Babi Na Goma (10).

1.2K 180 11
                                    


Cikin hanzari ta shigo dakin diyarta jin wani ihun da ta sake. A zaune ta same ta, ta dora chin dinta akan gwiwanta, hannayen ta ma were wrapped round her legs da alama a firgice take.

"Niima habibty" Karimatu ta kira sunanta a hankula bayan ta zauna a gefenta "What's wrong, why're you crying my child" ta tambaya. Dora kanta tayi a shoulder din mahaifiyar ta wadda ke ta faman shafa gashin diyar nata cikin kulawa.

"I had a dream, a very bad dream" ta fadi tana sauke ijiyar zuci.

"To shine zaki yi ihu madadin addu'a".

"It was so scary Ummi, I thought I was going to lose you". Ta fadi hawayen ta na qaruwa "it felt so real Ummi, I don't want to ever lose you".

"Shhhh" Karimatu ta fadi tana cigaba da shafa gashin kan Niima "It was just a dream, ba ga ni ba. I'm not going anywhere".

"I was little" Niima ta fadi "I was so little in the dream Ummi, mukayi hatsari" Sosai jikin Karimatu yayi sanyi jin abunda Niima ke fadi.

"It probably was just a memory from my childhood. Mun taba hatsari ne Ummi?" Maganar ta ne ya katse tunanin da Karimatu ta fara.

"Umm hatsari kuma, aah". Karimatu ta fadi cikin hanzari. Miqewa tayi zata wuce "kiyi sallah sannan kiyi addu'a sai ki koma barci. Don't be scared my love" sai da tayi kissing goshin Niima kan ta wuce. Har ta kai bakin qofa muryar Niima ya tsayar da ita.

"Ummi" ta kirata cikin nutsuwa "Have I ever had a sister?" Maganar ta yasa Karimatu juyowa ta yi facing dinta. Qafafunta ke rawa dan da kyar suke supporting din weight dinta "Da nike karama, na taba yin kanwa ne?".

"What are you talking about Niima, just go to bed please". Karimatu ta fadi not knowing what to say to her inquisitive daughter.

"Na taba kanwa kenan" Niima ta fadi not wanting to let go of the conversation.

"Aah Niima, bayan ke ban taba wata diya ba. You're my one and only. Okay?". Murmushi Niima tayi mata itakuma cikin hanzari ta bar dakin dan gudun kar Niima ta kuma dago wani tambayar.

Qofar dakinsu ta rufe kan ta zube a qasa ta saki wani kuka, Abdallah wanda gaba daya kwanakin baya iya samun wani barcin kirki ya matso kusa da ita ya fara shafa bayanta kamar yadda mintuna kadan da suka wuce ta dinga shafa na Niima.

"Me ke faruwa ne Abdallah. I'm I loosing my child. What have we done, what have we done" ta dinga fadi hawayenta na qaruwa.

"Haba Karimatu, ya kike yin haka ne. So kike Niima ta ji ki ta fara zarginmu koh me? Please stop".

"Things were going smoothly. We were happy; you, I and our daughter amma yanzu gaba daya abubuwa na neman sanjawa".

"Dan Allah ki bar damuwa Karima, I'll put things back in order, ko mi zai daidaita. Niima is a secret we'll take to our graves, ki daina damuwa dan Allah" Abdallah ya dinga rarrashin matarsa. Ya riga ya san next step inda ya kamata ya dauka. Tabbas Bakhtiar Al-Arab is the only person that can get him out of this mess he has created. Dole ya hadu da Bakhtiar, it was time to dine with yet another devil.

.
°°°°°°°°°°°°
.

Kano, Nigeria

Ta jima kwance a qasa inda ya wuce ya bar ta in banda kuka ba abunda take faman yi. Duk wannan wulakancin da Khalid ke mata be sa koh na kwana daya taji ya fita mata a rai ba sai ma wani sonsa da ke qara shiga zuciyar ta baza kuma ta daina praying and wishing that one day her Khalid, the romantic and compassionate man she married will come back to her, to their family. Kuka sosai take tana jin haushin kanta, tana takaicin yadda zuciyar ta ta kasa haqura da Khalid. Da gatan ta da komi ya maida ta marainiya, gashi ba abun tace zata fadiwa iyayenta abunda yike mata ba ya raba ta da yan yaranta wanda bayan Khalid duk duniya ba Wanda take so irinsu, bazata iya imagining rayuwa without Khalid and the twins ba. Dan haka dole ta cigaba da haquri, ta dinga jure duk wata cin fuska da zai mata, ta kuma cigaba da masa addu'a. Sa da ta gama cin kukanta ta qoshi kan ta miqe ta fara gyara inda ya bata. Shards of glasses inda ya fasa ta bi ta dinga tsincewa, wasu ma duk sun yanketa amma haka ta dinga tsincewa tana share hawayen da suka qi daina gangarowa daga fuskarta. Tsaf ta gyara wajen kan ta wuce ta hada ruwa me zafi sosai ta shiga bathtub ta zauna. For long ba abunda takeyi sai tunanin irin rayuwar da suka yi ita da Khalid a can baya kan ta wanke jikinta ta fito tayi dressing wounds dinta kan ta nemo kaya ta sanya. Ta san ba ita ba fita kuma har sai duk tabon dukan da ya mata sunyi fading. That was how merciless Khalid was. To the outside world he was an angel while to his wife he was a monster, one she dreaded.

SANADIWhere stories live. Discover now