11

49 3 0
                                    

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE!.

KHAIRAT UP.

Vote@wattpadkhairi_muhd.

Karamci writers association.
[karamci shi ne tushen mu'amala tagari].

                         11.

Kama hab'a inna lami tayi dake irin taofaffin nan ne masu shegen fada da tsaurarra abu tuni ta saki wani irin ihu tace "ke yar nan ki saurare ni da kyau ki kuma kalleni ni din nan Lami ni ba sakaryar uwa bace ba wadda bata san ciwon kanta ba saboda haka ki kula ki kuma iya takunki ko ince ki sake sabon taku nan gidan gidan gandu ne gida ne na ko wanne shege da shegiya ki saurarra in kan ki yana hayaki namu tururi yake yi ehe."

Dariya Rauda tayi irin dariyar nan ta rainin hankali da kuma naji ki sai kuma me?.

Haushi ya tike iya lami kowa yasan ciwon dariya baysn kayi kashedi kenan ma bata tsorata ba ta ganta yar karama yarinya sosai a tunaninta in tayi mata barazana zata nutsu ta tsorata sai ta ga akasin haks bata gama tsinkewa da lamarinta ba saida ta ji Rauda na ce mata.

    "Ke tsohuwa in nan gidan gidan shegu ne ni nan Rauda yar halak ce kuma kin san akwai banbanci tsakanin shegantaka da hallaci. Ina so ki sani wannan wasan ba karami bane ba wasa ne me kyau da aji yafi karfin kanki Wallahi saboda haka ina so ki ja tsuman rayuwarki salin-alin ki koma inda kika fito na riga da gaya miki ke ba tsarar yina ce ba sai dai danki wanda kika haifa shi ne daidai ne yo Allah na tuba misali yanzu in sabgar dambatuwa ce in na raruromo ki ai sai dai wata bake ba saboda haka ki kama gabanki."

Iya Lami bata da wani zabi da ya wuce ta juya ta koma inda ta fito dan ta sani in ta taba wannaj yarinyar ta taba tijararran uban ta Umaru ne.

Ajiyar zuciya ta sauke na karfin halin abin da ta aikata wanda bata taba aikatawa ba a rayuwarta.

*

A ranar da Aliyu yaji labarin abin da ya faru ya tattara komai ya bar garin ya koma makaranta da tarin bakin ciki da bacin rai da kuma kukan rabuwa da Raudan shi ya sani yayi rashin abar kaunar shi be sani ba ko zai iya kara soyayya ba amman so daya tak yayi kuma Rauda yayi wa shi tun tashin shi yake son yarinyar be san yaushe ya kamu da son ta ba amma yasan da son ta ya tashi kuma da ita yake kwana yake tashi. Kaddara ta rabashi da abar kaunar shi yanzu shi kenan wannan mutumin ya rigashi sanin Rauda shi kenan shi da Rauda saidai a gaisuwa duk kishin ta da yake yi shi kenan ya tashi a banza? Hawaye suka zubo mishi sannan ya daurawa Umman shi komai shi sa koda zai taho ta bijiro mishi da auren yar yarta Saddiqa ya gaya mata shi ba yanzu ba karatun shi zai cigaba kuma karta yi mishi tilas in ba haka ba bazai dawo nan kusa ba sai ya yi shekaru da dama tukuna zai dawo sannan Umman ta sarara mishi da maganar. Sallamar da suka yi da mahaifinshi tayi mishi dadi kuma ta sanyayya mishi jikinshi sosai sannan kuma yayi hasahen cewa in ya koma zai tarar da Mami a gidansu turkashi k'ak'ak'ak'a k'ak'a akwai matsala domin kuwa gidansu zai koma sansannin yaki da tashin hankali.

Baya manta wani lokaci da abin ya faru shekarun shi goma ya koma gidan kakarshi da zama a hannun Gwaggwo Rabi lokacin shekarar Rauda Biyar ita ma tana gidan ne amma rikonta a gun Gwagwo Fatu ne sanban ma kakaninsu maza na da rai gidansu sun taso cikin so da gata kasancewarsu a lokacin jikoko biyu tal da suke dasu daga yaransu biyu tal. Ya dauka baya son Rauda ne saboda kullum sai ya doketa kuma baya barinta zuwa ko ina da ta fita kofar gida zai korata dan akwai wani dakali a kofar gidan inda shi da abokanshi ke taruwa suna yan harkoninsu na wasa a lokacin da ciyayya. Rauda ta taso a sangarce da kuma son jiki ga tsiwa da farin jini saidai bata raina na gaba da ita. Sun taso cikin k'in junansu da kuma tsanar juna ba tare da sun san cewa so da shakuwa ce ba duk da shi Aliyu yana da sa ido a kan lamuranta in dai kaga kukan Rauda to Aliyu ne tun tana tsoranshi har ta girgije ta daina ta soma rama saboda tana girma tana kara wayo kuma tsiwarta na kara fitowa.

Yana da shekaru goma sha biyu ya koma boarding school. Jss1 kenan.

Inda take da shekaru bakwai tun da ya tafi take jin gidan yana yi mata dadi duk da tana kewarshi amma tafi sakewa yanzu dan kuwa yanzu tana fita kuma tana wasa.

A lokacin da ya kammala sakiandiri ne ya san cewa son Rauda yake yi sai ya zama over possessive a kanta gaba days baya barinta ta je ko nan da can saboda lokacin ya gama makaranta ya dawo kafin ya shiga jami'a, sannan ita kuma komai da ake bukata na yan'matanci ya bayyana a jikinta fara ce sol me siririn hanci bata da jiki sosai kuma baza a kirata siririya ba tana da shape me daukar ido dan tana da hips ga duwai b**bs din ta ma ma sha Allah babu laifi ga gashi ba irin mai damun nan ba amman yana da cika kuma baki sidik dashi takaice dai Rauda da ka ganta kaga bafulatana usul gaba da baya.

Aliyu kuma kalarshi mai duhu ce ba baki ba amma bai kaisu haske ba bakin shi mai kyau ne irin kalar nan da bature yake kira (chocolate colour.) dogo ne me kirar gaint ga miskilanci da tsade gida amman in yaso yana barkwanci mutum ne shi mai cinkisa da son girma sannan in dai yana son abu to fa baya hadashi da komai sannan ga biyayya ga na gaba yana da hazaka da kokari sannan fannin likitanci yake karanta fannin mata (gynecology ) kennan.

Aliyu ya sha fada da samarin garinsu in ya gansu da Rauda ko yaji suna maganarta ko tunkararta yanzu zai ce an mata miji ko kuma in kayi mishi gardama ya more ka yayi ma jina jina ba abu ne mai wuya a gun shi ba. Haka yasa sau da dama yake wuni zur a kofar gidan kakaninshi saboda kar wani yazo gun Rauda ko ita karta fita. Tun Gwagwo na fadan ya takurawa Rauda har ta sa musu ido dan kuwa ta lura akwai wani abu a tsakaninsu kuma abu mai girma dadin dadawa basa ganin laifin junansu yanzun nan zasu tarewa juna fada.

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.Where stories live. Discover now