TARKON MAQIYA

39 3 0
                                    

"Nifa kinga hafsa bana san irin haka;ke kullum muka zo nakaranta baki da aiki se yiwa mutum cakulkuli,gaskiya ni karatu zanyi ko natashi na barmiki gurin". " To kitashi mana;kinsandai babu me rabamu sai Allah,kuma duk inda kikaje se nabiki". "To kibini mana;nikuma nagayawa malam;kinsandai halinsa dukanki zaiyi baruwansa da magiyrki". " To yadakeni din mana; idan ya dakeni wata tsiyarce". "Ke surutum mekuke?". " Malam wai dannace ta tinamin nan gurin shine shi.....! "hafsa duk tabi ta rikirkice;gata da tsiwa gakuma shegen tsoro.Malam yace; " shine me?".Nayi caraf nace;"Malam wallahi qarya take kullum muka zauna bata da aiki se yiwa mutum cakulkul,kuma atambayi halima ma idan qarya nake".  "Baruwana kema ai basan karatun kikeba". Hafsa tafaki idon malam hanka linsa yana kan wasu dalibai dake qoqarin shigowa;tai min gwalo tare da fadin cewa;gashi nan ta gwaleki,a dai dai lokacin kuma hankalin malam ya dawo kammu bayan ya kora daliban a cewarsa sum makara. " Ke magan ganun me kuke?kufito gaba dayanku". "Wallahi malam atambayi halima itace akusa damu,tana ganin abinda ta kemin".
             " Ni babu ruwana su suka  san abinda suke fada". "To kufito gaba dayanku Ku karbi bulala;ai kullum tare kuke".idan dinan hafsa suka cicciko da kwalla gwarama ni nariqe nawa tsoran a zucuyata, muka qarasa gurin malam cikin fargaba da tsoro, ina daga gaba gaba;hafsa kuwa sai ja daba take tana ta famar magiya tana bawa malam haquri,na durqusa agaban sa;yadaga bulalar se da yayimin uku kwarara;wacce gwara ai maka guda goma masu sauqi,idona yacicciko da kwalla natashi ina sosa wajan.Hafsa ta durkusa nesa kadan da malam.Malam yace; " bazaki matsoba?idan kika bari na qaraso nan bulalarki ta qaru".Tamatsa a tsorace;malam yadaga bulalar jikake tsul tsul.....hafsa tai zumbur tamiqe tana sosa gurin hawaye suka fara kwaranya a fuskarta,ajin yayi tsit  sautin shashsheqar kukan hafsa ne yake tashi akusa dani,nikuwa se famar cika nake ina batsewa hafsa ta jawomin duka. Malam yace;kowa ya dauko qur,aninsa. Aka fara karatu,yana fita malamin tauhidi ya shigo.
                 Qarfe 3:55 pm muka fita sallar la,asar kowa yanufi wajan alwala tare muka fito da halima hafsa min barta a class nace da halima;"wallahi kema halima muna fukace kina kallon abinda take min amma bazaki fadi gaskiyaba". "Ina ruwana bake kike qawance da itaba;indai zakiyi qawance da ita bazata barki kiyi karatu ba". Ashe hafsa tana bayammu;se ji mukayi hafsa tace; " To munafuka ai badolabane qawancan da ita;ke kuma karki qara biyomin ma karanta se kije kiyi qawancan da halima".Daya daga cikin 'yan ajimmuce tazo wucewa taji muna cacar baki,tatsaya tace; "Hassana da Usaina sunan da suka samana kenan,"me yayi zafi haka?karfa aganku arana". Hafsa ta nuna halima tace; ai ga muna fukarnan data hadamu;tana fada tana hara rar halima tare da fadin cewa idan aka tashi daga makaranta se ta durza bakin halima aqasa tajuya zata tafi saddiqa ta jawo hannuta tace " hafsa kitsaya ayi sulhu";ta fincike hannunta tare da cewa;ni da Allah cikani naje nayi alwala";fuuuu....., taqara gaba tana 'yan guna guni narashin gaskiya,nayi wani dan mur mushi;wai hafsa ce za tai fada da halima,ni dai bana san suyi fada da halima;saboda nasan halima duka za taimata.Halima ta bata amsa da cewa "Allah ya kaimu a ta shin,yarinya zaki gane shayi ruwane,aikim banza se kace sallar ta dameta muka qarasa bakin fanfo ita kuma adai dai lokacin ta idar da alwala zatabar gun,nace da halima "gaskiya ki dena cemata salla bata da metaba". Halima tace to qarya nayimata saunawa ana barinta acikin aji kedai kice kareta zakiyi saboda qawarkice". Nayi shiru nasan tabbas abinda halima ta fada hakane,hafsa tana wasa da sallah nikaina inashan fama da ita akan yin sallah akan lokacinta amma se tace dani wai nakyaleta kotace ai ba kabarimmu daya ba,nace da halima " halima dan Allah karki biyewa hafsa kiyi fada idan antashi daga ma karanta". Halima tace; "dama aini ba kulata zanyiba;tinda inajin maganar iyayena da ta ma lamaina, bazan tsaya ina fada da ita akan hanyaba da kayam makaranta ajikina, idan nayi fada da ita ai senabata sunan makarantarmu,ace malamammu basa yimana tarbiya, kuma ace iyayenama basiyimin tarbiyaba,nayimata hakane dan na tauna tsakuwa aya taji tsoro;.
           5:30 pm dai dai muka tashi daga ma karanta;kafin qiftawar ido da bismillah;na nemi hafsa na rasa tagudu;dama nasan kuri take bazata iya fada da halima ba,dama ta saba irin wannan kurin ta tsokani mutum tace zata durje mai baki a qarshe se antashi ta gudu.
 

Ina cikin daki ina shiryawa;hafsa tayi sallama. " Assalamu alaikum".Umma ta amsa "wa,alaikumussalam" hafsa ta qarasa inda umma take tace; "Umma ina yini". Tace;lafiya hafsa;ya mamannaki?"Tace " lafiya qalau;tace tana gashheki".Umma tace; "ina amsa wa". Hafsa ta qaraso cikin palo ta qaraso inda nake tana fadin cewa,wai ke har yanzu baki gama shiryawaba?sarkin sinin niki". Naimata banza fuskata ba annuri;na qarasa saka kayana na dauki hijabina nasaka,muka fito muna zuwa a dai dai kofar palo nace tabani littafina na muqarrara,tace;  "to ki barimana sai munje makaranta na baki". Nace;  "gaskiya ni yanzu zakibani dan yau bazan zauna akusa dakeba,ki jawomin duka". Umma tana daga dakin girki  tajiyo magan ganinmu taqaraso inda muke tace;  "wai cacar bakim mekuke har yanzu baku tafiba,se kummakara?hafsa tace; "umma wai se na bata littafinta nace tabari muje makaranta taqi;wai ita bazata zauna akusa daniba,kuma wallahi umma ba kowane yake zuga taba se wata halima wai ta dena qawance dani"Umma ta kalleni tace;  "Aisha ashe baki dahankali! ke wawiyace?na gir gizakai alamar a;a to meyasa kike daukar zugar mutana harkika bari akeso ashiga tsakaninku da hafsa, yarinya tana sanki". Nace "to  umma ai ba lefina bane duka ta janyomana a makaranta,shi yasa nace na daina zama akusa da ita". Umma tace; "lefi kukayi gaba daya" hafsa da tasan bata da gaskiya se tayi qasa da kanta,nace wallahi ni bani da lefi itace kullum mukaje ma karanta bata da wasa se cakulkuli".Umma ta kalli hafsa wacce Taqara yin kasa da kanta,umma tace; "haba hafsa keda nake ganinki me wayau ;amma kike wasa wasamma na cakul kuli wasan cakulkuli ai ba wasa bane ki daina wannan dabi,ar kinji,tagyada kai alamar ta dauki fadan da ake mata,umma tacigaba dacewa;cikin aji dakin karatu ai bawajen wasabane kidena kinji ku maida hankalinku  kuyi karatu,bakyaso in kingirma kizama malamar makaranta?. Se alokacin hafsa ta dago kanta daga sunkuyon datayi da shi,tace; " a;a umma ni nafiso ko nagirma nariqa zuwa qasar dubai ina saro kaya kamar yadda mama take,teaching da wuya kai ta fama da yara".Umma tayi murmushi tare da fadin cewa; "hafsa kenan na fahimceki wato ba kyasan kudi kadan su shigo miki". " To umma wa zai so kuwa".Umma tai 'yar dariya tace;da hafsa ja irar yarinya,sannan tace;to Ku hanzarta Ku tafi karku sha bulala".aranar umma ta shiyamu.

          

TARKON MAQIYAUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum