part 3

10 3 1
                                    

   *CUTA BA MUTUWA BA*

             *NA*
      *KHADIJA A INUWA*
        *(UMMY LOVE)*
   


               ❄❄
                 
*INA GODIYA A GAREKU ...CUTA BA MUTUWA BA FANS*
*YHU CAN FOLLOW ME ON FACEBOOOK*
*KHADIJA A INUWA*
*ON WHATS'APP*
*08167748315*
*AND ALSO WATPAD*
*KHADIIJAINUWA*
*YOUTUBE CHANNEL*
*GIDAN HAUSA NOVEL*

*inuwakhadija395@gmail.com*

*Page 3
*THIS PAGE IS FOR YHU MEERA TAHIAHUZ*

Mommy na dauke da ciwon zuciya.Gashi hawan jininta ya hau.
Nan da nan ya gudanar da abinda ya dace.
Sannan daga bisani ya kira Alh.  Har kusa 10missed calls bai daga ba.Sai ya kira Abduol ya sanar dashi.
A gigice ya iso asibitin gashi dare yayi sosai.
"Mommy ki tashi...ya zakiyi min haka why why".?
Ko motsi batayi banle ta amsa masa. Yayi kuka sosai, Shi kansa Abdoul din karfin hali kawai yayi don ba karamin rashin jin dadin jikinsa yakeba.
Doctor kamal ya masa bayyana komai gashi ana bukatar magungunan Mommy gasu da masifar tsada sosai.
(Mommy na dauke da chronic heart attack). Tana matukar wahala da ciwon kuma dashi aka haifota dashi. Tun tana karama iyayenta suke shan wahalan kudin magani gashi babanta karamin da karuwane (Small Scale Business). Mahaifiyarta Kosai take siyarwa da safe a gidansu. Shigowar Alh. A rayuwarta ba karamin haske ya gudanar a gareta ba saboda yaci gaba da daukar nauyin kudin maganin.
Abduol ya rasa madafa gashi Ameenah jikinta ya tsorata Doctor Kamal.Don numfashinta na kokarin daukewa, ciwo ya tsananta ainun s sakamakon maganin da Ummah ta watsa mata (Boka Ya Bata).
Abduol ya koma gida don sanar da Alh. Shine kadai manufa. Don yan uwansu basu sonsu ko kadan banle yaje garesu.
Yan uwan Mommy kuwa sun tsanesu sakamakon sun cika ciwo.Wayyo rana zafi inuwa kuna.

       *UMMAH*

Ta tusa Alh. A gaba kamar wani dan ta,da matsanancin jaraba" Akan me zaka bata kudi bayan banda masaniya akan yin hakan, gaskiya a dakina zan kwana yau don raina ya baci ainun".
Gama fadi haka keda wuya ta dauki filo. Alh. Ya rikota "Am srry dear na fadamaki baxan karaba, tausayinta naji shiyasa amman inba don Ameenah ba wallahi da baxan bayarba".
Ta turo baki kamar shantu " To naji amman baxan kwana anan ba ".
Yayi ranrashin amman a banza da yake tana da fushi me karfi wanda yake jima bata sauko ba.
Tana isa dakinta ta kwanta "
Hello shegiya kawata ya katsinan"?
Kawar ta ta me suna Kubrah ta sheke da dariya " Amarya a gidan Alh. Shakka Babu Allah ya ja da zamaninki amman ki kiyaye ranar tonan silili".
"Hehhh zancen kikeso aini inabin umurni Boka akan duk abinda ya umurceni kinga ko inada nasara babban"".
Kubrah ta bushe da dariya " Amarya a gidan Shakka Babu kenan, so ya kike ya maganar Kishiyar taki ki sa an saketa kua?"
Ajiyar zuciya Ummah tayi" hmmm ki bari kawai so nake ta gaji da kanta zata nemi takardan sakin amman inason ganin bayan Ya'yanta tukunna, becoz Boka Ajal yace matukar ya'yansa na raye baxan taba malakan dukiyar Alh. Ba".
Kubrah tace" kutumelesi wallahi baxai yuyuba wai gurguwa da auran nesa, me kike jira ki zuba masu guba a abinci suci duk su mace mana".
Wannan shawaran ba karamin dadi yayiwa Ummah ba.
Kubrah ta kasance shegiyar kawa me zuga akan aikin tsabawa Allah ,amman ita bara tayi ba.Irin kawayen nan ne masu kai mutum wuta. Ita kanta haushin Umman takeyi saboda duk a cikin kawayensu ta fisu ci gaba.

         *ABDUOL*

A tsugunne a gaban Alh. Yake yana rokansa. Alh. Ya mike ta debu makudan kudade ya bashi akan ya boye kar Ummah ta gani.
Washe gari Mommy ta farfado amman bata iya mikewa sai hawaye take saboda matsanancin ciwo dake cikita.
Abduol na zaune a wajen Ameenah ta farfado amman bata iya tuna komai, sai kallonsa take kamar hoto.
Zuwan dagin mommy yasa Abduol ficewa daga dakin.
An fasawa Ameenah aiki asakamakon wani dalili na binciken Doctor Kamal.
Yan uwan Mommy sun jajanta masu sannan sunyi masu adua. Kanwarta Raiyah ta zauna don jinya.
Kusa yamma sannan Alh. Yaxo dubasu ,ya saki jikinsa kamar bashi ba. Ya jajantawa Mommy.
Ta dubeshi cikin sanyayiyar murya" a haka zamuci gaba da zama da Fateema kenan.. Alh. Duk wannan bakin rayuwar duk saboda ita muka Shiga".
Nan da nan Alh. Ya canja fuska" me kike nufi...shiyasa nace kishinki yafi karfinki".
Mommy ta matse hawaye saboda zazzafar zugi "Ka fifita rayuwar Fateema akan tamu. Anya kanaso Ka gama da duniya lafiya kua".?


Cuta Ba Mutuwa Ba.Where stories live. Discover now