IX

938 165 1
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

IX

✍️ Ayshatuuu 💙


Bayan ya tabbatar zaman Anty Rumasa'u gidan mu Kara lalata komai zaiyi, se ya fita ya sameta a dakin tana zaune tana Shan wani abu cikin cup, Zama yayi tareda fadin

" Rumasa'u"

Tunda ya shigo take kallon shi, Bai taba shigowa dakin ta ba se wannan lokacin, farin cikin da take ciki yasa Bata lura da Yanayin da yake ciki ba, seda taji yanayin yadda ya Kira sunanta se ta aje cup din tareda kallon shi Amma Bata amsa ba, kudi ya Ciro ya Mika Mata, kafin yayi magana tace

" Kudin meye wannan?"

Ya Sosa kanshi yace

" Kiyi hakuri, Zaki koma gidan Baffanki kafin lokacin da Zan shawo kan Hajara"

Da mamaki ta kalleshi, ranta ba karamin baci yayi ba ta bude baki zatayi magana yace

" Dan Allah Kar kice komai, kiyi packing lokaci na tafiya, dare zaiyi"

A wañnan lokacin tasan idan har tayi fada bazai taimaka ba sede ya Kara hasala shi hakan yasa ta fara kuka tace

" Yanzun doctor a gidanka zaka koreni?..."

" Ba wai korar ki nayi ba, kawai kije idan komai ya lafa seki dawo, keda Zaki dawo dindin gidan ma"

Maganar shi Banda Kara Bata Mata Rai Babu abinda take, ta Mike a fusace tace

" Kana nufin ka zabi matarka a kaina kenan?"

Bai ce Mata komai ba Amma a ranshi Yana ayyana me yasa Mata suna da matsala ne, idan ba haka ba meye na hada kanta da matar shi, shi akan Ammi Babu abinda ba zaiyi ba. Yana tsaye haka ta dauka necessary ta fita a gidan tareda Shan alwashin ranar da zata dawo gidannan mazauna gidan se tayi musu abinda har duniya ta nade ba zasu manta ba.

Bayan ta tafi ya koma gurin Ammi dake kitchen tana hada abinci, ko kallon shi batayi ba, Shima se ya fita kawai Dan yasan ya Bata Mata Rai. Bayan sallar Isha ya dakko mu muka dawo, gidan shiru Babu dadi, Ammi ta gimtse fuska shi Kuma komai daridari yake. Haka gidan ya kasance har karshen sati muka tafi Gumel. Anty Rumasa'u na gidan wani baffanta anan wajen jabiri suke. Ta Kira mamin ta ta fada Mata, hakan yasa matar ta dauki alwashi. A Dan ladin Gumel muka fara sauka ta aje musu tsaraba ta dauka Anisah muka wuni anan, da suka kebe itada Baba ta zauna ta fada Mata halin da take ciki, iyayen mu ne nada se ta Bata hakuri tace Mata watarana komai zai wuce, tayi kokari ta kyautatawa mijin ta ta Kuma rikemu ta kula damu. Se dare muka koma Gumel. Seda mukaje mukaji wai an matso da bikin zuwa sati uku, bayan Gwoggo ta gama tausar Ammi wadda tayi daurewar duniya batayi kuka ba, Amma gaba daya haushin Baba takeji ko gaba suke ya kamata ya fada Mata cewar zaiyi aure. Bayan ta dawo gida ta same mu mun dawo daga gidajen da ta lissafa Mana muje, gidan Yan uwan baban mu. Ta shiga daki ta rufe tayi kuka kamar ranta zai fita, mukam kwana biyu munsan Bata jin dadi kamar yadda ta fada Mana, se bamu dame ta ba, Amma nidai Ina tabbatar wa kaina cewar something somewhere is definitely wrong. Duk lokacin da Naga Ammi tana cikin bacin Rai se naji nawa ran ya baci, idan da akwai abinda Zan bayar Naga ta dawwamma a farin ciki da tabbas zanyi shi.

Washegari muka koma Funtua, Baba Yana asibiti kamar yadda ya fadawa Ammi, se muka maida hankali muka gyara gidan sannan muka Yi girki, se dare Baba ya dawo , lokacin dukka munyi bacci se Ammi dake parlo tana jiran shi. Can Ina bacci nake jin kuka a hankali da maganganu, se na sakko daga gadon da nake kwance na zo kofar parlon na tsaya, daga inda nake Ina hango Ammi da Baba na zaune opposite each other.

" Zakai aure kwanaki kadan Suka rage ba zaka fada min ba, wanne irin Zama muke? Kana ganin ni na isa na hanaka ka aureta? Kasaani tunda na dawo Babu abinda nake tsinta cikin gidannan se bakin ciki da takaici. Ka darsa min abinda bazai taba goguwa a raina ba"

A hankali na sake lafewa jikin curtain din tareda rufe bakina, Baba zaiyi aure? Maganar da yayi ta katse min tunanin da nake

" Ni dai kullum hakuri kawai Zan baki"

Daga haka bai Kara cewa komai ba Ammi ta mike se nayi saurin komawa na kwanta, Amma bacci ko daya ya gagara a idanuna, se juyi nake inajin wani nauyi a zuciyata. Da safe na tashi jikina a mugun sanyaye, ko shara da kyar nayi, nayi wanka sannan na tafi study room, kilan acan I'll find something pleasurable na karanta. Ina fata karatun se na manta da abubuwan da Suka faru. Wannan kwanakin sun zamo mabudin fara lalacewar abubuwa a gidan mu, Zan iya cewa bayan korar Anty Rumasa'u da Ammi tayi Bata Kara kokarin kwatar kanta ba, daga baya ma se ta tattara komai ta watsar ta Kara rungumar Baban se zaman gidan ya koma lafiya.

Baa dauka lokaci ba akai biki na gani na fada a Gumel, Baba ya cewa Ammi Yana son taje tace Masa ba zata je ba, muma Kuma ba zamu je ba. Se kawai ya tafi shi daya, Bayan ya tafi Ammi ta fada Mana cewar Anty Rumasa'u zata aura Baba, tana son duka muyi hakuri da wasu abubuwan da zamu gani sun canja, kada mu sake muyi Mata rashin kunya sannan duk abinda ta samu na aiki ko aike to muyi Mata.

A Gumel ta fara Zama seda sukai kwanaki bakwai dinsu cif sannan ya dakko ta suka dawo Funtua, ya riga ya saya gidan dake gefen mu ya hada da namu, so part dinta Yana gefenmu, Ammi tayi girki ta Kara gyara gidan, Dan ya canja Mana dukka furniture dinmu. Yayi Mana sabbin paint so se muma gidan ya koma kamar sabo. Basu dawo ba se yamma, ta gate dinta ya shigo shiyasa bamu ji Kara ba. Seda sukai settling sannan ya shigo part dinmu, muna zaune Ina cike form din da zaa Kai Anisah makaranta, Rayha na Shan cornflakes.

" Baba sannu da zuwa!"

Muka hada baki muka Masa sannu da zuwa, ya dauki Anisah ya Mata Wasa Yana amsawa sannan Ammi ta fito tayi kyau cikin wani coffee din material, fuskar ta dauke da murmushi tace

" Sannu da zuwa ya Hanya? Ya amarya Allah ya Sanya alkhairi!"

Yayi murmushi bayan ya zauna yace

" Nagode sosae, Allah ya muku albarka!"

Ta amsa da Amin sannan ta tambaye shi ko a kawo abinci yace Mata Yunwa yake ji, ta zuba Masa sannan ta zuba wani a cikin warmer tace Rayha ta Kai mata. Tasan halin mu duka shiyasa ba tayi gigin aika ni ba. Kafin Rayha ta fito a kitchen din mukaji sallamar Anty Rumasa'u, Ammi ta amsa Mata se gata ta shigo looking elegantly cikin wata atamfa, tayi kyau Babu karya. Tana Murmushin nasara ta shigo ta zauna, Ammi ta Mata tayin Zama, ta zauna kan kujera sannan ta gaida Ammi, muma muka gaishe ta ta amsa tana daukar Anisah wadda ke Wasa da Teddy dinta. Anan taci abinci sannan ta tafi. Gidan ya koma normal, Babu wata matsala, kullum Anty Rumasa'u na part din Ammi anan take yini se dare take tafiya, idan ranar girkinta ne kuwa tun kafin ya dawo zata koma can.

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang