Unedited chapter 😴Lagos, Nigeria.
Har yamma ranar suna beach dan sai wuraren maghreb Kabeer yayi mata magana su wuce. Tare suka jero ta taya shi riqe some of the stuffs they came with zuwa parking lot. Straight hotel suka wuce, suna isa Kabeer ya fada bathroom yayi wanka ya shirya tsaf cikin kaya marasa nauyi. Sallah yayi kan ya futa daga dakin dan ba Khayri space itama ta shirya. Tana ganin ya wuce living area din suite dinsu tayi sauri ta fada wanka. Time sosai tayi taking a bathroom din kan ta futo ta shirya tayi sallah itama. Tana kan sallaya tana azkhar ya shigo yace mata in ta shirya ta futo su je neman abinci. Cikin minti biyar tayi sauri tayi rounding up azkhar dinta da shirin ta ta futo ta same shi. Tare suka sauka qasa zuwa restaurant din hotel din, immediately suna zama waiter ya taho musu da menu sukayi making orders dinsu ya wuce dan processing order din su. While they waiting for their food, wayar sa ta shiga ringing. Tana kallo ya saki wata yar murmushi kan ya daga call din.
"Hello babes". Ya fadi cikin wayan. Hakan ya sa Khayri zuciyar ta na wani irin bugu da sauri ga kuma azabar zafi da taji yina mata. "You have no idea how badly I miss you". Ya fadi a shagwabe hakan ya sa Khayri taji kamar hawaye na shirin kufce mata. Koh kadan abun be mata dadi ba yadda Ya Kabeer ke ta hira da mace a gabanta, without a single care in the world. Ai koh ba komi matarsa ce ita, koh da baya son ta a ganinta be kamata ya dinga mata irin wannan cin fuskar ba. Danne hawayen da ke kokarin kwacewa daga idanunta tayi ta dauke idanunta daga kan Ya Kabeer wanda ke ta washe haqora sai kace wanda aka yi wa albishir da aljannah. Hirarsa yike tsakanin sa da Allah sai kalaman soyayya yike ta fadi a cikin wayan sa, sai kace be ma san Khayri na zaune gefen sa ba. Waiter ne ya dawo musu da abincin su, yayi placing musu several exquisite dishes a gabansu yayi wucewar sa. Abincin ta ta fara ci, willing herself to zone out of the conversation Ya Kabeer was having with his lover. Har ya fara cin abinci be ije wayar ba, soyewar su suke ta yi. Khayri dai fam! Ta cika da bakin ciki da kuma tsananin haushin da take ji.
"Okay baby, byeeee love you". Ya fadi yina murmushi. "Sai na dawo gobe. Zan zo na ganki soon as I'm back". Yana fadin haka ya kashe wayar ya ije a gefe ya cigaba da cin abincin sa. Sai a lokacin ya dan dago kai ya kalli Khayri wadda kanta na qasa tana kallon plate din abincin da ke gabanta. Dauke kansa yayi ya cigaba da cin abincin sa. Quietly suka gama dinner suka koma daki ta shige ciki ta daga wayarta shikuma Kabeer yayi zaman sa ya fara kallo a haka har barci ya dauke shi.
The following day tun wuri suka tashi suka fara kintsa kayansu, shirin tafia. Tare suka futa yace mata suje siyan ma su Billie tsaraba. Ikeja mall suka wuce ita dai Khayri tana ta bin sa a baya, duk inda taga ya shiga itama ta sa qafa. Sai da suka shiga wani store na body shop tukun Ya Kabeer ya mata magana.
"Ki daukan muku". Kawai yace mata ba tare da ya kalle ta ba. Dan tsayawa tayi unsure of where to start from "Duk abunda ya kwanta miki a rai ki dauka". Ya qara kan yayi gaba ya dau wani face cream yina dubawa. Ita kuma Khayri wata sales girl ce ta matso ta fara guiding dinta through choosing products. Komi guda uku take dauka har ta gama. Counter suka wuce aka yi packing kayan da suka siya suka biya kudi suka futo. Wajen kayan ciye ciye suka wuce nan ma Khayri ta daukan musu abubuwa har sai da tace masa ta gama tukun suka wuce suka biya suka bar store din. Next ya ce suje sama akwai store inda yike so ya duba. Shuru suka hau stairs tana biye da shi shuru har suka isa shop inda yike so ya shiga ya gama abunda zai yi ya futo suka wuce. Bayan barin su ikeja mall sun tsaya a wurare da dama Kabeer yayi ta harkokin gabansa.
Wuraren karfe biyar na yamma jirgin su ya sauka filin jirgin Malam Aminu kano international airport. Already Maamah ta sanar da driver ya dauko su dan haka da isar su already sun sama driver din ya iso yina zaman jiransu. Kabeer ne ya riqe musu luggages dinsu ita kuma Khayri ta riqe shopping bags suka taho driver na hango su ya rugo a guje ya anshi luggages din hannun Kabeer ya zuba a bayan mota, dawowa yayi ya karbi na hannun Khayri ita ma yina musu barka da hanya. Cike da fara'a Khayri ta ansa shi Kabeer kam as usual, kamar ana sa shi dole yin magana. Tunda suka shiga mota har isar su gida zaman kurame suka yi, ba wanda ke cewa dan uwansa komi, shi Kabeer yana ta danne dannen sa a waya yana ta sheqa dariya sai kace wanda ya zauce, khayri kam shuru ta zauna duk ta ji ta a takure. Bata ji hankalin ta ya kwanta ba har sai lokacin da suka iso harabar gida ta samu Maamah na waje na jiran isowar su kamar yadda ta saba. Tana saukowa daga mota Mahra ta taho da gudun ta dan hugging din khayri. Maamah na murmushi take fadin "Toh Mahra an ga yar uwa, yau baza mu sha iska ba". Khayri kam murmushin kunya kawai tayi da ta iso wurin Maamah ta durqusa har qasa gaishe ta. Irin abubuwan nan da khayri ke yi na nuna tsantsar ladabi da biyyaya ga Maamah har da su Dattijo, da kuma nuna nutsuwar ta da kyaun tarbiyyar da aka mata ke sawa a kullum Maamah ke qara son ta, take qara farincikin hada ta aure da Kabeer.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...