Chapter 8

25 2 0
                                    

*HUBBUR-RUH*

written by meerarh

*page 8*

ELEGANT ONLINE WRITERS

********
اللهم انت ربي لااله ال انت, خلقتني , و انا عبدك و ابا علي اهدك ووعدك, اعوذبك من شر ما سنعت ا بوع لك بنعمتك علي و ابوع بذنب , فغفرلي فانه لا يغفر الذنوب الا انت.
****       *****      *****      *****

12:00 am
Habban Idraaq Nuwaerah Intisaar nagani sun shiga motan Intisaar sunnufi gida, koda suka isa gida sosai diana tayi kukan farin ciki, shima Abboo dauriya kawai  yakeyi,  shikuwa Idraaq kasa shigowa yayi sosae yakejin kunyan Abboo da Diana , saida Habban ya koma ya jawo hannunshi sannan yashigo ciki badan yasoba, ko bayan ya shigo kasa daga kanshi yayi  saboda gani yakeyi bema kamata ace yanananba kamata yayi ace yana under police custody,Noor ce taga duk ya kasa sakewa ta rike hannunshi , c'mon Idraaq mekakeyi haka kasaki jikinka mana, murmushin dole ya kakalo sannan dakyar ya budi baki ya gaida Diana da Abboo, suka amsamasa cike da sakin fuska saboda su komae ya wuce agurinsu,
nan sukayita janshi da hira  har ya saki jikinshi, acikin hiranne Abboo yayi musu nasiha sosae dan Idraaq har kuka yayi yana kara rokon gafararsu,

Abbo yayi gyaran murya sannan yafara magana, toh godiya ta tabbata ga ALLAH daya nuna mana wannan lokaci , ke Nuwaerah kwana biyu kenan da haduwanki da Habban kuma ni amatsayina ta mahaifinki na yanke hukuncin daban saniba ko zaki amince dashi amma ina saran bazaki bijirewa umarnina ba, dazu da safe da Habban yazo...

flashback

koda Diana takai Habban gurin Abboo suka gaisa, nan Abboo yabukaci jin cikakken tarihinsa, Bayan Habban ya gama bashi labarin rayuwarsa ne Abboo ya yanke hukuncin daura musu aure, aikuwa basuyi sanya ba Abboo yasa Habban ya kira danginshi video call, koda yakira yayi musu bayani , sosae sukayi murna saboda sun dade sunason ya karayin aure, aikuwa anan aka daura auren akan sadaki mafi darajar aure

end a flashback

suman zaune Nuwaera tayi can kaman bayan mintuna goma ta dawo hayyacinta tafara kuka kaman ranta zai fita daga gangan jikinta, yanzu daman da auren Habban akanta aka mata wannan cin zarafin, wani irin kallo tayiwa Idraaq dayasa cikinshi yaduri ruwa, sai kuma tayi kokarin saita kanta tafara magana, Abboo kai mahaifinane, komae kayimun arayuwana baxan bijirewa hukuncinka ba , sannan takalli Habban.datunda suka.shigo baiyi wata doguwar maganaba, Deeda ina fatar zaka iya rayuwa dani ayanda nake dukda komae agaban idonka yafaru ina neman gafararka ka yagemun sannan idan aurena zai zamemaka matsala after all that happens kasawakemun takarasa fadar haka tana zubda wasu irin kwalla basu ban tausayi, inda take ya matso sannan yace, kidaina fadan haka, kedin rayuwata ce ke duniya tace kece mace ta farko bayan matata, ji tayi zuciyarta ta wani irin dokawa da karfin tsiya, acikin ranta tana fadin, nifa na manta dayanada mata, aikuwa kuka ya kufcemata, duk sukayo kanta suna tambayan me yafaru, nan tafara magana,
nidai kataimakeni ka sawwakemun, bazan iya rayuwa damai mataba, ni nama manta dakanada mata Allah sarki ni yanzu yazanyi da rayuwata, ai kuwa gaba daya su Abboo har da su Idraaq suka kyalkyale da dariya, sai lokacin ta fahimci tabaran datayi , da sauri tashige kirjinshi ta rungumeshi tana sakin murmushi , aikuwa duk suna ganin haka suka tashi suka fita daga palon Abboo zuwa palon Diana, nan su Intisaar sukayi musu sallama shima Idraaq yakara basu hakuri tareda tabbatar musu zaikai kanshi dan ayanke mishi hukuncin da yayi daidai da laifinsa, bayan sun bar gidanne Abboo yakalli Diana tareda fadin ina fatan su daidaita kansu ina matukar son su kasance tare, Diana ta matso jikinshi ta rungumeshi tafara kuka dan har yanxu tanajin zafin abunda yafaru da diyarta, shikuwa Abboo sai arrashi yakeyi.
bangaren su Nuwaera kuwa koda suka fita dago fuskanta , yayi yana karemata kallo, isn't it so soon shekaran jiya muka hadu amma har an daura mana aure, itama kallonshi tayi , is not   so soon Deeda, bata fuska yayi sannan yace ni kawai ki daina kirana da Deeda wannan na 'ya'ya nane, sai sannan tace to wai ina matanka ta karasa fada tana kallon cikin idonshi cike  fargaban abunda zai fito daga bakinshi, shina cikin idonta yake kallo yafara magana, matana tana garinmu, aikuwa batasan sanda wani kukan ya kufcemataba, saida yaga abunnata nayi ne sannan yace, Nuwaerana, dagowa tayi tana kallonshi, matana ta rasu shekaru biyu kenan kece mace tafarko bayanta, sai lokacin ta saki wani nannauyan numfashi har yana iya jiyowa, sai kuma takalleshi cijeda tausayawa tace, am sorry for your  lose , fuskanta yashafa yana mata wani irin tsadadden murmushi, kaman amafarki taji bakinshi anata, aikuwa tazaro ido tun tan nokewa har tabada kai bori yahau, saboda ita arayuwanta ba abunda ke burgeta irin kiss, aikuwa  nan suka shantake saida taga abun naso yafi karfinta sannan ta fara tureshi ina yayi nisa, saiga Diana tashigi dan taga sun dade basu fito dan lokacin kusa 3:00am, aikuwa tan shigowa karaf idanuwanta suka sauka akansu, ai aguje ta juyo karan gudun dayaji ne yasashi dawowa hayyacinsa, kallonta yayi cikeda shauqin so da qauna yace taso muje kar su Abboo suga mun dade, dakyar ta mika mishi hannunta saboda wata iriyar kunya da tayi mata dirar mikiya, koda suka fito palon Diana kallo daya tayimusu ta dauke kai, saboda sun bata kunya bama zasu bari su bar gidanba, aikuwa Abboo naganinsu yasa dariya sannan yace, Habban dan Allah bayan anyi sallar asuba kadauki matanka ku wuce abar mana Hidata nan ku ku tafiyanku, saiji sukayi Diana tace bama sai anyi sallanba kawai kawuce fmda ita yanxu za'a aikomata da kayanta, cikeda mamaki Nuwaera ke kallon Diana da alamun tambaya afuskanta, eh aikinji me nace wallahi baza a samarman jika acikin gidana ba, sai lokaci suka fahimci abunda take nufi, ai kuwa Habban ma dariya yasa sannan yace, haba Diana ina laifi idan ansama miki jika acikin gida, ai kuwa Abboo kamar jira yakeyi yace, ai kuwa Habban bakayi karyaba ai Nuwaera najin Abboo yasoma magana ta ruga aguje tabar gurin, sororo Diana tayi tana kallinta to kaji iskanci ashe daman kinada kunya, sai kuma tajuya takalli Habban sannan ta umurceshi daya zo inda take, aikuwa yaxo zai zauna kasa ta ce ya zauna agefenta, bayan ya zauna tafuskanceshi sannan tasoma magana, daga yau babu kai babu maraici , nice mahaifiyarka sannan Abbo shine mahaifinka dagayau duk abunda kakeso kayi mana magana mune iyayenka sannan bayan kwana biyu zamu tafi gurin dabginka, sosae yake kuka tunowa da mahaifanshi sai ya rungumeta yana fadin, kin gamamun komae Diana nagode sosae da karamcinki , kun bani 'yar ku batare da kunsan danginaba, sannan yanxu kun zamemun iyaye nagode sosae, sai kawai sukaji muryan Nuwaera tana fadin , ai gashinan kun sakamun miji kuka dan Allah ku kyaleshi, nidai HUB dan Allah katashi mutafi, ai kuwa duka sukayi sororo suna kallonta cikeda mamaki, batayi wata wataba ta karaso inda  yake gefen Diana tafara goge mishi hawaya, ti hakuri kaji HUB tashi mutafi, muryan Diana taji tana fadin to tashi Habbab karta kullacemu tace mun hana mata mijinta, duk suka sa dariya nan dai Abboo yayi musu nasiha sosae sannan shida Habban suka nugi masallaci itama Diana batayi kasa aguiwaba tashiga ba 'yar ta shawarwari akan zamantakewar aure , saboda Diana bata damu da ko yakukeba idan ta kama sosae takeyimaka bayanin koma meyw, hardai Nuwaera ta fara jin kunya,
bangaren Habban ma haka  kamar abokai haka Abboo yayita bama Habban shawarwari kafin su dawo daga masallaci har Diana tashirya Nuwaerah gutin karfe 7:00am aikuwa suna fitowa da Noor taga da gaske tafiya zatayi sai tasa kuka, dakyar dai suka lallabata suka wuce, cikin motama haka tayita sheshshekar kuka tun yana rarrashi har yagaji ya kyaleta ..

😴😌barci , wai bara natsaya anan nagaji☺ toh how is it goinna be agidan Habban da Nuwaera to wai ina Intee da Idraaq ya labarin Dr.aman, muhadu a next chapter

𝐻𝑢𝑏𝑏𝑢𝑟_𝑅𝑢ℎWhere stories live. Discover now