Unedited chapter. Was feeling lazy to go through it after typing so read at your own risk!
***********
Shi dai Bakhtiar kasa komi yayi sai pacing up and down yayi ta yi. Doctor na futowa ya nufe sa. Kallon halin da Bakhtiar yike yayi kan yace masa they should go to his office akwai paperwork inda zai cike. Suna isa doctor din yace masa ya zauna sannan yayi calming down.
"We think your wife was poisoned" Doctor din ya fadi a natse "An samu traces a jinin ta. Thank God it was a small quantity. A little bit more and she would've been in coma or probably dead even". Shock ne ya kama Bakhtiar ya ma rasa me zai ce. Nazari kawai yike koh ta ina Niima zata iya samun poison a system dinta.
"Kana iya tuna last abunda ta ci koh ta sha?". Bakhtiar ya fadi masa cewar daga kwano daya suka ci abinci a safiyar ranar amma shi gashi lafiyar sa lau. Nan doctor ya shiga masa bayanin cewar it was possible ba a ranar ta ci poisoned food din ba sabida poison din irin wanda ke aiki kadan kadan ne ba wai a lokaci guda ba. "It could be something she ate during the day yesterday, koh da dare".
"Well Alhamdulillah your wife is out of danger. Allah ya sa ka kawo ta da wuri we were able to stop the spread". Hamdala Bakhtiar ya fara "But unfortunately we couldn't save the baby. I'm sorry". Sosai Bakhtiar yaji ba dadi, for the second time in life he has lost his chance of being a father. Kan sa ya dora kan hannayen sa duk ya rasa me ke masa dadi. Doctor din ya dafa shi yana basa words of encouragement. Godia kawaii Bakhtiar ya masa kan ya cika paperwork din ya miqe. Tambaya yayi koh zai iya ganin ta doctor yace masa ehh yana iya ganin ta kan su bata allura dan ta samu ta huta.
Koh da ya koma samu yayi har Ummin Niima ta iso hankalin ta a tashe. A tsaitsaye yayi musu bayanin da doctor ya masa kan ya shiga dakin da Niima take. Tana ganinsa hawayen ta suka dawo sabo. Shine ya matsa kusa da ita ya fara rarrashin ta yana fadi mata kar ta damu Allah za ya maido musu da mafi alkhairi. Su Ummi suka shigo suka duba ta basu jima ba dan doctor yace yana so a bari ta samu hutawa. Sahar da Yasmeenah suka wuce gida da alkawarin zasu dawo zuwa yamma in ta sama enough rest ita kam Karimatu tace babu inda zataje ta bar diyar ta dan haka waiting room din dakin ta koma ta zauna shikuma har aka zo bata medication yana ciki ta kankame shi ta hanasa barin gefen ta. Har sai da yaga idanunta sun fara rufewa alamum alluran da aka mata ya fara aiki tukun ya miqe yace zai je gida ya wanke jikinsa ya sa fresh clothes sai ya dawo. Bending down yayi to kiss her tayi muttering something he didn't understand into his ears. Be kawo komi ransa ba kawai yayi tunanin alluran barcin da aka mata ne ya sa ta sumbatu. Futowa yayi ya ma Ummi sallama yace zai je gida ya dawo ta masa fatan alkhairi ya kama hanyar gida ita kuma ta shiga dakin Niima ta zauna da ita. Sai a lokacin ta tuna ta kira Abdallah wanda yayi tafia zuwa Calabar for a business meeting. Yana ansawa ta fada masa yadda ake ciki cewar diyar su ta sama barin ciki dan dama Bakhtiar be fadi musu about the poisoning ba dan kar su daga hankalin su, haka kuma ya gargadi doctor da kar ya fadi musu dan baya son suyi panicking. He was going to handle things.
Yana shiga gida ya kira head of household staffs din gidan ransa a bace ya tambaye ta su waye incharge of kitchen. Su waye ke da haqqin yiwa matarsa girki. "I want them all sacked! Every single one of the kitchen staffs. Su tafi ki nemo sabbi, I will personally oversee their interviews". Yana fadin haka ya kama hanyar sama head of household staffs kam sai bin sa take tana bada haquri on their behalf.
"Megida ayi haquri. In abinci ne bayawa madam dadi zasu yi improving, ayi haquri". Juyowa Bakhtiar yayi a fusace yana fadin
"I almost lost my wife wa ke zancen wani rashin dadin abinci! Some goddamn person poisoned her. Nayi musu adalci da ban sa an rufe su ba. I lost my baby because of their negligence and all you have to say to me is sorry? I want each and everyone of them sacked kina ji na". Salati ta fara shikam be ce komi ba ya haye sama a guje. Wanka ya wuce yayi straight, kayan da ya cire daga jikinsa straight ya saka su a waste bin, baya buqatar qara ganinsu dan kullum ya gansu zasu dinga tuna masa da loss dinsa ne. Wankan sa yayi rai a dagule ya futo ya shirya. Sai a lokacin ya lura da blood inda yayi staining inda ta kwanta dan haka yayi waya akan a aiko da me aiki ta zo ta sanja sheets din.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...