubo mata duk da sanyi dake 'dakin tasan yau mai 'kwatarta se Allah tunda harya tako 'kafansa yashigo tasan baida farillan mutunci gashi bagirmanta yake ganiba tunda tariga tazubar dashi" aysha da salman kan sunkuyar dakai sukayi cike da jin kunyar hali irin na Inna. Mi'kewa salim yayi rai a'bace duk da tsoron dakuma fargaban dake cinsa behanashi cewa ya isheka haka  ya MD baza kazo har sashen mu kace zaka cimana zarafin uwa ba bazeyiba inhar yaya salman baze Iya dakatar dakaiba saboda besan darajar taba toni zan dakatar dakai cikin 'karfin hali yake maganan dan ba'karamin shakkar sa yakeba"aikuwa be gama magana ba yaji saukan wasu tagwayen mari Wanda ya'dauke jinsa da ganinsa na wucen gadi.


Kallonsa MD yayi ta cikin glass din dake fuskarsa domin ba'abin da yatsana irin raini daga na'kasa dashi sannan kuma akan gaskiyarsa araina masa wayo.Mi'kewa salim yayi cikin 'karfin hali daniyyar rama Marin da MD yaimasa cikin zafin nama irin nasu na police wa MD yakai mai naushi ahanci sannan yasa kafa yakorfoshi Sega salim baje akasa hancinsa najini"dasauri Inna ta taso ganin MD na neman illata mata 'da  sannu tsinanne Wanda besan mutunciba aiko mutuwa najin kunyar idon uwa bare kai.Kallon daya matane yahanata 'karasa abinda tayi niyar fa'da dan ba'karamin 'kwarjini yayi mata ba" yace wlh duk time danike magana wannan sakaran 'dan naki yasake sanya min baki sena 'dauki tsatsa-tsauran mataki akansa ke kuma yanuna ta da hannu kijira haduwar mu batare daya jira jin amsarsuba yayi ficewarsa.

Dariyan she'kiyanci laila tafashe dashi ganin yanda salim yabaje a'kasa kamar wani 'dan kaciya ga hancinsa na fidda jini sewani zazzare ido yake"Afusace yataso yayo kanta danyasan dashi take wannan dariyar iskanci hannu ya'daga daniyar she'ka mata mari.Ri'ke hannun tayi cike da isgilanci tace wayyo!!dan Allah ya salim karka dakeni kaji bazan 'karaba ta'karashe maganan tana fashewa da dariya,Ha'de fuska tayi kamar ba itace me dariyar ba wlh inkayi kuskuren marina zakayi dana sani lusari kawai Wanda besan meyakeba aikamata yayi kagwada 'karfinka akan namiji bani ba yanzu MD yagama baka kashi anan anma baka tankaba inhar kacika kai jarume ne kaje kasa meshi karama abinda yamaka baka tsaya kana hura hanci ba tana gama fa'din haka tayi wurgi da hannunsa sannan tabar wajen.Haushi da takaicine suka cika inna da salim ga 'diban albarkan da MD yai musu sannan ga tijaran da laila tasake yi musu"janyo hannunsa tayi suka nufi 'dakinta tanata bas@  hakuri akan tasan mataki daza ta'dauka akan sa. tsaki laila tayi sannan tawuce 'daki tana mita. Yarage daga  salman se aysha akabari a parlour kallonsa aysha tayi tace everlasting tashi mu tafi 'daki Murmushi yayi sannan yace angama gimbiyar mata 'daukan ta yayi suka nufi part din su tun kafin Inna tadawo ta sau'ke haushin su akanta.


*****
Komawa tayi  tai sallama seda ya'dau mintuna biyu kafin yabata izin shiga gefe dashi tasamu tazauna. tana zama yajuyo da kallonsa gareta, Inaso kibani aron hankalinki dan magana me muhimmanci nikeso muyi dake zama ta gyara tance ina sauraronka.Gyaran murya yayi yace nayanke bikin jahida da mubin nanda sati biyu saboda 'kulla zumunci dakuma cika al'kawarin dana 'dauka inaso daga yanzu kifara shiryata tamkar yanda ake yiwa kowasu 'ya'yan gata inaso ayi bikin da duk fa'din cikin Maiduguri ba'a ta'ba irinsa domin bikin 'ya'yan gata za'ayi gidana dake jiddari zasu zauna akwai komai na more rayuwa acan inkuma tace bataso sekishirya kuje Dubai ko Italy da ita taza'bi abinda ranta keso saboda bikin kece reni za'ayi Wanda kaf Nigeria ba'a ta'ba irinsa ba ina so duk Inda mutane suka taru ya zamto babu hiran daza'anayi sena bikin.

"Kallonsa take cike da mamaki dakuma sankai irin nasa waize ha'da jahida da mubin aure impossible tafurta cikin ranta inde tanada iko  kuma tana numfashi aduniya wannan auren baza'ayishiba.Kallonsa tayi cikin sanyin murya tace aganina inde akace za'ayi wannan auren to akwai cutar wa domin jahida batason mubin shima mubin basan jahida yake sede sha'awarta aganina  kajanye maganan auren nan saboda kar azo ayi abinda zamuyi danasani me makon a ha'da zumunci sekuma araba .

Tunda tafara magana yake binta da wani matsiyacin kallo lalle fadeela bantabbatar dacewa ke sha-sha sha bace Mara mutanin se yau toh wlh babu abinda zesa infasa wannan auren koda jahida mutuwa tayi se an'daura da gawatan balle kee kewacece da harzaki yimin katsa landan dan kawai na'fada miki toh wlh baki isaba fice min a'daki kafin na illataki ya 'karashe yana nishi kaman wani kububuwa.

Mi'kewa aunty fadeela tayi cike da takaicin hali irinna uncle Kabeer shi babu abinda yasani face sankai indai tana darai dakuma lafiya wannan auren baza ayishiba" Wuce jahida da zayya dake tahira abinsu cikin nishadi tayi batare datayi musu magana ba.Cike da mamaki jahida tace meyasami  aunty fadeela kinga kaman ranta a'bace ko kallon mu batayi ba mi'kewa jahida tayi tace zanje intambayi uncle Kabeer meyasami aunty kekuma kije kitambayo mana aunty"A'a lovely sis kibari base muntam bayesuba saboda hakan kaman shishigine acikin al'amarinsu kinsan tsakanin mata da miji"jinjina kai jahida tayi alamar gansuwa" toh allah yasa de lfy cewar zayya"ameen" jahida ta'amsa.nande suka ci gaba da hiransu cike da 'kaunar junansu se manghariba suka mike kowacce tawuce 'dakinta dan gabatar da sallah.

Aunty fadeela nashiga 'daki tafara tufka da warwara ta ina zata 'bullowa al'amarin dan Sam bataga dacewar jahida da mubin ba duk da ba ita tahaifi jahida ba anma baza tabari wani Abu yasame taba dan amanace awurinta kuma tasan girman amana...!!!

   
*WACCE JAHIDA ????*


     *ESHAA CE~*🤙🏻

MR ARROGANTWhere stories live. Discover now