page 2

13 2 0
                                    

❄CUTA BA MUTUWA BA.❄

         🌀   BY🌀
      KHADIJA A.INUWA
     (UMMY LOVE)

2......

"Saina ga bayanku... Kamar yanda kukasa na ratsa ya'ta Kausar... Saina tarwatsa ahalin Ku da farin cikinku har abada."
Gama fadin haka keda wuya ta fice rai a bace.
(Fatima) Sunan Matar kenan, ta kasance matar ubansu Ameenah.Ko meyasa take kokarin kashe Ameenah da wanzar da bakin ciki ga zuri'arsu kamar yanda ta furta a baya.?
Ku biyoni donji meke faruwa.

  WAYE ABDUOLRAHMAN.
Abdul'rahman Lawal Shakka babu. Dan zuria Shakka babu ne, zuria ne wanda akasansu da arziki sosai a jahar kano ta dabo.
Alh.Lawal (Daddy) shine mahaifin Abduol me tsananin arxikine sosai sai dai Allah bai azurta iyalinsa da lafiya ba. Harta matarsa (Saffiyah) kullum cikin ciwo take, anyi maganin har an gaji. Ba karamin sabani suke samuba a sakamakon rashin lafiyarta. Alh. Lawal ya karo aure .Ya auro (Fatima) matar da taje asibitin don kashe Ameenah.
Fatima ta kasance tauraruwa a wajen Alh.Ta malake shi da asiri shiyasa komai itace gaba.
Kullum cikin fada suke da Safiyyah ,shi kuma Alh.in ya dawo baya jin Ba'asi saidai ya haukan maganar Fatima ya zauna.
Safiyyah naji na gani za'a bata rashin gaskiya saboda rufewa idon Alh.Lawal akan Fatima.
Ita kadai yake gani da kima da tarin daraja Mara musaltuwa.
Ba karamin farin ciki take da wannan mikamin ba. A bisa wannan dalilin yasa taci gaba da cin karanta babu babaka.
Wannan lamarin ba karamin zafi yakeyiwa Ameenah da Abduol a rai ba.
Wata ranar juma'ah da misalin karfe Tara na dare. Yunwa ya addabe Ameenah don tana daki kwance ko abincin rana bata ciba don tsananin damuwa.
Mikewa tayi ta nufi kicin ta zubo abinci sannan ta koma dining tana cikin ci, sai ga Fatima da yake da Ummah suke kiranta.
Ta dauke abincin cikin zafin nama"Wallahi baki isa ba,in dafa kici".
Ameenah ta dafe kanta saboda tsananin zafin dake firganta,ta mike saboda ta koma dakinta don mu'din tace zata biye mata...tasan zata iya laka mata wani mugun shairin.
"Ke don ubanki ina magana kina tafiya".
Ta tsaya cak"Me kikeso nace maki,bayan kin karbi abincinki sai kuma me"?
Ummah ta harzuka"Yanzu saboda rashin tarbiyya ni kikewa tsawa"?
"Ba tsawa na maki ba,gaskiya ce nake fada,amman inya maki zafi kiyi hakuri ".
Mari ta kai mata.Sanda Ameenah ta saki wani mugun kara sannan ta fadi a kasa sumamiya.
Mommy da Abduol a guje suka fito,ko da suka taran da Ummah a gaban Ameenah sai sukece daman zaa rina wai an saci xanin mahaukaciya.
Kanta sukeyi suna kiran sunanta.Amman ina ta suma.
Abduol ne ya dauketa sai cikin mota.Mommy ta ruga dakin Alh.ta sanar dashi...sai ma kara juyi yake akan gado"Allah ya bata lafiya".
Abinda ya iya cewa kenan.
Wani hadaden bakin ciki ya tsayawa Mommy a rai amman sai ta basar suka nufi asibiti, a inda Doctor Kamal ya shiga duba Ameenah cikin hanxari.


      WASHE GARI
Abduol na zaune kusa da Ameenah jiran farfadowanta kawai yakeyi.
"Ameenah ki tashi karki mutu.. Matukar babu ke ,ahalinmu bai cikaba".
Mommy na kuka,itama ba lafiya ne da itaba karfin haline kawai.
Ta Daura hannunta akansa tana shafar gashin kansa"Adu'a take bukata ba kuka ba".
Rungume Mommy yayi daga zaunan.
A haka har kusan mintoci sannan Doctor Kamal ya shigo.
"Ina kwananku ya me jiki?"
Mommy tayi saurin share hawayenta"Lafiya lau dacta.. Me jiki da godiya".
Suka yi musabaha da Abduol .
Sannan Doctor ya dubata ya gama abinda zanyi mata ya fice tare da basu umurnin zuwa office dinsa.
Bayan sun hallara doctor ya shiga sannan dasu cewa"Jikin Ameenah yana kara tashi sosai,a sakamakon haka zamu shiga da ita aiki gobe saboda ya shafin kwakwalwarta sosai."
Abduol ya mike zumbur"Innalilahir...
Yanxu doctor kana da tabbacin zata warke in anyi mata aiki?"
Doctor yayi sanyayar ajiyar zuciya gami da cewa"Am sorry to say.. Allah ne kadai yasan gaibu kuma shine me bada nasara akan komai,abinda Ameenah take bukata a wajenku shine adu'a".
Mommy tace"Insha Allahu ..."
Shiko Abduol jikinsa yayi sanyi. Doctor ya sanar dasu kudadan da zasu biya da magungunan da zasu siyo. Gidan suka koma sabila da ba kudin sai a wajen Alh. zaa karba.
Abin bakin ciki ya dami Mommy gashi tun da suka tafi asibiti jiya daddare bai kira yaji meke faruwa ba.
Mommy na isa dakinsa ta shige ta taran da Ummah kwance a kusa dashi.Ganin Mommy yasa ta fara masa shagwaba bai ita yawo takeso suje.
Cikin bacin rai Alh. Ya kalli Mommy"Ke Baki iya sallama bane da zaki shigowa mutuna daki kai tsaye".
Mommy tace'Na nemi izini sai naji shiru ,Amman in na bata maka rai kayi hakuri".
Ummah ta kara kankame shi"Dear ta dameni da hayaniya.. Kuma kasan banason hayaniya".
Alh. Ya kwatsawa Mommy tsawa. Nan da nan ta fice.
Abduol na ganin fitowarta ya mike zumbur,"An sami kudin?"
Mommy ta dake" Aah".
Yace"Yaah Salaam... Meya faru".
Ta kasa furta komai. Abduol ya fahimta.
A takaice Dan kunna gold dinta ta siyar,shi kuma Abduol ya siyar da wayarsa. Suka hada kudin aikin da magungunan.
Wajen karfe 5:03 na yamma,suna asibitin tare da Ameenah don ta farfado.Abduol ya riko hannunta"Ya kamata ki saki ranki Insha Allahu zaki warke...Kiyi sauri ki warke saboda samar da farin ciki a zuri'a mu"
Ameenah ta yi ajiyar zuciya,amman sai ta kasa furta komai.
Mommy tace"Karka damu Abduol zata warke da yardan Allah, ai cuta ba mutuwa bace".
Abduol yace" Insha Allah Mommy.. Ya kamata ace Daddy na tare damu a daidai wannan lokacin ko don' bawa Ameenah nishadi gami da karfin gwiwa akan aikin".
Mommy tace" Uhmm kabar maganan nan, Muji da kanmu".
Abduol yace" Toh Mommy ...".
Ko da dare yayi sai Abduol ya koma gida,Mommy ce zata kula da Ameenah zuwa wayewar gari.
Abinda ya taran dashi a falo ya firgita shi yayi tsaye cak.
Ummah ce xaune akan kujera,a yayin da Alh. na mata fifita da hand fan.

"Kai baka iya sallama bane bare gaisuwa?"
Ko kulata baiba ya wuce.
Tsawan da Alh.ya kwatsa masa yasa ya tsaya cak.
"Don Ubanka ba magana take maka ba?"
'Kayi hakuri Daddy ni banji ba'.
"Okay.. Yanxu duk surutun da mukeyi bakaji ba ,haba dai".
Ya fadi yana mamaki, itako sarauniya tace"Barshi kawai bakaga yayi zubin marasa hankaliba ai tsawone dashi amman ba tunani ko kadan shiyasa nake masa uzuri".
Alh. Yace" Ba shakka ai naga alama".
Har Abduol zai wuce sai ya hango abinci a dining.Kai tsaye ya wuce ya zauna ya zuba abincin kenan zai kai baki,sai yaji saukar duka da kan tsisiya.
Cikin fifinanan daga murya take ta faman jaraba"Amman ka cika mara kunya,abincin uban naka zakaci, ni da wahala kai da cinyewa".
Ya mike dafe da keya saboda tsananin zafi"Baki da hankaline zaki dokeni sai kace dan ki".
Alh. Ya mike ya shiga zabga masa mari baji ba gani.
Abinda Ummah takeso kenan, taga ta hadasu fada. Kuma dalilin ta na dukan Abduol saboda tasa magani a cikin abincin shiyasa bataso yaci abincin ba .
A dadafe Abduol ya shige daki, sai hucin bakin ciki da takaice yake. Ya tsani Ummah har  a zuciyarsa, da yace bashi da hakuri da Allah ne kadai yasan me zai faru.
A haka ya kwanta da yunwar cikinsa ko da yunwar ta ishe shi sai ya Mike ya shige kitchen.
Zuwan Ummah gidan yasa tasa Alh. Ya kori yan aikin girki saboda ta iya dafa abinci gagara misali.
Ba karamin dadin girkinta Alh. Yake ji ba.
Sai yan shara ,wanke2 da sauran aiyuka aka bari.
Koda Abduol ya shiga kitchen sai ya daura tukunya a kan gas.
Ya kasance tun yana karami ya iya girki da sauran aiyukan gida.
Da yake shine dan fari sai Mommy ke koya masa a hankali duk da dan gidan mai hannu da shuni ne .
Indomie ya girka yaci sannan ya sami sa'ida gami da kwanciyar hankali.
Yana zaune akan dining Ummah ta fito rike da hannu Alh. Da dukkan alamu fita zasuyi saboda sunci ado me tsananin kyau gami da daukar hankali.
Ummah ba wata babban bace don kuwa Abduol ya girmeta.Shekarun shi 28 itako 24.
Ko kallo bai ishe suba suka fice.Tana dariya kamar sabuwar mahaukaciya.Ko da suka fita inda suke ajiye motocin gida sanda ta zaba motar da takeso su hau na alfarma me tsananin kyau gami da daukar ido.
Sahat store suka nufa a inda tayi dan siyayan kayan makwalashe kamar su cholocate,sweet candle da dai sauransu.
Har sun dau hanya komawa gida sai ta kafe akan suje asibiti don duba Ameenah.
Isarsu keda wuya. Doctor Kamal ya masu zagora dakin da suke.
Ba karamin mamaki Mommy tayiba sbd tasan akwai dalilin daya kawo Ummah duba jikin Ameenah.
Ta gaisheta kamar ba ita take mata rashin kunya a gida ba.
Mommy da Alh.suka fita suna tautanawa don haka Ummah ce akan Ameenah.
Itako Ameenah barci takeyi sosai.
Ummah ta dauki filo ta dana wa Ameenah akai.
Ameenah ta galabai ta sai ta samu ta hankada ta ,babu jira Ummah ta fadi a kasa.
"Kasheni zakiyi me nayi maki,ke muguwace baki da imani".
Ummah bataso ba wai haihuwa da damuna.Sai ta fusata " Bai kamata ace kina wahala da kudadan Alh. Ba kinga kwara ki mutu kawai ki huta ,taimakon ki nake fa".
Ameenah ta fashe da kuka"Mommy ki taimake ni ,Ummah zata kasheni".
Ummah ta fito da wani magani a jikkarta ta watsa mata.Nan da nan Ameenah taci gaba da barci.
Ummah ta gyara komai kamar babu abinda ya faru.Sai ga Mommy ta shigo hannunta rike da makudan kudade.Nan da nan Ummah ta fusata "Wadanan kudaden na meye?".
Mommy ta bushe da dariya" Wannan aikin Allah ne ba aikin boka ba".
Sai Ummah ta harzuka,ta fisge kudaden sai suka shiga kokowa.
Har kan Ameenah,Amman ko motsi batayi.
Alh. Na shigowa ya shiga kwatsa masu tsawa sai suka yi cunko2.
"Da izzini wa Ka bata kudaden nan?"
Alh. Ya marairaice"Am sorry Dear...na tausayawa halin da Ameenah take ciki shiyasa na bata, Amman keep clam zan baki ko nawa kikeso, let go ".
Ta manne kudadan a kirgi" Baxai taba kasancewa ba, inhar suna bukatar kudin magani suzo gareni har inda nake ba kaine Zaka bata ba tare da izzini na ba, da fatan kaji"?
Ya amsa da "Okay dear".
MOMMY naji na gani anfi karfinta.A haka suka fice.
Mommy ta zube akasa sumamiya.
Kayi kusan 12mins kafin nurse ta shigo,a firgice ta kira doctor Kamal.
Mommy na dauke da ciwon zuciya.Gashi hawan jininta ya hau.
Nan da nan ya gudanar da abinda ya dace.
Sannan daga bisani ya kira Alh.  Har kusa 10missed calls bai daga ba.Sai ya kira Abduol ya sanar dashi.
A gigice ya iso asibitin gashi dare yayi sosai.
"Mommy ki tashi...ya zakiyi min haka why why".?

Next page......

#Comment
#Share
#Like

Cuta Ba Mutuwa Ba.Where stories live. Discover now