8

655 54 1
                                    


Dinner yayi dadi anci ansha Amarya da ango sun samu kyaututtuka mai tarin yawa, basu bar wajan ba har saida Dadyn Fadima yakira k'anwarsa Maman shaheed awaya, fada yafara yi sosai ya kuma umurcesu da suwuce da Fadima gidan mijinta direct lkcn har 10:00PM tayi..

   haka kuwa akayi nandanan abokan ango suka fara kwasar yan'uwan Amarya da tawagan kawayanta cikin motoci na Alfarma, yayinda ango Zayyan yaja hannun matarsa suka fice daga Hall din bedireta ko ina ba sai cikin motar dake fake a harabar hotel din, 'Wanda dagani an tanadeta ne domin su babu kunya Zayyan yamaida murfin motan yarufe beko damu da idanuwan dasukai masu chaiiii,

masu gud'a nayi masu kirari nayi yan gulma da y'an ganin kwakwaf ma gasu nan kowa da irin nasa ra'ayin mu kam bamu da bakin magana,😜

       Fadima ko sai wani narkewa take ajikin sa tana shagwabe fuska ita adole ga me shirin yin kuka, abinka ga kasaitaccen gaye Wanda yadade da qwarewa a harkan love bata ankareba taji yakai mata wani gigitaccan runguma taisaurin buda baki da nufin dakatar dashi nan yasamu damar aika mata sakonnin daya dad'e yana adaninsu dominta, dan ya gaza haku ri su isa gida,

  Fadima tin tana kokarin hanashi har yakaiga tafara biye masa ganin yana Neman wuce gona da iri aifa tafara xubda hawaye Zayyan kam da alama yamance inda yake.

     Sunjima ahaka bebarta ba har sai da anwar ya karaso wajan da karfi ya bubbuga Motan, ahassale yafara magana,

"Zayyan wai kai wani irin dan iskan mutum ne kana Abu kaman wani karamin yaro wannan wulakancin ko Wanda betaba sanin mace ba bazaiyi abunda kake ba kawani..

tin isowar anwar Zayyan yarabu da Fadima sedai har lkcn tana lafe ajikinsa dakyar ya budi baki yace, "idan ka gama fad'an saika shigo kajamu ka karasa damu.

D'an bakin ciki kawai kawani yankemin jin dadi.. Dogon Tsaki anwar yasaki yabude gaban motan yazauna a mazaunin driver afadace yatada motar kaman meshirin tashi sama beko kalli inda suke ba,

Daga bayan mota Zayyan yakece da dariya da gangan yasake kankame Faty yace, "idan kaji haushi gobe adaura maka aure!"

Faty kuwa kunya kaman ta nutse gashi ba yanda ta iya dashi dole takara cusa kanta a kirjinsa tai lamo.. .

Suna xuwa anwar yai parking mota yashiga dasu cikin gidan, sadiya Jegal kanwan mahaifiyar Fadima takarasa da amarya part dinta basu samu damar gabatar da ita ga uwargida Zainab ba, cos dare yyi shiyasa suka bari sai dasafe, sosai kawayen amarya duk sun hallara xasuyi siyan baki,

suna xuwa guys din ango suka firfito ba a wani dau lokaci ba suka siya baki batare da bata lokaci ba aka watse..

koda Zayyan tadawo daga rakiyan abokansa kaitsaye part din Zainab yawuce, lokacin fitarsu XOXO da JH kenan bayan sun kwantarwa Zainab da hankali sun kuma jaddada mata tayi kokari wajan yaki da shed'an tana yawan karanta!!!

*"RABBANA AFRIG ALAINA SABRAN WASABBIK TAKADAMINA WANSURNA ALALKAUMIN KAFIRIN!"*

Sukace, "insha Allah idan kika rike wannan zakisamu sassauci azuciyaki duk wani xafin kishi Allah zai yaye maki!" da haka sukai mata sallama suka tafi.

Kwance take saman fakadedan gadonta Tanajin shogowan Zayyan ta fito suka hadu a falo murmushi yasakar mata tareda kai hannu zai rikota tajuya tana dariya tace Allah yatashemu lfy nasan dai good nyt kazo min dariya yyi yana mika mata ledan hannunsa tace, naki wayan ka aje anan Idan katafi na dauka, cikeda kaunan juna sukai sallama shikansa yayi mamakin Zee dinsa Dan beyi zaton zatai hakuri hakaba..

DANNAR 'KIRJI...💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now