*TUN RAN GINI TUN RAN ZANE*
Khairat Up.
Vote @wattpadkhairi_muhd.
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to like our page https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsappWattpad-https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube- https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 019.
___________📲
﷽
"Verily patience is the best conduct in the affairs of mankind. Anyone endowed with patience is indeed blessed with the most loved of all gifts".
May Almighty Allah Continue to Bless us with His Love, Mercy, protection and Blessings.
Ameen.
Jumma'at Mufeeda.*.
"Kin tara yara kina koya musu mugun hali ko? To kiyi duk yadda kika ga daidai ne kiyi rayuwa ce ki dai bi a sannu domin idan suka ji abin da kika aikata a shekarun baya ma dan ki auri ubansu kunya zaki ji dan sai sun ji basa sonki saboda haka ki san me kike yi. Ku kuma ban bawa kowa kofar da zai raina min ahali ba balle yar'uwata ba to yanzu matata ce ita kuma Rauda matar wan ku ce saboda haka ku nutsu kar kuyi halin da zaku zo kuna shan kunya ku kasa had'a ido da mutune. Ke kuma Gwagwona zaki yi mamakin idan na ce miki aure zan yi miki dan kar ki lalata min farin cikin gidana."
Kuka Rabi ta saki ta soma bashi hak'uri "kayi hak'uri Abba Wallahi bazan kuma ba ni ban da ma saurayi Abba kayi hak'uri dan Allah ban k'arawa."
"A'a ni ai ina da su sosai yaran da zan iya baki dan ki yi auren in yaso sai ki maida hankali a naki gidan ta yadda gidana zai sami salama ko?."
"A'a Abba tsautsayi ne yanzun ma ya sani tankawa ni babu ruwana Allah Ya baku zaman lafiya kai da Mami."
Murmushi ya yi sannan ya ce "Toh ku tashi ku bani guri zan yi magana da Ummanku."
Cikin k'ank'anin lokaci suka fita daga cikin d'akin suna yan maganganunsu.
"Burinka kullum ka dake ni ka hanani kuka sannan ka bi ni da gorin abin da ya wuce . Wai dan Allah yaya kake so nayi ne ni da rayuwata?, da son ka zan ji ko kuma da kishin Khadija?, ko kuma da ci min fuskar da kake yi ba dare ba rana a gaban mutane?."
"Bana ci miki fuska , kuma bana wulakantaki, kullum so nake yi ki bi hanya daidai madaidaiciya idan kina yin wayanan abubuwan zaki raba kan gidana a matsayinki na uwargida ki ja girman ki dan Allah in kina yin haka daga baya zaki zo kiji kunya dan kin sani ko ba dade ko ba jima sai an tuna baya."
Kuka ta saki tana shashek'a ita dai wannan soyayyar banda wahala da tashin hankali babu abin da ta tsinana mata.
Tausayinta ya kama shi komai tayi dan son shi tayi. Zaunawa yayi a kusa da ita ya dinga lallashinta saida ya ga ta daina kukan tukuna ya fita daga gidan so yake ya kira Aliyu yazo suyi magana da shi.
Yana fita ya ci karo da Aliyu na koka'arin shiga cikin gidan da ga nin shi babu nutsuwa a tattare dashi ko kad'an.
"Aliyu."
"Na'am Abba barka da Safiya."
"Barkanmu yaya hanya ?, yanzu kake tafe?."
"Eh Abba."
"Toh lafiya dai ko? Dan na gan ka baka tare da nutsuwarka ko akwai damuwa ne?."
Ji yayi kamar ya rungume mahaifinshi ya fada mishi damuwarshi amman bazai iya ba sai kawai ya basar ya waske yace "lafiya lou Wallahi Abba kawai nayi kewarku shi yasa na taho in gan ku."
"Ah ! Ka kyauta sosai daman fitowar nan da nayi kai zan kira kazo ina neman ka sai gashi ma kazo da kan ka shiga ciki tukuna ka kimtsa ka huta sai muyi magana. Sannan ka k'arasa ka duba Umman ku bata jin dadi dan k'arin ruwa ma ake yi mata."
"Subahanallahi Abba me yayi zafi haka?."
"Dalilin neman naka ai kenan nasan zata gaya maka in ka shiga ciki bari na je na dawo zan shiga Kano ne."
"To Abba a dawo lafiya ko in zo in yi maka rakiya?."
"Aa nagode ni da su Alhaji Fatahi ne zamu je ganin wasu filaye ne."
"To Allah Ya bada sa'a Abba kuna jinda kud'i kuyi ta tara filaye."
Yana dariya yayi gaba sannan yace "wa ku muke tarawa ai da jikokinmu ba na kanmu bane."
"Allah Ya k'aro arziki da wadata."
"Amin!. Sai na dawo."
"Abba a dawo lafiya."
"Allah Ya Sa."
Ciki ya shige direct d'ak'in Ummansu ya shige ko gaisuwar su Iya Zulai bai amsa ba balle ya bi ta kai ba. D'akinta ya shiga da salamar shi yadda ya ganta saida hankalin shi ya tashi ta yi wata iriyar rama tayi firit kamar babyb roba sai farin.
Amsa mishi tayi idanuwanta sun ciko taf da k'walla ta na jin ta ko ina Dije ta fita tayi mata fintikau ta auri mijinta 'yarta kuma ta auri d'anta.
"Umma!."
"Aliyu na zo kusa dani d'an albarka."
"Umma wane irin ciwo ne wannan ? , tun yaushe kike ciwon aka rasa mai fad'a min?."
"Aliyu kashe ni Abbanku yake son yi kawai wannan ciwon daga jiya zuwa yau dubi yadda na koma Aliyu komai ya lallace min duk na koma ni kad'ai amman na san baza ka watsa min k'asa a idona ba duk abin da na saka ka nasan zaka yi."
"Umma meya faru?."
"Abbanka ya auri Maminku jiya bayan ci min mutunci da suka yi a gidansu bai ishesu ba suka kuma had'a baki suka d'aura auren ka da 'yarta."
Cike da mamaki da al'ajabi ya ce wai wace 'yar yasan dai Rabi karama bata kai minzalin aure ba . Rauda kuma tayi aure to wacce 'yar ce wadda bai sani ba?."
"Umma wacce 'yar?."
"*Rauda*".
Tashi yayi a zabure yayi baya yana ma Umman wani irin kallo. Kafin yace "Umma wace Raudar? Raudan da tayi aure?."
"Hmm! Aliyu ai Rauda ta kaso auren ta kusan kashe musu d'a nan aka biyota da rodona da sanduna ga k'araya a hannu Abbanku ne ma ya ceceta ya raba fad'an ya biyasu mak'udan kud'i suka sako ta shi ne kai aka lik'a maka."
K'anshi ya k'ulle komai ya kwance mishi ya rasa mai zai yi farin ciki ko kuma bak'in cikin abin da ya faru dashi da kuma bak'in cikin ta fara sanin wani bayan shi?. Bai yi wata-wata ba ya juya ya fice da gidan da mugun gudu ko kiran Umman tashi bai ji ba yayi waje.
#*TRGNTRZ.*

YOU ARE READING
TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.
RomanceLabari ne akan masoya guda biyu wayanda suka taso cikin kaunar junansu saidai iyauen su sun dauki alwashin babu a aure a tsaksninsu. Ga dai jini daya na yawo a jikinsu na zumunci amman wani shudaddan alamari ya yi musu katsnga da samun junansu.