81&82

304 15 1
                                    

*MR ARROGANT*
_(The story about young police man)_

*STORY AND WRITTEN*
           _BY_
*REAL ESHAA*

*WATTPAD*
_Realeshaa~_

*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

'''Barka da cika shekara sittin dasamun 'yanci kai.Happy independent Nigeria people🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬'''

'''I dedecited this page to my younger brother MUHAMMAD KAREEM (MK) wishing you Beautiful wife and so so so. may Allah bless your life'''🤭🤭🤭

*And*

'''NAZIFI YAREEMA'''
_(N-yareema)ina maka fatan alkhairi_

     *PAGE 81&82*🖊️

_________________________________📖Shiru 'dakin taron yayi tamkar bawani mahaluki dake numfashi acikinsa kowa da abinda yake sa'kawa aransa kan maganan alkali,'Dakin yayi shiru na tsawon mintuna goma Wanda Har al'kali yafidda ran jin amsar su.Abbu ne yanumfasa cike da farin ciki yace hakika ranka shi da'de nayi matu'kar farin ciki dajin wannan shawaran naka kuma muna fatan Allah ubangiji yasanya alkhairi atattare da wannan kalamai naka Allah ya tabbatar da alkhairin daya keciki sannan yakawar daduk wani sharri daze kusan tosa."bababa ma kai yajinjina Cike da gamsu da shawarar alkali kana da Murmushi afuskar sa menuni da zallan farin ciki yace yalla'bai ha'ki'ka nima nayi matu'kar farin ciki dajin wannan maganan naka domin nima nada'de da hango dacewar hakan sede ban furtaba sakamakon wasu dalilai,salman ma Murmushi yayi yace gaskiya hakan  yadace muna kuma fatan alkhairi aciki."Aunty fadeela wani farin ciki ne yalullu'beta jin maganan da alkali yayi sede ko afuskarta bata nuna alamar hakanba domin tun shigowarta kotun talura da kallon da Abbu dasu inna rabi kebinta dashi tayi kamar batasan Allah yayi halittarsu awajen ba kallo 'daya tamusu takawar dakai,yanzuma talura da mayen kallon da Abbu ke binta dashi anma ta'dauke kanta tamkar batasan yanayi ba,dan ko kallon sa bata 'kaunar yi" shima mubin sunkuyar da kai 'kasa yayi yana jin wani irin kishi nataso masa tamkar yahadiye zuciya sede koda wasa benuna ba sema sunkuyar dakai dayayi a'kasa tamkar ruwa yacinyeshi, kunyar hada ido da Jahida yake dan abinda mahaifinsa ya aikata ba'karamin kun yatashi yayi a idanun duniyaba,Yanzu haka ma da 'kyar aunty fadeela tararrashe shi kan yashigo dakin taron domin Jahida batada yayan daya wucesa."Gyaran murya alkali yayi yana maida Kallonsa kan aunty fadeela da mubin dasukayi 'kasa dakansu kowa natofa albarkanci bakinsa anma banda su,'dagowa sukayi suka maida hankalin su kan alkali,gyaran murya alkali yakara akaro nabiyu yace Hajiya muna magana keda 'danki bakuce komaiba kode baku amince da shawaran damuka yanke bane??domin ba muji ra'ayinku dangane da shawaran namu ba"Gauron numfashi aunty fadeela tasauke cike da ladabi tace yame girma mai shari'a bawai banyi farin ciki da maganarka bane anma ina Neman alfarmarman da aji ra'ayin 'yata tukunna domin banason abinda ze'kuntatawa rayuwarta mairainiyace kuma amana tace banason abinda zesata cikin damuwa ta'fada cike da ladabi"Murmushin su namanya alkali yayi yace karkidamu insha Allah baza'asamu matsala ba domin inahango soyayyar junansu acikin kwayar idanunsu,shiru aunty fadeela da mubin sukayi baza kaga ne yanayinda dasuke cikiba farin ciki ko akasin haka "Murmushi alkali yayi yace kun amince kenan??"Allah yasanya alkhairi kawai suka iya furtawa"Cike da farin ciki alkali yace alhamdulillah sannan yasanya hannun acikin l a'aljihu yaciro ku'di kimanin naira dubu 'dari biyu yace,yana kara fara'ar fuskarsa yace ga sadakinta yamikawa mubin domin shine alwalinta.kar'ba yayi hawaye nataruwa a idanunsa,yasan Jahida tayi masa nisa. Nisan dabaze iya cimmataba, koda ance za'a auramasa ita ayanzu baze yadda ba dan besan dawani ido ze kalleta ba insun haifi yara sukatambayi kakansu na wajen uwa taya ze iya cemusu mahaifinsa yakashe su,Abbu ba'karamin farin ciki sukayi ba bayan sun dawo cikin kotun ne akasallami duka matan suka fice daga ciki.atake dubban jama'an dake cikin kotun suka sheda 'daurin auren Rabi'atu jabir jammaina tare da angonta mujahid Ibrahim gaidam akan sadaki naira dubu 'dari biyu lakadan ba'ajalanba"yayinda Abbu yazamo alwalin,Jahida bababa kuma alwalin MD
Atake kotun ya'dauki kabbara kowa natofa albarkanci bakinsa kasancewar yanda auran yazo abazata, mutane se zuwa taya MD murna suke kowa nabashi hannun tare DA fatan alkhairi Allah yatayasa ruko yakuma basu zaman lafiya
"Wani irin yanayi yashiga me wuyar fassarawa, yakasa tantance shin wai shi mujahid din ne aka'daura wa aure, batare da anji ra'ayinsaba kowa sezuwa yimasa murna yake tare da Fatan alkhairi" Shi haryanzu yakasa tantance yanayin dayake ciki shin farin ciki zeyi an 'daura masa aure kokuma ba'kinciki,mayarda Kallonsa kan Abbu yayi da keta Washe baki kamar gonan audiga yana amsa gaisuwar jama'a"kowa yakalla acikin family sa fuskarsu nabayyanar da farin ciki Mara misaltuwa.Dafa kafadarsa da akayi tabayane yasanya shi juyawa yaga Akram, rungumesa Akram yayi cike da farin ciki yace congratulation mujahid natayaka murnan samun Jahida amatsayin mata hakika kuntadace dajuna ina maka fatan alkhairi Allah yatayaka ru'ko,yafada yana janye jikinsa daga nashi" bayabo ba fallasa yace Ameen Akram nagode.
Bayan duk anwatsene yarage sai family Jahida sena MD  awajen wanda basu wuce goma ba"umarni alkali yabawa Akram kanyaje ashugo da matan tunda angama 'daurin auren"amsawa Akram yayi cike da ladabi sannan yafice.
Acan waje kuwa lokacin dasukaji kotu ya'dauki kabbara tare da hayaniyan angama daurin aure ba'karamin hauka laila ta tayarba,se ihu take tana zage zage kan cewa mujahid natane ita ka'dai,bataga uban daya isa yarabasuba,kowani munafuki ne yaha'da auren tose yaraba kaman yadda yaha'da"da'kyar inna tajanyeta tasanya ta amota gudun kar jama'an alkali suji zagindatake yasa azaneta tunda deshi yaha'da"Jahida kam jin abin take tamkar almara mamaki al'ajibi ru'du duk alokaci 'daya yashigeta,tun sanda taji an'daura auren ta da MD tashiga wani mewuyar fassara tarasa farin ciki zatayi ko ba'kinciki?Hawaye taji yanabin fuskarta Wanda tarasa dalilin zubowarsu,sake jinjina lamarin take aranta wai Ya MD shine mijinta,ya rabbi ta ina zan iya zama da wannan *Mr arrogant* 'din amatsayin mijina kuma abokin rayuta?mutumin da magana mawuya take masa wayyo Allah na ta'fada tana hawaye tuni wa datayi wanene MD"gaba 'daya inna takasa samun nutsuwa tubsanda idanunta sukayi tozali da aunty fadeela,wani irin matsanancin kunya ne ya lullu'beta jitake inama 'kasa yatsage tashige,ganin aunty fadeela cikin shigar alfarma bawanda zeyi zaton cewa ita tahaifi mujahid sede ayi zaton kaninta saboda yanayin jikinta ba wahala atattare dashi,ko kallon inda aunty fadeela take inna takasa"Abangaren aunty fadeela kuwa batamasan Allah yayi tsiron halittar taba awajen ba domin kallo 'daya tamata tadauke kai saboda bata fatan kowacce ala'ka tasake shiga tsakanin su wanda yawuce gaisuwa kamar yanda addinin musulunci yaha'da,
" Sallaman Akram ne yakatse ma kowanne tunanin dayake aransa!!cikin ladabi yasanar dasu alkali na Neman su, mi'kewa Aunty fadeela tayi  taja hijab din dake kan Jahida tarufe mata fuska sannan tari'ke hannayenta suka nufi dakin dasuka zauna nafarko batare data kalli inda inna rabi take ba,waje kowanne su yasamu yazauna Inna se wani sussunkuyar dakai take kamar munafuka duk jikinta asanyaye _(koda yake *sa'ar bukar rabi'u* tace daman wai munafukace lol😹nide baruwana tsakanin kune intajiki)_.
Gyaran murya alkali yayi cike da farin ciki yace alhamdulillah alakulli,halin dukkan yabo dagodiya sutabbata ga Allah mekowa me komai hakika nayi farin ciki da wannan auren domin tun sanda mujahid yabada labarin haduwarsa da Rabi'atu nasan wannan wani hikimace ta Ubangiji"
Hakika INA godiya agareku dakukabani ha'din kai wajen Ganin mun 'kulla wannan kyakykyawar alakar ina rokon Allah yasa wannan abinda muka kulla yazamto silar shiganmu aljannah"Ameen suka amsa"hakika nasan bawanda yadace da zama miji kuma uba ga Rabi'atu se mujahid.
Ya 'dan dakata da maganan nawasu mintuna kana yamaida Kallonsa kan MD daya sunkuyar da kai Wanda duk bin 'ko'k'kofinka da diddiganka bazaka fahimci halin daya ke cikiba,farin ciki ko akasin haka,Murmushin manya alkali yayi Bayan yagama nazartan yanayin fuskar MD, Mujahid Jahida yakira sunansa cike da so da kauna domin haka Allah yajarabcesa da kaunar yaran aransa saboda nutsuwarsu"amsawa sukayi cike da ladabi, kusa dashi yamusu nuni alaman su zauna Ahankali sukadawo kusa dashi suka zauna cike da kunya.
Mujahid ga amanar Rabi'atu nabaka inafatan zaka kularmin da ita tamkar yanda zakula dakan ka koma fiye da haka,saboda nayaba da tarbiyanka dakuma nutsuwarka"batare da kasantaba kaceci rayuwarta Wanda samun irinka awannan zamanin yana wahala"inafatan awannan karon data zamto mallakinka zaka kula da ita kowani hakkinta kasauke muddin kanada hali yanzu, karka zamto miji mai zargi kokuma saurin yanke hukunci akan matarsa batare dakayi bincike ba duk abinda akace matarka ta aikata kokuma kagani toh katsaya kabincika bawai kayan ke hukunci kana dokin zuciya ba domin ance idan rai ya'baci be kamata hankali yagusheba aduk sanda ka aikata hakan to hakika wataran zakayi danasani.Tun sanda alkali yafara magana Abbu ya sunkuyar dakanshi dan ji yake tamkar dashi alkali yake wannan maganan wani irin matsanancin kunyar ha'da ido da aunty fadeela yake yayi danasani abinda ya aikata yafi akirga sherrin she'danne dakuma hawa dokin zuciya yasanya shi yanke hukunci batare dayayi bincike ba duk dakuwa yafi kowa sanin halayyarta, yaso ace yasaurareta a lokacin datake cewa yasaurareta,se yanzu yake nadama."Jikin MD ba'karamin sanyi yayiba jin nasiyyar alkali cike da girmamawa yace insha Allah ranka yadade zan kula da ita zankuma kare hakkinta akaina dede da karfi na sannan bazan bari hawayen ta yazuba adalilina ba"Murmushi alkali yayi yace Allah ubangiji ya albarkanci rayuwarka tare dakai da zuri'ar ka baki daya yakuma sanya wa rayuwar auren Ku albarka"Ameen suka amsa baki dayan su"Cikin nutsuwa da dattako alkali yakira sunan ta Ahankali Jahida ta'dago ta'amsa yace inaso kibi mijinki sauda kafa kizamto mace tagari awajen mijinki karki kuskura mijinki yayi fushi dake domin fushin miji yakan janyo tsinuwar mala'iku akan mace kizamto mace tagari Wanda ko kallon ki mijinki yayi zeji farin ciki aransa,karki zamto mace mai asiri da bin bokaye da Malam tsubbu domin bazasu iya yi miki komai ba sede su hallakar dake sukuma hanaki rahamar ubangiji kirike iyayen mijinki tamkar naki domin bakida wa'anda suka wucesu kada kiraina su wai saboda basu suka haifekiba,ina horon ki dakiji tsoron Allah arayurki domin samun farin ciki acikin rayuwarki."Sosai alkali yayi musu nasiyya me ratsa jiki banda kuka ba'abinda Jahida keyi"Inna Rabi kuwa wani irin zufa ke karyomata ta ko ina ajikin ta jitake kamar da ita alkali ke wannan jawabi bata ta'ba danasani irin na yauba.Seda alkali yagama jawabinsa sannan yakallesu yace ko akwai me magana acikin Ku Murmushi sukayi Abbu yace airanka ya da'de kagama magana sede muyi fatan Allah yabasu zaman lafiya yakuma kawar da idanun makiya akansu."baki 'daya 'dakin aka amsa da Ameen"Hajiya kokinda magana cewar alkali yana kallon Aunty fadeela, 'dan Murmushi tayi tace eh ranka shi da'de,inaso senan da wata biyu Jahida zata tare domin akwai shirye shirye dazamuyi kuma dole yana bu'katan lokaci" 'dan Murmushi alkali yayi yace toh wannan izinin aiyana wajen mijinta se abinda yace akai,alkali yakalli mujahid yace to mekace ka amince takai wata biyun kokuma a'a"shiru yayi bece komaiba sema sunkuyar da kansa dayayi.bakace komaiba koda kabarmin za'bine alkali ya'fada cike da barkwanci,dariya suka sanya dukansu anma banda Jahida da MD"kai ya gya'da alamar ya bashi iko"Kallon aunty fadeela alkali yayi akaro na uku yace toh Mmn Amarya muna Neman alfarman abari nanda sati biyu tatare nasan insha Allah zaku gama duk wani shirunku acikin sati biyu,sannan nizanyiwa Jahida kayan daki tamkar yanda kowani uba keyi ma 'yarsa,Ganin yanda yamata 'kwarjinine yasa ta amince da sati biyun,godiya suka shiga yimasa Tare da fatan gamawa da duniya lafiya. Cike da farin ciki bababa yace nikuma zan ha'da masa kayan lefe Sosai sukayi murna sunayima juna fatan alkhairi,kusa da kunnen MD Akram yamatso cike da zolaya yace wannan shine bikin 'dan gata babu sisinka ka samu santakeliyar mata" dan hararansa MD yayi batare dayace komaiba.
Cike da farin ciki suka yiwa alkali sallama kowa yafice"Suna fita Akram yakaraso wajen su Cike da farin ciki yace aunty nataya Ku murna Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi"ameen ta'amsa"yakalli Jahida cike da tsokana yace kanwata sekuma yafashe dariya yace nafamanta Ashe yanzu matar abokina ne baki tatura ta cikin hijab in tace Nide ya Akram haryanzu kanwarkace,dariya yayi yace Toh kanwata Allah yanada zaman lafiya yakuma sanya alkhairi,sallamar Mubin ne yakatse musu hiransu hannun yamika wa Akram sukayi musabaha. sannan ya kalli Jahida hannayenta yari'ke cikin wata raunanniyan murya yace dan Allah Jahida kiyafemin abinda namiki abaya Wallahi nayi nadama tun lokacin dakika bar gida yafada yana kokarin durkusawa kasa, dasauri ta taro tare da fa'dawa jikinsa tafashe dakuka cikin muryan kuka tace ya Mubin bakamin komaiba  kuma koda ka yimin ma nayafe maka Wallahi"Tun sanda Mubin yari'ke mata hannun yake kallansu harsanda tarungume sa wani iron malolon ba'kinciki ne yatokaremasa wuya idanunsa sunkada sunyi jawur tsabagen kishi,Ganin yanda tarungume wani katon banza tana kuka ne yasan shi fitowa daga motar yayo kansu tamkar wani namijin zaki..



     _VOTE COMMENT AND SHARE_ ✅


            *ESHAA CE ~*🤙🏻

MR ARROGANTWhere stories live. Discover now