TUN RAN GINI TUN RAN ZANE!.
Khairat Up.
Vote @wattpadkhairi_muhd.
Karamci Writers Association.
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)04.
Da fitar Alhaji daga gidanshi gidan Alhaji Mudan ya nufa a fusace ko da ya karasa ya gan shi a kofar gidan sa tare da yaran shi samari su uku cikinsu bai san waye Kabeer ba kawai ya karasa gun Mudan ko sallama babu kana ganin shi kasan ranshi a mugun bace yake.
Baba ga Alhahi Umaru nan .
Da sauri ya tashi jiki na rawa ya karasa gurin shi suka yi musabaha sannan suka yi magana kasa kasa.Mudan ya yafiyo yaranshi da hannu ya yi musu magana sannan suka shiga motar Alhaji Umaru suka bar unguwar.
*.
Sak'on Gwagwo na isa kunnen Alhaji Iro ya shiga cikin gidan ya kira Aliyu a dakinsu shi ka sameni a jikin mota yanzu ka kintsa kan ka.
Cikin gida ya kuma shiga ya sami Umman tana kwasar tuwo Firdausi dauko hijab din ki zamu je gidan Gwagwo yanzu. Saida gabanta ya fadi lokacin da taji kiran na Gwagwo ne Allah sa wannan tsohuwar ba wani abin zata yi ba dan wannan karon bazan yarda ba wata zuciyar tace " infa tasa danki ya sake ki fa?." Tabdi Innallilahi.
Firdsusi kina ina ne?.
"Gsni nan Alhaji."
*
Har su Alhaji Iro suka karasa gidan Gwagwon ba a ga Alhaji Umaru ba sai can iliyasu ya gano shi a baki masallaci sai washe hak'ora yake yi ya kasa rufewa tsabar mugunta da bakin hali.
"Yaya aka yi ne Iliyasu?."
"Alhaji! Gwagwo ke neman ka daman tun dazu nake cigiyar ka."
"Ah ayya ina nan ban san ana yi ba muje ko muje , muje. Murmushi ya ki barin fusakar shi domin kuwa shi kadai yasan abin da ya shirya. Kuma jikin shi ya bashi wannan kiran na Gwagwon a kan Aliyu da Rauda ne kuma yayi maganin abun kenan Khadija can ta wuce."
*
Jigum suka yi a katoton tsakar gidan nasu wanda aka malale da tabarmi.
Banda zare ido da harare harare babu abin da Umman keyi dan ko ta ga Khadija a gurin ta tsani ganin ta ba kadan ba musamman ma yanzu da ta ga Iro a gurin.
Sallamar Alhaji Umaru ce ta katse musu shirun suka amsa tun a bakin kofar Alhaji Umaru ya sha mur ganin Khadijan shi ga Iro kenan ma sun gama ma tattaunawa a tsakaninsu babu wani abu marar kyau da bai raya a cikin ran shi ba kishi dai ya zame mishi tashin hankali da rashin nutsuwa a rayuwarshi ya ki sakin jikinshi yayi rayuwa kamar ko wanne magidanci ko da yaushe zancen shi Iro na neman rabashi da matarshi abar son shi.
"Barka da dare Gwagwo."
"Barka."
"Umaru wato duk abin da yake faruwa ina sane kuma ina ji ina gani ko ds na goyi bayan marigayi ya baka auran Khadijatu na ba dan komai bane sai dsn ya isa dani amman ba dan ina son ka fiye da d'an yar'uwata ba."
Wannan magsna ta k'ona ran Alhaji Umaru ba kadan ba sannan ya kuma murtuke fuskarshi .
"Sannan duk abinda kake yiwa yata tilo ina sani kuma ina ji ina gani kawai bana son shiga hurumin aure ne, ka hanata zumunci da dan uwanta tilo sabida mugunta nayi shiru ka hanata sakat ba fa tsoronka ni nake yi ba balle tsoron ka Khadija keyi ba aa wannan auren dake tsakanin ku shi ne ya zama katangar da ta daga darajarka a fuskokinmu da ta Yaya ne ma da tuni komai ya kare amma saboda ni take shiru to ahir dinka Wallahi kaji tsoron Allah ka ji tsoron hakkin zumunci da kuma hakin uba kan ya'yanshi."
Muryarshi a sarke kamar zai yi kuka ya ce "Allah huci zuciyarki Gwagwo wani abin aka ce nayi?."
"Meye dalilin ka na kin yarda da batun auren Rauda ta da Maigidana?."
"Gwagwo kiyi mini afuwa na riga da na bada auren ta ne wa dan abokina Kabeer."
"Toh a warware tunda ba a amshi dukiyarsu ba ko ds an amsa a warware ni nan na bada wannan umarnin Raudata matar Aliyu na ce da yardar Allah."
Carf Umma tsyi ta ce "kiyi hakuri Gwagwo ban yarda Aliyu ya hada iri da jinin Khadija ba sam ban mishi izini ba a matsayina na uwarshi."
"Firdausi daman ai ke annamimiya ce ni na sani duk abin da kike shiryawa na sani da ke ds waccan munafukar mai aikin taki Zulai toh Wallahi ki kiyaye gamuwarmu shiru ba tsoro ne ba gudun magana ne. Ke har kin isa in hada jini dake? Wallahi da ace babu jinin Heemu a jikin Aliyu baki isa na yarda danki ya auri yata ba saidai kash kaddara ta riga fata akwai jinin Heemu a jikin Aliyu ni bazan raba zumunci ba duk cin amanar da kika yi min bai isheki ba har zaki bude baki kice za ki yi min habaici to da yardar Allah Aliyu sai ya auri Fatima. Saidai ke da Uban nata ku hadiyi zuciys ku mutu ya isa haka wato shi yasa dazu kika aiko wannan munafukar tsohuwar dan ta fadi mishi ko to kin yi nasarar gaya mishin amma aure bb fashi." Inji Khadija.
Maganar ko tayi wa Firdausi zafi don kuwa tasan bata da gaskiya kuma bata son wani abu ya faru igiyar aurenta ta kade.
A fusace Alhaji Umaru ya ce "Gaskiya Gwagwo kiyi hakuri amman yanzun nan aka daura auren Rauda da kabiru a masallaci ga goron ma."
Difff filin yayi babu alamar ma da mutum a gurin ko numfashi wani irin sarawa kan Aliyu ya yi yaji wani irin daci a makoshin shi juwa kawai yake gani.
Yayin da Rauda ta fadi kasa tim a sume.
Sai a lokacin Gwagwo ta hau salati tana sanar da ubangiji.
Firdausi ko kabara ta sa ta ji wani sanyin dadi na ratsa ta tundaga jini da jijiyoyin kanta na farin ciki sai hamdala take yi.
"Kayi ta auren ka Umaru dan Wallahi sai ka sake ni na zo kenan bazan koma ba alkawari ne nayi maka kaje ga yar nan taka ce daman ni ma yau na yankewa kaina kadararn auren ka babu ni babu gidan ka."
Wata iriyar zufa ce ts karyo mishi don kuwa yasan kafiya da taurin rai na Khadija daman Gwagwo ke sauko da its to ga abin da ya faru baya jin wannan karon akwai mai ceton shi.
Dana sani ta lulllube shi dan bai hangawa kan shi cewa Auren Aliyu da Rauda kamar shi ne zau raba Iro da Khadija ba sai yanzu.
Hularshi kawai ya cire yana firfita kan shi.
Alhaji. Iro ko cewa yayi su shigar da Rauda mota a kaita asibiti. Ya kalli Aliyu yace muje gida ke kuma Firdausi ki koma inda kika fito. " daga nan yasa kai ya fita.
Hannu Umman tasa a ka ta saki kuka da ihu.

YOU ARE READING
TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.
RomanceLabari ne akan masoya guda biyu wayanda suka taso cikin kaunar junansu saidai iyauen su sun dauki alwashin babu a aure a tsaksninsu. Ga dai jini daya na yawo a jikinsu na zumunci amman wani shudaddan alamari ya yi musu katsnga da samun junansu.