XVII

1K 194 10
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

XVII

✍️ Ayshatuuu 🤎

Jigawa is 30 today! Allah ya albarkaci jahar mu, Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali me dorewa...May it continues to stand tall among others... Allah ka bamu shugabanni na gari kamar #Baba Lamido# We'll continue to hail you and honor you. Jigawa a fast growing city, it's a new world, it's mother with a long breast that suckle it's children to nourishment. #Hail mother and Father land#

Haka muka dawo ni da Anisah muka shiga ciki muka kwanta, Bayan duk sunyi bacci na kasa bacci se tunanin Ammin nake, she's so much extra careful akan kada mu kwana mu kadai, dalilin da yasa Bata fiya yin bulaguro ita daya ba se damu, duk Dan kada mu kwana mu kadai, Amma kalla mu kadai din muke kwana. Nanma se na dasa sabon kuka kafin bacci me nauyi ya daukeni. Bayan munyi sallar asuba na dakko littafai na fara boko saboda I'm far left, gashi mun kusa komawa makaranta baifi kwanaki ya rage ba.

A Dan ladin gumel, Ammi ta Isa gida da tsakar Rana, kallonta kadai idan kayi kasan Bata cikin nutsuwar ta Koda da abinda ke jikinta ya Isa ya baka amsa. Babu tsammanni se sallamar ta Baba ta ji, gidan duk ya tashi Inna ta rasu, ta ukun ma ta rasu, dama sune Yan mulki su Suka Hana zaman lafiya gidan Kuma duk Basu nan, yaran gidan duk sun dare yawancin sunyi sure wasu kuma sun tafi wajen nema ko makaranta, Yan gidan su Ammi su ashirin da biyar ne, ita kadai ce Bata da mahadi, ita daya Baba ta haifeta. Da anyi zaman kishi, zaman tsangwamar juna, iñna tayi mulki ta juya gidan dashi kan shi Alhaji, to Amma meye makomar ta? Cuta tayi kamar ta haukace, tana daki sede ku ganta tsakar gida, idan Baku rike ta ba se ta fice. Yayan da tayi fada akan su suka kasa tsinanan Mata abin kirki, which is obvious, hakan Yara suke ki saida komai naki saboda su, ki zalunci wasu saboda su Amma karshe ba abinda zasui Miki, Dan kullum yayanta cewa suke ta cuce su! To me yayi zafi?. Ya kamata mun hankalta mu gane Allah yace namiji yayi aure Kuma a gidan aure shi ne shugaba, there's no point ko reason da mace zatai seizing wannan damar ba, idan kikai haka kin bijirewa umarnin shi, kinyi fito na fito da ayoyin shi. Har kullum Mata ba zamu daina Shan wahala ba saboda mune matsalar kan mu, Abu me wuya, ni ban taba ji ba ace uban mijin ta ya takura Mata, sede uwar miji, ita kanta mace ce Kuma kilan ita ta uwar mijinta treated her right Amma ke tace baza ki Sha ruwa me dadi ba, Ina ce Mata min ce ciwon ' ya mace na ' ya mace ne? Ko mun hakura munyi giving up, idan dangin miji kike fama da matsalar su zakiga yawancin su Mata ne, su sun manta Suma wani dangin suke aure. Idan kishiya ce Kuma haka zata dinga muzgunawa Yar uwarta mace, da ace zamuyi teaming akan namiji Allah Bai Isa yayi wani abin ba, the more we divide haka zamu ta Shan wuya. Ya kamata mu farka mu fahimci how far muke destroying kan mu. Mu Mata ne ya kamata muyi sticking for our women bawai mu uzzura musu ba. Yawancin Wanda suke kangararru gidan miji ki duba zakiga they were traumatized, either kishiyar uwarta ko kuma dangin ubanta sun muzguna ma Babarta shiyasa take ganin ki dai ta Rama, ko kuma fear din Kar ta Kare kamar uwarta se itama ta kauce Hanya. Kije kiga matar da kishiya ta uzzura Mata, ko kuma miji ya zalunce ta, duk ranar da ta bar gidan tayi wani auren se ta nemi Hana zaman lafiya a sabon aurenta, saboda tana ganin ba zaa maimaita ba.

A cikin zuciyata babban tanadi na yiwa kishiya, inada cikinta bazan taba Bari bakin cikin da Ammi ta dandana Nima na dandane shi ba, tun a wañnan lokacin nayi deciding, banida fitina Amma Baba ya dasa min iya cikin zuciyata! shiyasa zamana da Kubra ya Zama tashin hankali! Baba taji gaban ta ya Fadi ganin Ammi da tsakar Rana, tana shiga ta zauna tareda cire hijabin jikin ta tace

" Baba Ina wuni?"

Baba ta amsa jikin ta a sanyaye, mussaman jin muryar Ammi da tayi Babu kuzari, ga damuwa a tattare da ita, Kuma tasan irin zaman da Ammi keyi da Baba. Ruwa ta kawo Mata tace

"Ki Sha! Zakiyi wanka?"

Ta gyada kanta sannan ta hada Mata ruwa, gidan an gyara shi sosae saboda an samu masu rufin asiri cikin zuriar tasu, dukda Ammi ma ba karamin kokari tayi ba. Ta zage tayi wanka Allah ya taimaka tana da Kaya baifi guda uku ba data taba kawowa ta aje, se kawai ta saka ta samu tsakar dakin ta kwanta, gidan shiru se ta fara tuna yadda gidan su yake, lokacin kowa ba wani santa yake ba, ba dama tayi motsin kirki, dadin ta daya mahaifiyar ta da mahaifin ta, su Suka taimaka wajen zamewar ta uwa ta faru gare mu, gashi yanzun ta dawo matsayin bazawara Kuma, ita ce aurenta da Baba ya mutu, ita ce Baba ya saka sakin wulakanci, yarta ya bawa takardar sakin ta, tayi tunanin duniya ta kasa figuring laifin da ta yiwa Baba, tasan lafiya kalau Suka kwana, Dan wannan Daren he kept telling ya Yi kewar lokacin yarintar ta dukda ba wani canja Masa tayi ba, tana nan a hajarar da ya sani, they were so intimate a Daren, tamkar zai maida ta cikin shi, da zai tafi sallah lafiya Suka rabu, to me ya faru...Ta kasa daina tunanin possibility sakin, Bata son zargin kowa Amma ta sani ba zata taba yafewa Wanda ya dagata daga kan yayanta ba, se kuka, ta fara kuka data tuna mu, ta tuna how fragile we were, rayuwar mu uwar mu kawai muka sani, komai ita ke Mana, duk abinda muke so gurin ta zamuje, yau ta tashi Bata tare damu. Cikin kukan taji sallamar Alhaji da Baba da kuma Kawu Saleh babban yayan su, Yana son Ammi ko da can, ya damu da lamuran ta saboda Yana ganin gaba daya rayuwar ta abin tausayin ce. Ganin kukan da take yasa duka Suka tsinke da lamarin, Babu tantama auren ya mutu, ko da suka zauna haka ta fada musu. Alhaji yace kada taji komai, aure dama Rai ne dashi ta kwantar da hankalin ta Allah yayi zaman su ya Kare, mu kuma Allah zai kiyaye mu, Kawu Saleh ma haka ya Mata nasiha se taji sanyi tunda ta samu support dinsu, ita tashin hankalin ta mu ne, a wanne Hali muke ciki? Ta tuna yadda muka rirrike ta da zata tafi Muna kuka tareda rokon ta kada ta tafi.

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now