Babi Na Ashirin Da Takwas (28).

917 153 22
                                    


Abuja, Nigeria.

Tafia suke a cikin mota tare da wasu mutane da bata san su ba, bata taba ganin su ba. Zaune gefen ta wata yarinya ce yar qarama, wadda kwata kwata bazata wuci shekaru uku ba. Kallon hannun yarinyar tayi sai taga tana wasa da wata yar tsana, irin wanda ita ma take da shi, wanda ta yi kyauta da shi ta ba wata da suka hadu gidan mai a katsina, a lokacin tun tana yarinya. Gaban motar kuma namiji ne yana tuqi yana hira da matar da ke zaune gefen sa riqe da baby kan cinyarta.

"Su waye ku? Ina zaku kaini?. Ta tambaya amma babu wanda ya juya cikinsu ya kalle ta, kamar basu ji me take fadi ba infact kamar she was invisible to them, ba me ganin ta cikinsu. Yarinyar da ke zaune gefenta tayi yinqurin tabawa amma sai hakan ya gagara because it was as if there was an invisible wall of glass keeping both of them apart. Tana kallo yarinyar ta cigaba da wasa da yar tsanar ta tana mata rawa. Tana kallo matar da ke zaune a gaba ta juyo ta kalla yar yarinyar. Tana ganin mijin ya juyo shima kallon yarinyar. Tana kallo tanker yayo kan su. Ihu tayi tana fadiwa mutumin ya juya ya kalla gabansa amma kamar baya jin abunda take cewa. Ji tayi motar ya fara juyi, mata da mijin nan suna ihu, itama yarinyar da ke zaune baya tana ihu ga karamar itama tana kuka.

Firgigit Niima ta farka daga barci, jikinta jiqe da zufa. Tafin hannunta ta sa ta share fuskar ta tana fadin Innalillahi wa inna ilayhi raji'un. Wannan wana irin mafarki ne haka tayi? Komi cikin mafarkin was so vivid to her, clearly taga fuskar kowa da ke cikin mafarkin kuma clearly ta ga duk abun da ya auku. Wayar ta ta jawo ta duba time taga it was a little past two am, zama tayi shuru tana kokarin collecting memories din mafarkin ta daga baya dai ta miqe ta wuce bayi ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallan nafila ta dan yi karatun Al-Qur'an kan ta miqe ta nannade hijaab dinta da sallaya ta ije. Har zata koma kwanta sai ta wuce vanity table dinta don ta shafa Vaseline a hannunta da take jin ya bushe. Ta gama shafa Vaseline din har zata juya kenan sai idanunta suka fada kan wani hotonta da ke vanity table din. Hoton ta ta ne da aka dauka lokacin tana da shekaru hudu a duniya, zaune take jikin Umminta a gidansu da ke USA. Hannunta riqe da yar tsanar ta wanda tayi kyauta da shi shekarun da suka wuce, tun tana yarinya. Frame din hoton ta dauka ta riqe ta qurawa fuskar ta kallo. Dan runtse idanunta tayi na wani dan lokaci tana kokarin picturing fuskar yarinyar da ta ga ni cikin mafarkin ta. As if struck by electric shock, Niima ta sama kanta da gigita wanda har hakan ya sa ta saki frame inda ke hannunta ya fadi qasa, Allah yasa kan carpet ya fadi dan haka be fashe ba. Tabbas koh shakka babu yarinya da ta gani cikin mafarkin ta ita ce, koh kuma me irin fuskar ta ce a sanda take karama. Gashi Yar tsanar da ta riqe sak irin nata. Toh amma kuma su wanene mutanen da take mota da su, koh kadan basu da kamanni da Ummi da Abban ta, kuma taga matar was holding a baby, ita kuma a iya saninta bayan ta Umminta bata sake haihuwa ba. Kan a haife ta ma iyayenta basu taba haihuwa ba, ita ce one and only dinsu. Komawa tayi bakin gado ta zauna tana ta tufka da warwara can dai ta kwanta da niyyar komawa barci bayan ta yanke shawarar tambayar Umminta da safe game da mafarkin da ta yi.

Ta idda sallan asubah kenan koh miqewa bata yi ba daga sallaya sai ga Ummi ta turo qofar ta shiga tare da matar da ke mata gyaran jiki. Murmushi tayi ta gaida su suka ansa mata da fara'a suma, Hajia Aisha yar Sudan sai faman washe baki take tana amarya kin sha kamshi abunki.

"Maza maza a fara kan gidan ya fara cika, ban so sai mutane sunzo sun taru a fara". Ummi ta fadi. Corridor Hajia Aisha ta wuce inda take ije kayan aikin ta tun ranar da ta fara ma Niima gyara. Kaya ta fara ciro kan ta juya tace wa Ummi "Hajia muna buqatar madara, sannan ki aiko masu aiki da garwah".

"Toh" Ummi ta fadi ta juya zata futa. Miqewa Niima tayi ta bi bayanta dan dama da mafarkin da tayi ta kwana a ranta. "Habibty, lafia kike bi na?". Ummi ita fadi da ta juya a corridor taga Niima a bayanta.

"Ummi tambaya nike so na miki".

"Ina jin ki 'ya ta".

"Ummi mun taba accident ne?". Tana da lura da shift a mood din mahaifiyar ta kamar bata so tambayar da Niima ta mata ba.

SANADIWhere stories live. Discover now