59&60

289 22 0
                                    

*MR ARROGANT*
_(The story about young police man)_

*STORY AND WRITTEN*
           _BY_
*REAL ESHAA*

*WATTPAD*
_Realeshaa~_

*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

   *PAGE 59&60*🖊️

________________________________📖Washe gari:bayan sun tashi sunyi sallah kitchen MD yashiga yaha'da musu breakfast,mai lafiya"yayinda hakimar kecan tana bacci. kasancewar koyaushe shiyake ha'da musu kan darning yajere sannan yawuce toilet ruwan wanka mezafi yaha'da yadade a toilet din kafin yafito,yana fitowa yayi arba da,kyakykyawar fuskarta tsiramata idanu yayi yana kallon baiwar kyau da Allah yamata,yanda take bacci cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kamar batada wani matsala acikin rayuwarta.Ganin tana motsine alaman zata tashi yasanya shi saurin barin wajen dan beso tafarka tagansa"bayan yagama shiryawane cikin wasu ha'da'd'dun Riga da wando,wandon yakasance farine rigan kuma neavy blue wanda ya bayyanar da faffa'dan 'kirjinsa,yayinda yataje sumar kansa  me santsi da laushi irin na indi'a wa,wani ba'kin eyeglass yasanya a idanunsa Wanda yasake fitomasa da ainihin kyawun fuskarsa.Fitowa yayi yanufi dining zama yayi yai serving kanshi cikin nutsuwa yaha'da tea me kauri sannan yazuba Irish da soyayyan 'kwai,yana cikin cine yaji motsin fitiwarta batare daya juyaba yacigaba da break dinsa"zama tayi agefensa tafara ha'da nata,cikin respect tace dashi good morning, mamaki ne yakamasa jin yanda tagaishesa,tunda tazo gidan dede darana 'daya bata ta'ba gaishesaba,'boye mamakin sa yayi yace morning, how's ur body?tatam bayesa, Am getting better yace da ita ata'kaice.mamakin sauyinta yake sede be nuna hakanba yacigaba da break dinsa,batare da wani yasake cewa da 'dan uwansa komai ba. 'karar wayarsace takara'de parlour Ahankali yasanya hannun sa ya'dauka  sunan my friend keyawo akan screen din picking yayi tare da sallama. a'daya bangaren amsa wa Akram yayi tare da gaishesa,dayimasa sannu da jiki"Sir muna bu'katan ka yanzu dan munkama wasu yara da mugayen makamai kuma muna zaton yaran KB Cinnaka ne,aida sauri MD yature plate 'din gabansa yace Ok ganin zuwa karku yi komai akai senazo"insha Allah sir muna jiranka,sallama sukayi kowa yadatse kiran.Cikin sauri yature plate din dake gabansa yafice,saboda yanda yake saurin yaje yamanta berufe 'kofar ba "da kallo tabi Bayan sa kana ta ta'be,baki taci gaba da break din ta,bayan tagama break din kayan ta tattare kai kitchen tawanke ko wanne tamayar dashi mazaunin sa parlour tadawo tayi kwanciyarta akan 3siter" kwanciyar ta bada'dewa taji kaman ana ta'ba kofan falo Ahankali tami'ke setaga 'kofan abu'de mamakine yakamata Ganin kofar abude,rufewa tayi takoma tazauna sekuma taji tana sha'awan kallon waje yau kwanan ta goma rabon datakalli waje."Ahankali tami'ke tafice daga parlour"tsayawa tayi tana kallon yanayin tsarin gidan part biyu ne a'kasa sekuma wasu part biyun asama gakuma wani 'kofa daga gefe da'alama garden ne awajen daga can gefe kuma parking space ne yayinda akagewaye gidan dawasu flowers masu kyau,wasu kyawawan butterfly (Malam bu'de littafi)guda hu'du akan flowers din sosai suka burgeta dan akwai irinsu a garden din gidan su sosai takeson su, hannu tasa daniyyan kamawa anma se suka fire, ahankali take binsu suna sake yin gaba har suka isa 'dayan part 'din adede wajen ne tayi nasaran kama 'daya ihun murna tasanya tana tsalle yayinda gashinta yabaje afuskarta kasancewar babu mayafi akanta dan arayuwarta tana matu'kar son su murna takeyi tana tsalle dashi ahannunta baki 'daya tamanta da inda take."Abbu da tun fitowarta daga sashen MD yake binta da kallo cike da mamaki shin wannan yarinyar daga ina tafito inbagizo idanunsa ke masaba kayan mujahid ne ajikinta sannan da'alama batun yau ta kenan ba duba dayanayin jikinta"inna da fitowarta kenan salim yasata gaba da jaraba kan cewa setabashi dubu ashirin yaje birthday abokin sa itakuma tahanasa ganin zedame tane yasanya ta fitowa shi kuma yabiyota se magiya yake zabga mata.Turus taja tatsaya ganin mace na'ko'karin shiga cikin part din MD mamakine yakama,aranta tace wato abinda yasa yake hana shiga part din sa kenan wani irin farin ciki ne yaziyarci zuciyar ta yau zata tozarta mujahid akan hujja me'karfi,keeee tabuga mata wani razananniyan 'kara Wanda seda ilahirin gidan baki 'daya ya amsa dasauri Aysha tafito daga 'dakinta domin a tunanin ita inna ke kira saboda wani lokacin bata 'kiran sunanta sede kee"A matu'kar tsorace Jahida tajuya zuciyanta na wani irin buguwa da 'karfin gaske"cikin sauri inna takaraso wani 'kas'kantaccen kallo take binta dashi daga sama Har 'kasa cikin 'daga murya tace ke dan ubanki mekikeyi anan?shiru Jahida tayi kanta a'kasa jikinta serawa yake, Hannu inna tasanya ta'dago ha'barta ahasale tace ba magana nake mikiba me kike nema??"tuni idanun Jahida suka cika da 'kwalla,tarase mezatace,lafiyyayan Marin dayasau'ka akuncinta ne yasanya ta fashewa da kuka metsuma zuciya"wani wula'kantaccen kallo tawatsa mata wato 'kan'kanuwar ki dake harkin San karuwanci kizo ki tare a'dakin saurayi harda sanya kayan shi kegaki karamar 'yar iska ko yau kinzo inda yafi 'karfinki wannan daga kallon ki baki ra'bi addinin musulunciba duba da wannan gashin dokin dake kanki ta'fada tana mefinciko gashin kanta daga tsugunnen datake...ihun azaba Jahida tasanya jin wani azabebben zafi daya ratsa kanta.Cike da bacin rai Abbu yakaraso wajen kallon inna yayi yace haba Rabi meyesa bakya aiki da hankali ne, bazakiyi bincike akan abuba kafin kiyanke hukunci daga ganin bewar Allah kinhau aibanta ta tare da bugunta batare dakinji dalilinta aduk sanda zakiyi Abu bakya yinshi cikin nutsuwa datunani bakisan daga indatakeba anma kina zaginta tare da aiban tata,salma tayi saurin cewa gaskiya inna bakiyi Dede ba ni wallahi tausayima take bani dan Allah inna ki'kyaleta.ahasale inna tajuya kan Jahida dake raku'be agefan abbu batare da tasaurari maganganun suba dan batada lokacin su burinta bewuce MD ya wula'kantaba"tace ke 'karamar karuwa zokifice agidannan kafin na lahantaki wallahi bazaki zauna agidan nanba seki bari idan kwarton naki yadawo yanemamiki wani wajen kokuma kije can kinemasa" finciko hannunta tayi tanufi hanyan waje da ita...'kokarin 'kwacewa take tana wani irin kuka tamkar ranta zefita ni bakarubace dan Allah kitsaya kisaurareni,Cikin rashin sa'a santsi yaja kafanta akan 'kafanta tafa'di garin 'kokarin kwace hannunta 'kara ta'kwalla tana ri'ke 'kafanta wanda seda yayi 'kara dan azaba,anma tsaban rashin imani irin na inna hakataci gaba dajanta a'kasa batare data tausaya mataba.Tsawa Abbu yabuga mata wallahi rabi inbaki rabu dayariyyar nanba ranki ze 'baci haba wannan wani irin rashin imana nine da tausayi"Inamiki magana saboda banida daraja awajenki shiyasa bazaki saurareniba.saketa tayi tana huci se 'kun'kuni take Wanda ita ka'dai tasan metake fa'da"ganin tasaketa ne yasa taja 'kafan tana kuka takoma gefe tarakube"salim kuwa wani irin kallon sha'awa yakebinta dashi dan ba'karamin tafiya da imaninsa tayiba" ganin hakane yasa salma kiran wayar mujahid domin sanarmasa anma haryakatse be amsaba,Har miscall biyar tamasa anma bedagaba,cike da damuwa tari'ke wayar ahannunta tana addu'ar Allah yasa yakira,Aysha ma hawaye take cike da tausayin yarinyar.

*****
Abangaren mujahid kuwa yana fita direct station yanufa koda yaje betsaya westing time ba yasa Akram yakai shi wajensu" tambayansu yasomayi cikin salama kan su fa'da masa gaskiya,anma sesuka nuna masa basusan komai akaiba ganin zasu wahalar da shine yasa amusu gwale-gwale cikin mintuna ashirin akacanza musu kamanni"ganin azaban yayi yawane yasanya su fa'dan gaskiya duk maganan dasuke MD na recording, besa anbaryimusu azaba ba harseda yasamu abinda yake bu'katan San sani dabgane da KB Cinnaka.basu suka gamaba se  misalin karfe daya bayan yadawo daga masallacine,yaciro wayarsa daga aljihu kasancewar yasanya shi a silent duk sanda zeyi aiki irin haka yakansanya wayar a silent"yana cirowa da niyyan duba time yaci karo da miscall din salma sama da goma,mamaki yake anya lafiya kuwa?"kiran yasake bi ringing 'daya salma ta'dauka cike da damuwa tace ya MD dan Allah kazo yanzu akwai matsala,jiyayi kirjinsa yabada rass,me yafaru??dan Allah kazo de maganan bana waya bane" tsaki yai yakashe wayar batare dayace mata komaiba" Akram ne yakara so wajen sa da'alama shima daga sallah yake"Akram zanje gida salma takira ni wai akwai matsala toh bansaniba kojikin Abbu ne yatashi,se kayi kokari Ku karasa kafin nadawo katabbat bakubada belling din suba kowayene sukazo"cike da jimami Akram yace toh Allah yasa lafiya"Ameen ya amsa sannan yashiga motarsa yamasa key."Tunda ga haraban gidan yafuskanci akwai matsala tsats-tsaye ya tadda ahalin gidan baki daya, yayinda inna tahakimce akan kujera tana karka'da 'kafa cike da masifa.Zuciyarsa ce yaji yabuga dumm sakamakon arba dayayi da Jahida raku'be ajikin part dinsa tana kuka tamkar ranta zefita,kasancewar sa namijin duniya ne seya waske tamkar besan tsayuwar dasukeba direct inda take yanufa, meyasameki??tashi muwuce tana jin muryansa wani irin farin ciki yaziyarci zuciyar ta domin tasan inde suna tare tatsira baze bari acutar da itaba,dasauri tami'ke "Ranshine yaji yabaci sakamakon ganin shatin Hannu afuskarta,kobe tambaya ba yasan wacce zata aikata hakan,bece da kowa komaiba yariko hannun ta" salati inna tasanya tana tafa Hannu tace hausawa sunyi gaskiya barewa bazatayi gudu 'dan ta yayi rartafeba gado bakarambani ba an made ba'ayi gadon arzikiba,zargina yazama gaskiya"bedamu da maganan taba domin idan da sabo yasaba dajin irin wa'dan nan mugayen kalaman nata dan haka betankataba bawai dan maganan ganunta basuyi masa zafiba sedan besan meze ceda itaba.Ganin betanka taba yasa cikin sauri tashari gabansa cikin 'daga murya tace wallahi wannan karuwar yarinyar bazata zauna acikin gidan nanba,sede kanemamata inda zata zauna kuci gaba da ba'dalanku anma bazaku hana mana rahamar ubangiji shigowa gida ba shiyasa akecewa kayi aure kaki Ashe kasan abinda kake aikata wa haba ba'abanzaba katsera kofan ka kahana kowa shiga saboda kasan me kake aikatawa ba'a yin gadon hali me kyaubade."Rintse idanunsa yayi yanajin maganan ganunta kamar sau'kar aradu aka,idanunsa sunyi jawur alamun bacin rai,cikin husky voice dinsa yace bazata fita acikin wannan gidan ba sede kifitar daita inzaki iya"da'karfi yaja Hannu Jahida dan baze iya juran wa'dannan kalaman nataba"maganan ta daya kara'de kunnuwan sane yasa shi tsayawa cak batare dayajiyoba.
'Kwarai kuwa zanje insanar wa  commissioner kan cewa ka'ajiye mana karuwa agida,wata kila shiya'isa dakai, runtse idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa ra'da'di akan kiranta da karuwa datake yi"Hannun Jahida yari'ke suka nufi hanyar waje"Rintse idanunta tayi sakamakon azaban ra'da'din da 'kafafunta keyi mata" seda yaje Dede wajen Inna sannan yatsaya ido cikin ido yake kallon ta yace kinyi nasaran Koran 'da daga cikin gidan ubansa kinci galaba akaina,anma kisani bawai tsoronkine yasa zanbar gidanba sedan wani dalilina"bejira jin abinda zataceba yafinciki hannu Jahida da 'karfin gaske,ya MD salma takira sunansa tsayawa yayi batareda yajuyaba ,tace bazata iya tafiya ba taji ciwo akafantanta"batare da tunanin komaiba yatsugunna ya'dauketa kamar jaririya yafice daga gidan...


    _VOTE COMMENT AND SHARE_✅

    *ESHAA CE~*🤙🏻

MR ARROGANTDonde viven las historias. Descúbrelo ahora