VII

984 159 5
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

✍️ Ayshatuuu 💙

VII

Munyi nisa a girkin, Anty Rumasa'u ta shigo ta dube mu, Rayha ce ta tambayeta ko tana son Abu, Amma nikam barar Maggi kawai nake ban ko kalla inda take ba, ba tace komai ba ta Kara fita daf da zamu Gama ruwan zafin da muka rage ya barowa Rayha a kafarta, ta tsalla ihun da ni kaina seda na yadda laddle din hannuna saboda tsoratar da nayi, abinka da fara gurin yayi ja, kusan Anty Rumasa'u ta fara zuwa tana fadin

" Uban meye Zaki dinga yiwa mutane ihu ? Bakida hankali ne ko yaya?"

Muryar Baba mukaji yace

" Ruma what's this? Kin tambayeta me ya sameta tayi karar? This is nonsense!"

Se taja gefe tana kunkuni, ya kaarso ya Kama kafar ya Mata addua sannan suka fita, ranar Babu Wanda yaci abincin se ita daya, Bayan mun dawo daga asibiti da takeaway dinmu, Baba yace ta kwashe kayanta ta koma guest room, tunda ta shiga dakin Bata ma duba time ba kawai ta Kira Ummaah, tana kuka wai Baba yaci Mata mutunci, mun Rai na ta waye ya mutu waye ya dawo!

" Banda abinki keda kwanaki kadan ya rage mulkin gidan ya koma hannunki, meye matsalar ki? Shi dadin humiliation bazai Bari ki manta goal din daya kamata kiyi achieving ba, kada ki manta cin mutuncin dashi da yayan shi Suka Miki, seki Rama akan Hajara, idan har baki kwace wa Hajara farin cikin ta ba, to ki tabbatar Zan canja ki!"

Anty Rumasa'u ta sauke ajiyar zuciya, taji wani karfin gwiwa ya mamaye ta, duk duniya Babu matar data tsana kamar Ammi, tun ranar data fara ganinta matsayin matar Baba taji ta tsane ta haka kurum, ko Dan lemme not put it this way, dama can tana son Baba tunda Ammi ko ta girme ta ba zata Bata shekara biyar ba, dukda ba haduwa suke sosae ba Amma duk lokacin da Suka hadu se Anty Rumasa'u ta jangano wani abin. Baba yasan da hakan Kuma ya kawota ta zauna a gidan mu, shiyasa da abubuwa Suka lalace se naso na Masa uzuri se naji Bai canci uzurina ba.

Bamu da wayon da zamu gane lokacin da table yayi turning, daga disgusting look din da Baba ke yiwa Anty Rumasa'u zuwa wani adoring smile da yake Mata, dukka abin ya faru cikin sauri, kafin mu ankare ta karba ragamar gidan gaba daya, dake ta gama KASU ta je camp, tunda tasan da maganar Zama damu se akai relocating dinta katsina malumfashi, da kyar ta samu da naci da bin connections aka dawo da ita funtua, duk lokacin da zata fita Baba zai kaita, Muna zaune zata Kira tace ta gama yaje ya dakko ta, haka zai fita Koda dawowar shi kenan ya tafi dakko ta. Tun muna ganin normalcy abun har na fara jin tsoro cikin raina. Itama ganin ya fara shigowa hannunta se ta fara amfani da damar ta wajen cuzguna Mana idan baya nan,abinci a dafa Dan kadan Wanda bazai taba Isa ba, ko kuma my dawo daga islamiyya mu tarar Bata dafa ba, Kuma ta Hana mu mu dafa. Kudin da Baba ke bamu ta hannunta yake biyowa se ta siyo sabon piggy bank take zubawa a ciki. Ban taba damuwa ba Koda Rayha ta mini complain akan Anty Rumasa'u da abubuwan da take nace

" Nifa Twin wallahi ban damu ba, saboda nasan komai na duniya lokaci ne, duk abinda akeyi watarana zaa daina"

Cikin damuwa tace

" Amma twin role din Ammi take karbewa fa.."

Na rufe littafin dake gabana nace

" Don't think too much, bawa bazai iya canja kaddarar shi ba, kawai muyi musu addua"

Shikenan se muka hakura da maganar muka cigaba da Zama Muna kwasar takaici, ni se na daina zaman parlon yawancin rayuwata idan Babu islamiyya to Zaki sameni a study room din mu Ina karatu, ita Kuma Rayha tana kallo ko tana games din ta, yawancin Sudoku ko kuma puzzle, abinda da dai zatayi racking Brain din ta.

Wata ranar Friday, Baba yayi call so a asibiti ya kwana Bai dawo ba, tunda muka tashi wajen seven mukai tilawa se nayi wanka na tafi study room Ina son na gwada solving wani equation da zamuyi a ss1, Ina Yi Ina tsoma Pringles cikin mayonnaise Ina ci, Anty Rumasa'u ta tafi mo monthly clearance dinta, har wajen 10am sannan na fito na tashi Rayha nace

" Twin ke Kika kulle kitchen ne?"

Cikin rashin fahimta tace

" Kitchen Kuma? A'a ni fa tunda nayi wanka nake bacci period pains ke damuna"

Nayi Mata sannu sannan na fita, nasan ko da na tashi kafin Anty Rumasa'u ta fita na debo mayonnaise daga fridge din kitchen, Amma waye zai kulle? Ina nan zaune Ina tunanin yadda Zan bawa cikina hakurin yunwar da nake ji, Rayha ta fito sanye da skirt da riga, ta zauna da fuskar ta da tadan kumbura kadan saboda hormones.

" Ko Anty Rumasa'u ce ta kulle?"

Nayi tsaki nace

" Kai shiyasa Ammi tace miui hankali da ita, to meye abin rufe kitchen tunda abincin ba nata bane"

Haka mukai jugum jugum har wajen daya Baba ya dawo, freezer da zamu dauka drink itama ta Dade da kulleta da cire key din, mukam duk mun Zama marayu, lemo daya idan zaka dauka se ka amsa series of questions kafin ka dauka, ni kuwa bana jurar wannan na kwammata na daina Shan lemon. Duk wannan abubuwan Baba Bai sani ba tunda shi aikin shi ne a gaban shi. Ganin mu zaune yasan Yunwa muke ji, ya zauna Yana tambayar mu ko munci abinci, Rayha idanunta taf da kwalla tace

" Yunwa muke ji Kuma kitchen din a rufe"

Ya maimaita a rufe sannan kuma ya dakko waya ya Kira Anty Rumasa'u, tana dauka yace Mata Ina key, banji me tace ba Amma daga amsar shi na gane abinda ta fada

" Kuma makulli a jakar ki, kafa ce dashi da zai shiga ciki? How can you lock the kitchen and leave this kids starving?!"

Yayi ta fada karshe ta kashe wayar shi se kawai ya dauke mu muka fita ya siya Mana abinci. Bayan ta dawo ta dinga bacin Rai ko Baba Bata yiwa magana ba, Shima Bai kulata ba se ta shiga dakinta, ta fada gado ta Kira Ummaah tareda fada Mata abinda ya faru

" Na gaji Ummaah, kinji tsawar da yayi min Akan kawai na tafi da key din kitchen.."

Tsawa Ummaah ta daka Mata tace

" Rufe min baki shashasha kawai! Hajara ce kawai Target dinki, auren shi zakiyi ki suppressing Hajara. Kinsan yaran nan yadda nake son su, to bashi ba Nima Zan iya mantawa da alamar mu na ci muku mutunci akan su Sofy!"


Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now