69&70

299 18 0
                                    

*MR ARROGANT*
_(The story about young police man)_

*STORY AND WRITTEN*
           _BY_
*REAL ESHAA*

*WATTPAD*
_Realeshaa~_

*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

     *PAGE 69&70*🖊️

_________________________________📖 *Asalina* :
Malam bilyaminu mai albasa haifaffen garin Gaidam ne dake jahar yobe"mafiya yawan mazauna garin sun ta'allakane akan nomar albasa domin Allah yasanya musu albarka acikin nomanta.malam bilyaminu yana 'daya daga cikin manoman garin Wanda kuma Allah yasanya masa albarka acikin sa"Malam bilyaminu cikekken 'dan gaidam ne'matarsa 'daya mesuna saratu,Allah ya azurtasu da 'ya'ya biyu maza, Ibrahim da Yusuf"Ibrahim shine babba se Yusuf mebi masa Suntaso cikin so da 'kaunar junansu."Allah yasanyawa Malam bilyaminu albarka acikin sana'ar albasan ba'inda ba'asanshiba acikin garin Gaidam,gari gari ake zuwa sarin albasa,yanakuma turawa,wajaje daban daban kama daga Niger cikin garin damaturu Maiduguri kano kaduna wajaje da dama yake aikawa dashi buhu buhu,Cikin ikon Allah da antura yake karewa sannan a aiko masa da ku'dinsa.

Ibrahim da yusuf suntaso Cikin so da kaunar mahaifansu kasancewar su biyu suka haifa,tindaga kansu iyayensu basu sake samun haihuwa ba.Ibrahim da Yusuf suntaso cikin so da 'kaunar junansu shida 'dan uwansu,tunsuna yara basa son abinda ze batawa 'daya rai komai 'kan'kan tarsa. iyayensu sunbasu cikakkiyar tarbiya Wanda yakamata duk wasu iyaye nagari subawa 'ya'yan su,inda suka sanyasu amakarantar boko dana mahammadiyya,duk da awannan lokacin bakowane kesanya 'ya'yan sa amakarantar boko ba anma Malam bilyaminu yasanya 'ya'yan sa domin yanada burin sugirma suzama wani Abu acikin rayuwarsu yanda al'ummah zasu amfana dasu suzamto abin kwatance acikin acikin garin.maifina yamaida hankali sosai akaratun sa inda yakaranci fanni business domin sana'ar kasuwanci yafi burgesa kamar yanda mahaifinsa Malam bilyaminu keyi, baya sha'awar aikin gwamnati koka'dan wannan dalilene yasa mahaifansa goya masa baya akan  karatun sa  dayake domin yasamu yacimma burinsa na kasuwanci."
Yusuf kuwa tun tasowarsu bashida ra'ayin kasuwanci kamar yanda mahaifinsa keyi"bega abin burgewa acikin kasuwanci ba da haryarin jayi  yayansa yakeso aganinsa bazeyi karatu ba sannan yazo Yana sake wahalar dakansa wajen Neman ku'di, yafi bu'katan tunda yayi karatu yasamu aikin 'dan sanda yanda duk 'karshen wata albashi zena shigo masa,batare da wani wahala ba sannan yakare rayukan al'ummah.Iyayensa sungoya masa baya akan abinda yake so, anma sunce yabari ya kammala koda NCE ne se ane me masa aikin yanda zefito da matsayi,ba amatsayin coustable ba" Sam yusuf ya'ki yarda yace shide abarsa yaje da kwalin secondary indan yaso seyaci gaba da karatun yana aiki.kasancewar Malam bilyaminu da matarsa saratu mutane masu matu'kar sau'kin kai da bawa 'ya'yan su muhimmanci akan abinda sukeso yasa su amin cewa da bu'katansa tare dayimasa fatan alkhairi toh haka Yusuf yatattara yatafi training na police cike da kewan iyayensa dakuma yayansa Wanda suka matu'kar shaku dajuna tamkar wasu abokai."
Toh akwana atashi bawuya awajen Allah Yusuf yaje training yadawo lafiya inda yadawo gida amatsayin coustable,iyayensa da 'dan uwansa suntayashi farin ciki 'sosai akan cikon burinsa.
Allah yasanya wa Ibrahim albarka acikin kasuwancin sa, daya fara inda harya ke nema yazarce mahaifinsa daukaka afannin kasuwanci domin shi hargari gari yake zuwa da kansa"inda harkan yafi tafiya masa yanda yakama ta acikin garin Maiduguri harya ke saran wataran zekoma can baki 'daya."Bayan wani lokaci ne Yusuf yabijiro wa da iyayensa maganan aure yakeso dan akwai yarinyar dasuka daidaita da ita ance manya sushigo lamarin.sosai iyayensa sukayi farin ciki,dan burinsu bewuce ace yayansu sunsamu abokan zama nagari ba.Sede Malam bilyaminu suka katse sa kan cewa yabari yayansa yakawo mata se aha'da su rana 'daya a aurar, yusuf ya'amince da maganan iyayensa domin shima bazeso yariga yayan nasa aure ba zeso su tare rana 'daya"toh koda Ibrahim yadawo daga kasuwa iyayensa suka sheda masa da bu'katan da Yusuf yazo dashi sannan suma ga abinda suka yanke.Cike da kunya Ibrahim yasheda musu cewar akwai yarin yar dayake so shima asalinsu 'yan Niger sukazo Gaidam Neman ku'di anma Allah yayiwa iyayenta rasuwa bada'dewa agidan me unguwar dasuka sauka anan take dazama shi yake ri'ke da ita tamkar 'yarsa.kasancewar Malam bilyaminu da matarsa saratu mutanene masu matu'kar mutunci da sanin darajar 'dan Adam yasa suka amince da batun Ibrahim batare da kyarar rashin asalin yarinyar ba,cikin dattako da kamala Malam Ibrahim yace ha'ki'ka naji da'din wannan bayanin naka insha Allah zansa ayi bincike akansu kuma baza'a 'dauki lokaci ba za'ayi bikin cike da kunya Ibrahim yami'ke yafice daga 'dakin yanamusu godiya kana yanajin kaunar mahaifan sa.
"Koda Malam bilyaminu yasa amasa bincike akan yaran da 'ya'yan sa keson aure"se fadeela tasamu kyakykyawar sheda daga mutanen unguwar su dakuma wa'anda suka zauna gida 'daya kowa nayabonta yake saboda kyawawan halayyarta nutsuwar da 'dabi'unta bazaka ta'ba ganin ance ga abokin fa'dan taba."
Koda sukaje bincikan halin yarinyar da Yusuf keso se akasamu sa'bani domin anyi musu shedar rashin haku'ri ga asiri acikinsu duk Wanda ya aure su se sun mallakesa, uwa uba rabi bata da kunya daganin mutuncin naga da ita hakane yasanya yawa Malam bilyaminu gwiwa koda yadawo gida zayyanewa  matarsa Saratu yanda akayi sejikinta yayi sanyi,da abin" domin kanaganin kashi da rana da dare bazaka takaba dan ba'ayi wa su Rabi shedan arzikiba koda Ibrahim da Yusuf sukadawo aka zayyanewa kowa halin da ake cike se Yusuf yace yahakura da Rabi zenemi wata inyaso ayi bikin yayansa tunda ba'asamu Martsala tafannin saba"kai Ibrahim yagirgiza yace a'a zejira sa yanemi wata mai nutsuwa idan yaso se ayibikin tare"Sosai iyayensu ke farin ciki da hadin kan 'ya'yansu dakuma 'kaunar junansu.Bayan wata biyu gaba'daya Yusuf yafita asabgar rabi yadena zuwa zance wajen ta yadena kulata ko office din su taje seya 'buya yace ace mata bayanan inkuma tazo tasameshi baze kulataba"Ganin abin nasa da wula'kancin ne yasa Rabi zuwa hargidansu yusuf dan shedawa mahaifiyarsa sannan tabasa hakuri ko wani lefi tamasa.Zaune tasamu tasamu mama Saratu tana gyaran shin kafa,bayan sungaisane rabi tazayyanewa mama Saratu abinda ketafe da ita numfasawa Mama Saratu tayi sannan tabata hakuri akan ta ha'kura da Yusuf. koda Jin haka se Rabi tami'ke cike da rashin kunya tace toh mama inkin isa kihana aurena da Yusuf in gani dan yanzu nafahimci kece bakyason auren kuma baki isaba,tana gama fadin haka tayi tsaki tare da ficewa" Cike da mamaki mama Saratu tabita da kallo aranta tace ta Allah bataki ba,bata'dauki maganan Rabi da muhimmanci ba domin azatonta irin rashin kunyar tashen balaga ke damunta duk da kuwa talura Sam yarinyar batada tarbiya."Yusuf yasamu yarinya mai nutsuwa da tarbiya wacce tafito daga tsatson kamilallun mutane"inda aka sanya biki watanni hu'du masu zuwa,sosai Yusuf keson rahila saboda tarbiyanta da nutsuwarta.
Koda Rabi tasamu labarin auren Yusuf ba'karamin hauka tayi agida ba tatayarwa da mahaifiyar ta hankali kanse kandole se Yusuf ya aureta,koda hanne mahaifiyar Rabi taga yanda hankalin 'yarta yatashi seta shirya tsaf domin samawa 'yarta mafita domin Rabi ba'karamin San Yusuf takeba,hanne batada WO gida dawuriba se bayan sallan isha'i,abinda boka yabata yace tabawa Rabi tsakiyar dare misalin karfe 2am taura wuta tajefa tana kiran sunan Yusuf aciki,duk inda yake hankalinsa zedawo gareta"haka Rabi ta'aikata kamar yanda aka fa'da mata kotsoron dare batayi duk da karancin shekarunta domin a lokacin bazata wuce 23 years ba _(ya Allah ubangiji katsaremu daga aikata shirka da sa'bawa ubangiji mu masuyima Allah kashiryar dasu)_.
"Washe gari:dasafe Yusuf yatashi da wani irin kaunar Rabi dason ganinta" bayan sungama karyawane suka shiga hira cike da so da 'kaunar junansu anma banda Yusuf dayazabga tagumi,kallonsa Ibrahim yayi Cike da kulawa yace meyasameka ne Yusuf naga kamar baka da lafiya" 'budar bakin Yusuf sewawa yayi  baba ni Rabi nakeso a'auramin,ba rahila ba ya'fada,babu alaman wasa atattare dashi"cike da mamaki duk suka kallesa jin abinda yace sunma rasa mezasuce ganin babu alaman wasa atattare da maganan sa.Ibrahim ne yayi karfin halin cewa Yusuf kasan meka kecewa kuwa?anma de kanasane da yau saura wata 'daya bikinka da rahila,shine kake kawowa mutane shirmen banza bayan kasan mugayen halayyarta kuma kai da kanka kace kafasa ai,"afusace Yusuf ya'daga wa Ibrahim hannu yace Yaya inde bazakamin fatan alkhairi ba toh ka kyaleni anma auren rabi ba gudu baja da baya tunda nizan zauna da ita bawani ze zauna min da ita ba,yana gama fadin haka yafice daga gidan a matu'kar fusace"cike da mamaki iyayen nasu ke kallonsu abinda be ta'ba kasancewa atsakaninsu ba kenan anma yau dubi yanda yake daga masa murya lalle da lauje cikin na'di."
Duk yanda suke zaton Yusuf abin yaci tura domin yadena ci yadena sha kowajen aiki yadena zuwa kullum maganarsa rabi ko bacci yake sunan rabi ne abakin sa iyayensa da Yayansa ba'karamin tashin hankali sukashigaba ganin yanda Yusuf ya susuce akan rabi."koda Malam bilyaminu yaga dansa na Neman zaucewa akan Rabi kawai seya amince da a'aura masa ita,duk sunyi na'am da wannan shawaran dan atunaninsu hakan shine mafita"mama Saratu nashiga daki tafashe da kuka cike da tausayin halin da  'dan ta yashiga domin yanzu maganganun rabi kedawo mata akai.Washe gari Malam bilyaminu yaje yasamu magabatan rabi akayi magana da yayan babanta  kasancewar mahaifinta yarasu akatsaida kwanakin biki wata 'daya masu zuwa.

*****
Bayan Aure: Ibrahim da amaryarsa fadeela sosai sukayi farin ciki da rana me tarin albarka ranan dasuka mallaki juna amatsayin mata da miji gida me kyan gaske yagina dede rufin asirin sa 'dakuna biyu ne manya manya se kitchen da ban'daki atsakar gida dakuma rijiya cikin gidan anshafe da cement,mai unguwa yayi kokari wajen yiwa fadeela kayan 'daki kamar yanda zeyima 'yar cikinsa haka yamata."Yusuf yatare da amarensa rahila da rabi,iyayen rahila sunyi mata kaya masa kyau dede 'karfinsu"rabi kuwa bawani kayan kirki aka mata ba dan mahaifinta yarasu 'yan uwansa kuwa ba ha'din kai bane dasu gashi asanya biki a'kurarren lokaci,wannan yasanya tsanar rahila sake nunkuwa azuciyar rabi takuma ci alwashin fitar da ita agidan kotawani hali."Soyayya me tsafta fadeela da Ibrahim suke gudanarwa,tari'ke iyayensa tamkar nata inde taje gidan bata barin mama Saratu tayi komai kowani ita takeyi kama daga girki,wanke-wanke,shara wankin kaya"kowani aiki inde fadeela taje gidan batabarin mama Saratu tayi takeyi wannan yakara mata kima da daraja aidanun surakanta shiyasa suke alfahari da ita,rahila ma tanada kokari sosai inde taje tana temaka musu da aiki.Rayuwa tayiwa Rahila zafi agidan Yusuf ba'karamin azabtar da ita sukeba da wahala kala kala Yusuf yanajin ba'kinciki abinda suke aikata wa rahila a'kasar zuciyar sa sede baze iya tunkaran rabi ba dan wani irinshakkarta yakeji."Rana 'daya rabi ta tayarwa da Yusuf hankali kan cewa seyasaki rahila yanaji yana gani yasaki rahila badan yanaso ba sede dan Bayan da zeyi,ba'a farin ciki da saki anma rahila da iyayenta sunyi matu'kar farin ciki da sakin saboda azabtar da ita dasuke"rabi duniya yadawo sabuwa cin karenta take babu babbbaka inbataga damaba Yusuf be isa yaje gidan suba seda izinin rabi duk irin cin mutuncin da rabi keyiwa iyayensa yana gani sede be isa yace kanzir ba akai.Ibrahim abin nakona masa rai ganin rashin mutunci da rabi keshukawa,bataagawa uban kowa hakanne yasa yakira Yusuf domin yamasa fa'da akan abinda rabi ke aikatawa dakuma sakin rahila dayayi"kuka Yusuf yafashe dashi yace wlh Yaya ina matu'kar kaunar rahila sede bazan iya tsallake maganan rabi ba dan Allah kutayani da addu'a nima Kaine bansan meyake damuna ba"Sosai Ibrahim yatausayawa kanin sa yakuma yi alwashin insha Allah ze temakawa kanin nasa yaku'butar dashi daga sharrin rabi...

      _VOTE COMMENT AND SHARE_✅

          *_ESHAA CE~_*🤙🏻

MR ARROGANTTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang