Page 1

74 7 1
                                    

 ❄CUTA BA MUTUWA BA.❄

🌀 BY🌀
KHADIJA A.INUWA
(UMMY LOVE)

*[1:30pm]*
*20_08/2020*

Dedicated To All Muslims Ummah They Ones That Are Suffering From diff.types Of Sickness.

Bismillah.....
1
Daga ganinsa kasan bashi da cikakiyar lafiya saboda yanayin yanda kuzarin jikinsa ya nuna sannan da yanda yake tafiya. A hankali kamar an masa dole amman haka halittasa take.
Zaka dauka kamar yana da shafuwar aljannu sbd yanayin tafiyarsa.
A haka yake tafiya kai kasa kamar me Neman wani abu. Yarinyar da suke tare itama kusan yanayinsu daya saidai bambamcin dan kadan ne, sabila da Ameenah tana da surutu shiko Abduol bashi da surutu ko kadan.
"Yayah Abduol inaso naje wajen Mommy anjima, saboda nayi kewarta sosai".
Ya dubeta, ba tare da yace da ita ufab ba. Saima tafiyarsa da yakeyi kai kasa.
Tasha gabansa"Yayah Abduol magana nakeyi, plz take me to her"
Yace"OK zan kaiki amman baxamu dade ba saboda zanyi wani abu mai muhimmanci".
Tayi matukar farin ciki, da yake shagon bakin titi suka nufa.. Ko da suka dawo sai Ameenah ta shirya suka nufi wajen Mommy.
A matsanancin damuwa suka taran da ita, tana zaune akan kujeran falo ta zuba uban tagumi kamar wacce akayiwa mutuwa.
Ameenah ta zube a gabanta"Momm meke damunki"?
Momm ta dago ta kalleta sai ta fashe da dariya ,ta Mike tana raye2 da dukkan alama tayi hauka. Abinda ya firgitasu kenan suka shiga damuwa ainun duk dadai ba cikakiyar lafiyane dasu ba.
Mijin Momm ya fito da kayanta yayi mata watsi dasu yana fadin tabar masa gidansa yanzu2 nan. Ya ki fadin me tayi masa amman bai tausaya mata a halin da take cikiba duk da shine sanadi.
Babban burinsa shine tayi maxa tabar masa gidan.
Abduol ya jata suka fice.
Damuwar sun masa yawa wai shege da hauka. Yana cikin mawuyacin hali me cike da rudani gami da ban al'ajabi.
Gidan su suka nufa da itah.. Mahaifinsu na fitowa yaci karo dasu a falo.. Burki yaja ami da shiga bakin ciki"Me Saffiyah taxomin a gida?"
Ameenah tace cikin kuka"Mommy na bukatar taimako, Baba Hayat ya koreta".
Daddy ya kare mata kallo sai ya fahimci tayi hauka. Nan da nan ya shiga zazaga jaraba akan su fita da ita ,tunda ba aure a tsakaninsu me takeyi masa a gida. Abduol da Ameenah suka shiga ranrashinsa amman a banza. Babu yanda basu yi dashi ba akan ya hakura ta zauna dasu amman ya ki.
Hakan yasa suka fita taran da ita, sai firge2 takeyi amman Abduol ya riketa gam.
Suna sa kafarsu a get daddy ya fito da cewar saidai su zaba uwarsu ko ubansu. Wannan maganar ba karamin girgizasu yayiba.
Abduol yace" Daddy bai dace Ka ringa furta irin wandanan muyagun furucin saboda mahaifiyar muce, babu yanda zamu barta cikin wannan yanayin".
Daddy"Na fadamaku Inhar kun zabe ta to Ku sani babu ni, babu ku har abada'.
Ameenah ta fashe da kuka"Dadd ka taimaka mana.. Mahaifiyarmu ce. Ka duba ka gani a halin da take ciki."
Daddy ya harzuka" Banason karin bayani.. Ku zabi daya".
Suka tsaya cirko2 saboda wannan tambayar, Abduol yace"Baxan iya barin Momm a irin wannan halin ba kayi hakuri daddy".
Ameenah tace cikin sautin kuka"Kayi hakuri daddy".
Suka sa kafa suka bar gidan.. Momm nata haukata tana rike a hannu Dan ta.
Tafiya Abdul yakeyi ,babu Ameenah a kusa dashi juyawan da zanyi ya ganta a kasa sumamiya.
Wani faduwar gaba ya raxanashi yana hango Daddy yaja kofarsa, babu shiri gami da rikicewa ya saki hannu Momm ya nufi kan Ameenah da take yashe a cikin jini.. Tana ta zubar da Jini ta hanci saboda matsanancin damuwa da kuma cutar dake jikinta.
"Ameenah.. Ki tashi".
Ko motsi batayi hakan ya raxana shi. Juyawan da zanyi yaga wata bakar Land Cruiser a Parker ..wasu katai sun bito suna kokowa da Momm.. A haka har suka saka ta a cikin motar.
Da ganin abinda ke faruwa ya mike zumbur yana kokarin cin masu amman ina.. Subar wajen a hanzarce.
Nishi yake ba kaukautawa ya nufi wajen Ameenah sai asibiti.
Bayan wasu mintoci, Doctor Ya fito a kidime yana neman Abduol ,ba Abduol ba dalilinsa.
Ya wuce Police station. Ya shigar da karansa ya sami Inspector yayi mashi bayani sai Inspector ya kwashe da dariya, wai Abduol bashi da hankali daman yayi zubin marasa hankali.
Wasu zazzafar hawaye suka zubo masa.
Ko da yaga Inspector da gaske yakeyi sai yayi maxa ya dauki bindigar dake kan tebiri ya kafawa Inspector akai "Ka yarda dani ,gaskiya nake fadamaka'.

Cuta Ba Mutuwa Ba.Where stories live. Discover now