4

11 2 0
                                    


*Page 4*

*Wannan page din naki ne doctor beely, u are d best*

Nan da nan bincike ya gudana, babu me matsalan rashin haihuwa a cikinsu saidai wata CUTA ce ta mamaye masu jiki shiyasa suka kasa haihuwa.
*Wannan wata cutace haka???*
Hannal na dauke da cutar SANYI (TOILET INFECTION) Ta samoshine ta sanadiyar Zaman hostel da tayi a lokacin tana karatu a Bayero uni kano.
Gashi ciwon sanyin ya zamu mazauni a jikinta har tayi aure shima Amud yana dauke dashi.
Yana matukar sa mata ciwon ciki tayi2 kamar zata mutu, kaikayi da fitar farin ruwa duk sune alamominsu. Gashi Hannal ta kasance me wasa da amfani da shan magani a rayuwarta. Doctor Kamal ya tabbatar masu da cewar cutar ya lulube mata mahaifa. Mujinta Amud yana dauke dashi shima ta hanyar matarsa ya kamu da cutar. Ya dage da magunguna lslamic kamar su amfani da tafannuwa, gayen magarya da kanufari gami da sauran magunguna masu nagarta dana asibiti dukka.
Amman ya kaurace ma shimfidarta saboda samun sauki, ya dauka tana amfani da magunguna.
Intayi na kwana biyu sai ta watsar.
Amman in ciwon ya taso tana jin jiki.
*Wannan shine abinda ya faru da Hannal game da rashin haihuwa*

Doctor ya harzuka saboda ya fahimci ba amfani da magunguna take ba.
Bayan jikin ya lafa. Suna office zaune tare da Amud.
"Cutar sanyi Babban cutane shi yake janyo mata matsananci ciwon ciki musamman a lokacin al'ada sannan hakan na janyo mutuwa cikin gaugawa".
Amud ya razana sai ya mike zumbur saboda yana matukar son ta. Gashi ya ji maganar mutuwa.
"Doctor banason in rasa matata pls minene abun yi".
Doctor ya gyara zama " Abinyi shine amfani da magunguna yanda na bata shine kadan mafita. In Baku dage ba haka zai ci gaba da cinta".
Amud yace"Gaskiya na fara gajia da wannan lamarin but I wil try my best insha Allah ".



         *Ameenah*
Jikin nata sai adu'a numfashi na kokarin fin karfinta,a dalilin haka doctor yasa mata oxygen . Cikin Yardan Allah sai jikin ya fara sauki . Ba karamin rikicewa Abduol yayi ba ya tsorata ainun ji yake tamkar mutuwa zakayi ba sauki sai wajen Allah.
Ga jikin mommy sai adu'a yawan damuwar dake cikin zuciyarta ya karawa ciwon tsanani matukar sabila da haka jininta ya hau sosai.
Abduol ya kidime sosai.
Itako Gimbiya Ummah zata yada zango a gida sai ta Shiga waya da kawarta Kubrah ta sanar da ita koma saboda ta yarda da ita matuka, shiyasa take fadamata cikinta.
Kubrah ta sheke da dariya" Mata a gidan Shakka Babu kenan, ki aiwaitar da komai yanda boka ajal ya umurceki mana. Me kike jira?"
Ummah tayi sanyayar ajiyar zuciya" Ai key dakinta yana wajen Abduol kuma suna asibiti".
Kubrah tace" to ai wannan damar zakiyi amfani dashi ki banla kofa ba tare da wani ya gankiba".
Ummah tace" akwai matsala fa..yan aikin gidan zasu gane"
Kubrah ta ringa zigata akan itace da gidan sai abinda taga daman yi ,kawai tasan dabaran da zarayi kan Abduol ya dawo.
Ummah ta mike tana safa da marwa a haraban dakin.
Can kuma sai ta tunsure da dariya.Tanawa kanta kirari na salon mugunta da keta.
Dakin ta nufa da bakar Leda a hannunta ta dauki wuka ta boye ta nufi wajen dakin mommy. Anan ta taran da yar aiki tana moping sai tace taje kitchen tayi mata wanke2.
Tana tafiya ta shiga bubuga kofa tana soka me wuka. Ta dade tana haka sai ga kofar ya bude.
Da sauri ta shige tana me tura kofar. Nan da nan ta wurga ledan kadangarun karkashin gado.
Sai ta shiga wargaxa dakin tana bincike. Sai ga wasu takardun gidaje biyu da Alh. Ya bawa Mommy kyauta kan ya auro Ummah.
Nan da nan bakin ciki ya cika mata ciki ta boye a riga ta fito tana gunaguni.
Dadai lokacin Alh. Ya shigo falon.
" My dear ya naganki Kamar baki lafiya?"
Ta juyo tana yamutse fuska" Lpy ta lau an dawo?"
" Eh na dawo inata sauri saboda naxo naci girki me dadi sannan nayi kewarki sosai".
Ko kulashi batayi ba ta wuce dakinta shi kuma ya bita kamar rakumi da akala.
Ta samu ta boye
takardun.
Can kuma sai ga Abduol ya shigo ya dawo saboda yunwa . Yana sa key a kofar dakin momny sai yaga tsabanin haka yayi matukar mamaki daya ga dakin a hargitse.
Amman sai ya fara zargin Ummah. Ya tattara komai gami da gyara dakin.
Ya nufi falo Kai tsaye ya Shiga tambayar Ummah wa ya bude dakin Mommy. Kawai ta rufeshi da masifa akan me zan tambayeta wa ya shiga dakin wawiya.
Zafin zagin da Ummah tayi yasa shi ramawa. Kawai takai hannu zata mareshi.
Alh. Da sauri ya rike hannu yana bata hakuri. HHaushin hakan yasa ta dauke Alh. Da mari wai tunda bayason a hukunta Dan shi to ta rama akan shi.
Nan da nan Abduol ya dauketa da mari.
Sai Alh. Ya rufeshi da masifa.Itako ta kara dauke Alh. Da mari.
Ran Abdul ya baci abincin da bai Ciba kenan.
Shiko Alh. Sai hakuri yake bata.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 18, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Cuta Ba Mutuwa Ba.Where stories live. Discover now