XLI

1K 195 15
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XLI(41)

✍️ Ayshatuuu 💛

Saboda yamma tayi, Albi Kuma yace na kwana haka muka koma gidan ta muka daura sabuwar Hira. Ranar munyi hirar yaushe gamo ga mijinta baya nan se abin ya Kara Mana lokaci. Washegari da wurwuri na tashi na gyara Mata gidan sannan na fara Shirin tafiya, lokacin d ta tashi a bacci na Gama komai hatta breakfast, ta zauna tace

" Ke Sofy Wai da wurwuri Zaki tafi haka?"

Na Dan Harare ta nace

" To kwana Zan Kara Yi?"

Ta girgiza Kai tace

" Ina ce Albinki yace zai zo ku tafi tare"

Na girgiza kaina nace

" No min fasa wannan, Bari kiga"

Na Mike na hada tea na fara Sha

" Sofy yaushe za kice Masa ya tura ne"

" Lokacin daya shirya, nikam ai banida option Kuma"

Se ta gyara zaman ta tace

" Se Naga kamar Baki murna da tarayyar ku, se Naga Baki dokin shi kamar Bai dameki ba ma"

Nayi dariya nace

" Eh hakane, bansan dalili ba Amma bana jin irin wannan farin cikin ko kuma doki akan shi, how can I possibly do that? He's nothing near what I want, kawai dai Allah ya kaddara ne Babu abinda Zan iyayi"

" Sofy har yanzun kinada chance idan kina ganin Baki son Usman don't force yourself saboda kaucewa wani abu, beside har yanzun bakiyi girma ace bakida miji ba"

Na gyada Kai na nace

" Ba wai bana son shi bane, ba Zaki gane yadda nake ji bane, I'm in a state of despair, komai ya fita a kaina Rays, kullum mafarkina rayuwa ta nida Jaafar, ban taba kawowa Zan rayu da wani bayan shi ba se gashi ya tafi..."

Se nayi shiru kawai saboda yadda naji Abu Yana tsaya min a makoshi, hannuna ta riko tace

" Dan Allah ki daina fadar hakan, Jaafar is already in the past, idan Kika cigaba da sakoshi hakan zai raunana Miki imanin ki, to every action of Allah akwai great wisdom da mu ba zamu fahimta ba se shi kadai, you can't possibly question Allah akan abinda ya hukunta a rayuwar ki. Sofy kiyi hakuri ki karba koma menene Allah ya tsara Miki"

Har naje Gumel Ina tunanin maganganun ta, it really made sense ya kamata na hakura da Jaafar haka, idan na tuna shi addua kadai ta isheshi. Allah ya dauke shi a duniya saboda we were never meant to be.

Kamar yadda kowa zaiyi tunanin zamuyi soyayya sosae bamuyi ba ni da Usman, relationship dinmu is a bored relationship wani daga farko, wani lokacin se muyi sati bamuyi wayar minti uku ba, sede kullum zai kirani yaji yadda na tashi, Nima hakan Bai dameni ba. A hakan ya turo iyayen shi akai formal magana sannan aka saka Rana watanni bakwai zuwa lokacin na kusa final exams Dina, Ranar da ya kirani shi ne mukai kusan minti talatin Muna magana dashi, he kept complaining me yasa zaa saka wata bakwai

" Kai Albi wata bakwai din fa kamar yau ne"

Se yayi tsaki yace

" Ba Zaki gane ba Gem, na jira da yawa fa"

" Bana son muyi aure Kuma Ina tafiya school, nafi son na Gama school I can dedicate myself to you"

Yayi murmushi yace

" Gem ke Kika fadar haka? To shikenan Allah ya kaimu lokacin"

Mun Jima muna tsara rayuwar mu ranar. Bayan nan na fahimci wani Hali da Usman yake dashi, shi mutum ne da baya nuna true feelings dinsa, duk yadda nake ganin I'm reserved to shi ya fini, halayensa suna da sanyi, Kuma Bai iya chasing Abu ba, akwai mutane da duk yadda suke son Abu they can't chase it, wannan dalilin yasa lokacin da yake Bina na aureshi idan naki se ya kyaleni, idan ya Kara samun chance se ya dago da maganar idan naki se ya hakura, akwai ranar da ni na kirashi na dawo daga clinic, Bayan mun gaisa ya tambayeni ko naci abinci nace naci se muka fara Hira har nace mishi

" Albi Ina son na tambayeka"

" Oya go on Ina jinki"

" Me yasa lokacin idan nace bazan aureka ba kake hakura baka kokarin tura kanka gur ina. Kasan Mata basa son irin haka"

Yayi dariya kadan yace

" Wallahi na sani Nima bansan me yasa nake haka ba, kawai dai hali nane, bawai zuciya nake ba Amma bana son takurawa mutum. Amma kinsan se inajin what if idan na rasa ki gaba daya Kuma, ba yadda zanyi ne"

Na gyada Kai nace

" Wannan halin naka Yana taba ego din Mata, yawanci min fi son a dinga binmu head and toes"

Yayi dariya yace

" To ai gashi Allah yayi, saboda I didn't chase you Wai saboda bana sonki ba Aa kawai Ina ganin rayuwar ki ce, ke Zaki zaba yadda kike so"

Bayan wannan se wani halin shi Dana karanta Kuma, shi ba mutum bane Wanda yake bada time din shi, ni dashi muna speaking different love language, maimaikon mu dinga samun matsala ko nayi ta complain se na Bari akan ni Zan canja shi, Zan maida shi ya fara speaking yaren da nake fahimta. A wañnan watannin da Suka rage Mana se Dana tabbatar mun fara fahimtar junanmu.

Na tashi da safe na Gama dukkan abinda nake, na saka labcoat dita Dan zuwa clinic, wayata na Ciro na fara Kiran shi, kafin ta katse ya dauka

" Good morning!"

Yana murmushi ya amsa ni sannan na gaishe shi nace Masa

" Albi Zan tafi clinic na Kira na fada maka Kai min addua"

Ki a yanayin maganar shi nasan yaji dadi yace

" Allah ya bada saa ya tsare min ke, kiyi hankali da patient din ki Kar su cije ki"

Nayi dariya saboda na tuna na bashi labarin Kare ya kawo min cizo, daga haka mukai sallama yace min shima ya fita aiki. Can da Rana na Kara Kiran shi naji yadda yake,se ya zamana ni nake calling din. Seda nayi sati daya kullum duk abinda zanyi se na fada Masa shima zai fada min nashi, bayan sati se na daina Bai Kira ba shima se washegari very early daidai time din da nake fita ya kirani yace min zai fita, ni na fita nace Masa Ina dai kokarin fita, daga haka se ya zamana duk abinda zaiyi zai fada min, a kalla a Rana zamuyi waya kamar sau uku sannan muyi chatting. Abinda nake son mu gane there are things that you can change through action, ba wai se magana ba, a zauna baka Kirana, idan kana son Abu ba zaka ce side daya zai ta Kira ba, dukka ku biyu have to make effort to make it happen.

Haka muka cigaba da tafiya, relationship dinmu was slow and steady, ba irin me zafin nan bane, kafin wani lokaci na fara jin shi a cikin duniya ta, naji Babu yadda zaayi na hada soyayyar shi da ta wani, it's a taboo wani ma ya kalleni yace Yana Sona. Tafiyar mu tayi nisa munata Shirin aure muna Kara fahimtar junan mu.

Usman Dan bafullatanin adamawa ne, iyaye da kankanni duk can suke Amma Kuma shi a Gombe aka haifesu. Mahaifiyar shi bakanuwa ce typical bahaushiya, shiyasa ba zaka kalle shi kallon farko kace shi fulani bane, sosae yake Kama da mahaifiyar shi. Mahaifin shi sun rabu da mahaifiyar shi tun Yana yaro, ya tashi a adamawa wajen kakar shi, dukka sauran Yan gidansu yan uba suke a gurin shi. Bayan ya Gama primary kakar ta rasu Dole aka dawo dashi wajen Babar su Anty yusra. Zaman dai Babu dadi ko kadan, haka a daddafe yake zaune Amma Yana zuwa Kano wajen mahaifiyar shi data riga tayi aure ta Tara nata iyalin. Kubra ita ce matar shi ta farko da aka Masa auren gata da ita, Dan lokacin daya aureta ko aiki Bai fara ba, baima Gama service ba. Tana da kirki kamar yadda Anty yusra ta fada min, dukda shi baya zancen ta, idan Muna magana baya kawo zancenta, Nima nafi son hakan. Yayi karatun shi na engineering a BUK. Yaran shi Afaf da Afreen.




I'm sorry yayi kadan page din, na kwana biyu banyi ba saboda na koma makaranta, exams Dina ta kusa. Ina muku fatan alkhairi se Kun jini. Ku Kara hakuri.

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now