This chapter is specially for my friends, my sisters, my one big online family😍🤗 yan SANADI readers group. Thanks for the immense love, motivation and support. It was great talking to you beautiful ladies yesterday 🤗🤗 that was the highlight of my day! I hope you enjoy the chapter. Xx
.
******************
.Kano, Nigeria.
"Me sa baka zo da ita ba?".
Ahmad da ke tuqi ya juya ya kalla Kabeer kan ya ce "Wace? Zulaikha?". Daga masa gira daya yayi alaman tambaya.
"Quit joking around Ahmad. You know who I'm referring to".
"Oh I do?" Ahmad ya fadi kan ya kwashe da dariya "Ni na san abunda mind dinka ne Kabeer? Koh ince wadda take mind dinka". Wani irin kallon kallon Kabeer ya masa ya rasa abunda zai ce da shi dan haka ya share shi kawaii. Har sun sha kwanan da zasu dau hanyar gidan Dattijo Kabeer yace wa Ahmad ba nan zasu ba su fara zuwa gidansu tukun ya gaida su Maamah dan a tunanin sa Khayri tana nan gidan ne. Murmushi Ahmad yayi ba tare da yace komi ba dan ya riga ya gama dago Kabeer din. Juya kan mota yayi kawaii suka koma kan hanyar da zai sada ka da unguwar su Maamah.
"Wai koh ka san aure na saura sati uku kuwa". Ahmad ya fadi in a teasing tone amma Kabeer ya qi biye masa "Koh kuwa ka san kanwar ka zan aura". Juyawa ya ga how Kabeer was gritting his teeth, trying so hard to maintain his cool "I love her so much. We will have seven or eight babies tog....". Ahmad be gama maganar ba Kabeer ya cakumo sa.
"Are you discussing the kids you're going to have with my sister with me Ahmad". Dariya Ahmad ya fashe da kan yace "Toh in ba da kai ba da wane zan yi? Kai ne babban aboki na ai".
"I'll kill you i swear. Talk about my sister again and I'll strangle the life out of you".
"Your sister?" Ahmad ya tambaya "Oh you mean my wife-to-be! My Mahra". Tsaki kawai Kabeer yayi ya share shi dan ya lura da gangan Ahmad yike yi to rile him up.
Murna wurin Maamah da taga Kabeer baya misaltuwa. Rasa inda zata sa kan ta dan farin ciki tayi, shi kam Kabeer din kamar ta maida shi ciki ta kuma haifan sa ta dinga ji sabida dadewar da tayi bata gan sa ba. Nan gidan ya ci abinci ya dan huta ana ta hira, kowa da kowa was around except the one person he was hoping he would find. Kalle kalle ya dinga yi koh zai gan ta amma dai yaga alaman Khayri bata nan. Billie ce ta miqe da plate din snacks imda suka ci zata kai kitchen Kabeer ya yi saurin miqewa ya bi bayan ta dan ya tambaye ta.
Billie bata ankara ba cikin kitchen din sai kawai ji tayi an dunguran mata kai da muryar Kabeer yana fadin "Hey Bils" nickname in da yike kiran ta da shi. Juyawa tayi ta kalle sa fuskar koh wata walwala babu, ba kamar Billie inda ya sani ba "Ina khayri?". Ya tambaye ta.
"Nan gidan matar ka ke zama?". Ta tambaya kan ta fice daga kitchen din bata ma tsaya jiran abunda zai ce. Dariyar Maamah wanda be san lokacin da ta shigo kitchen din ba yaji a bayanshi. Dan tabe baki yayi kan yace "Maamah kin ji autar ki koh? Daga tambaya".
Dariyar Maamah take yi ta ce masa "Toh ai da gaskiyar ta. Nan gidan matar ka ke zama ne? Koh ka bamu ijiyar ta ne?".
"Ahhhh lallaikam" Ya fadi kan ya qara da "Allah ya baku haquri barin zo na tafi gidanmu naga matata".
"Toh in ka gan ta kace mata muna gaida ta". Maamah ta fadi.
Yana futowa daga kitchen din ya sama Ahmad a living room yana waya. Bisa dukkan alamu da Mahra yike waya sai wani qasa qasa da murya yike yana murmushi. Harara Kabeer ya galla masa kan ya ce "In ka gama sai ka miqe ka kaini gida".
Dariya Ahmad ke yi yadda yaga Kabeer ya hade rai ya san takaicin rashin samun Khayri da yayi a gidansu yike ji "Wife-to-be tace na gaishe ka. Wai ya hanya?".
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...