TARKON MAQIYA

26 2 0
                                    

Ranar wata asabarne;na shirya zuwa gidansu hafsa dayake ranar
ba islamiya,na sanar da umma cewa zani gidansu hafsa,da farko
umma ta dan nuna rashin amin
cewarta, tace; "nifa ba nasan yawo kuma kin san dai halin Alhaji in yazo yaga bakyanan ni zewa fada". Nace; " umma tinda
fa mukai hutu sau daya naje gida
nsu hafsa,itakuwa tana yawan zu
wa".Bayan nayi wanka na shiryane,nafito palo nace da umma zantafi,tace; "to Allah ya tsare ki gaida maman nata,kuma,
kikula da kanki". Nace; " inshaAllahu umma
zan kiyaye".Tace Allah yadawo dake lafiya". " Nace; "ameen umm a".

Sannu sannu;ina takawa cikin nu tsuwa na danyi kasa kasa da kaina, nakusa zuwa gidansu hafs
a, nadago kaina sosai;me zan gani hafsa na hango takusa qaras
owa inda nake,taci wata uwar kwalliya kamar aljana, tana tafamar murmushi.
ta qaraso dab dani tace dani; "daga ina zuwa ina?". Nace; "daga gida zuwa gidam mama". Tace; " ba wani nan ke dai kice wani gurin kikaje kika qaraso". "Nace; "au shedar dazaki
min kenan?"Tace; " oho;kekika sani tinda akayi hutu zuwanki daya nikuwa kullin ina kan hany
ar gidanku, nace;naji na dau lefin
nace "keyanzu ina zaki?" Tace; "gidanku zani". Allah sarki hafsy ba daga nanba wajan zumunci,kice da munyi sabani". Muka qarasa cikin gidan tare dayin sallama. "Assalamu alaikum". Mama ta amsa; " wa,alaikumussalam".Na karasa inda mama take na gashsheta,tace; "ammadai haduwa kukayi ahanya?" Nace; "eh; mama". Tace; "to ya ummannaki?" Nace; "tana lafiya tace;a gashsheki". Tace; "na karba". Muka nufi dakin hafsa.

Hira muke sosai; duk hirartamu akan makaranta muke kowa acikinmu nabada labarin yadda yanayin dokokin makarantarsu yake, wani abun yay dai dai dana school dinmu da tasu hafsa,wani kuma ya ban banta.Nace; "gaskiya exam din wannan karon tayi zafi dayawa,hafsa ta tabe baki " ummm; nikam wannan karon ina gida ban komaba,han
kalina akwance".Nace; "kekuwa hafsa dan Allah me yahanaki ko mawa,Allah hafsa kiriqa yiwa kanki fa....ban qarasa maganarba
tayi caraf tace; "Nariqa yiwa kaina fada,kema kinsan ban da lafiya shi yasa ban komaba". Nace mata; "wannan haka yake, alamar ban yadda da maganarta
ba,nafa san halinki hafsa indai akan karatune,kedai kawai kin langwabewa su mama zakice ba
ki da lafiya 'yar renin wa yau". Ta harareni;tare da yin fari da ido,tana cewa; " ke nifa school din nan in naga dama, daga wannan hutun na gamata kuma ba wanda ya isa ya mai dani". Nai mata wani kallo me dauke da alamar rashin kunya atare da ita
nace; "okey haka kikace?". Tace;
" Eh" tana fada tana sake yin fari
da ido. Nace; "kamar a kunnan abba da mama" ina fada ina murmushi namiqe kamar gaske
.
Na nufi kofa, tinanin hafsa daban da nawa a zahiri na nunawa hafsa zanje na fadawa su mama amma abadini zan fita dan yin alwala, nayi hakane dan na tsora
tata,nasan bata tsoran mama amma tana shakkar abba.
Cikin sauri ta sha gabana tana magana qasa qasa "haba Aisha ke ba,a sirri dake da wasafa nake ". Nace mata; "Allah ko....! 'yar renin hankali,to aikuwa se na fada ko da wasa kike". Tariqe hannuna "dan Allah Aisha karki fada,kin san halin abba",
Nace; " ke ni dawasa nake alwala zanje nayi".

Bayan sallar magrib na baro gidansu hafsa ta rakoni bamiyi nisa da ta fiyarba wata mota tazo ta sha gabammu daga bisani ta tsaya hasken lantarkin
da ya gauraye kan hanyar shi zai baka da mar ganin mutanen dake cikin motar
samarine guda biyu kallo
daya zakai musu kasan 'yayan hutune, dukkansu qananan kayane ajikinsu kalar kayansu
iri daya tamkar 'yam biyu se dai shi dayan idan sa yana dauke da bakin gilashi Hafsace ta fadada fara,arta tare da fadin cewa; "shikenan ke kin huta se aqarasa
dake,gasu Abdul can".kafin nace;
wani abu har hafsa ta qarasa inda suke,ban tsaya bi takan hafsa ba na qara gaba nabarta a
nan sautin muryar hafsa najiyo
tana kirana, "Aisha Aisha dan Allah ki tsaya". banju yaba nacigaba da tafiya motsin mota naji abayana amma hakan besa na juyaba se dan matsawa danayi
nakoma gefe amma ban dena tafiyaba inajin alamun tsayawar
motar, hafsa ce ta bude murfin motar tafito cikin sauri ta qaraso
inda nake ta sha gabana fuskarta
ba walwala. " Haba Aisha mene
ne haka ya mutane zasuce kizo
su rage muki hanya ki gwalesu".
Fuskata ba annuri "kinga hafsa karki qara yimin irin haka
tinda kike dani kin taba ganin an
tsaidani akan hanya an daukeni?
haka kawai bansan mutaneba zan shiga motarsu". "To ai kinsan
haka kawai bazance kizo kishiga
ba, batare da na sansuba", qarshe
dai muka rabu da hafsa ranta abace nawa abace,rakiyar da bata qarasa minba,acewarta daya daga cikinsu yayantane wai
na wulaqan tasu.

Sannu sannu haka rayuwa tacigaba da tafiya tsakanin gida,
da makaranta in kana makaranta
kayi kewar gida, in kana gida
kayi kewar makaranta mu samman yanzu da muke gab da kammala karatu.
Ina zaune adaki ina kallon wasu picture dimmu da muka dauka tin muna j.s one,ina kallon
fuskokin kowa kowanne da yana
yin daukar hotansa irin na quruciya, ko wacce ka kalleta se tabaka dariya,kusan dukka ninmu 'yan class dimmu a school
din zamiyi graduated en ka dauke mutum biyu daya tabar makarantar daya kuma ta rasu,
Allah sarki school life! rayuwar makaranta kenan wani
ya batamaka yasaka kuka wani
ya saka farinciki yabaka dariya,
wani yabaka haushi da takaici,
wani ya cuceka wani ya kyautata
maka.wani en kuka rabu dashi har abada baza ku sake haduwaba

Munkoma makaranta se fatan Allah, ya bamu sa,a mugama lafiyi.

Danku nake, Ku qarfafamin gwaiwa     
                  da
comment,vote, share.

TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now