39

32 2 0
                                    

*TUN RAN GINI TUN RAN ZANE*

Khairat up.

Vote @wattpadkhairi_muhd.

Karamci Writers Associations.
[Karamci tushen mu'amala tagari]
  Visit to like our page https://www facebook .com/110308337320465?referrer=whatsapp

Wattpad-https://my.w.tt/RXazzMOMY7

Youtube-https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Page

____________📲 40.

"To jeki gani nan zuwa."

Rabiat ta fita daga falon.

Abba ya kalli Mami ganin yadda ta shiga damuwa ya sanyayya mishi jikin shi wani irin tausayinsu yaji ita da Raudat Aliyu ya gama dasu.

"Kar ki damu Maminsu in sha Allah alkhairi ne. Bazan bari a cuci Rauda ba."

Murmushin karfin hali kawai Rauda tayi ta ce mishi "Hmm! Haba Abbansu wane irin magana ce wannan ai babu abin da zaka yi wa Rauda na cuta a duniyar nan ko da bayan raina ne na san wannan balle kuma ina nan ma. Kawai ina tausayawa Aliyu da Rauda ne saboda dazu ma ta zo min tana cikin uwar daki ma duk ta kasa sukuni."

"Ku zo muje dukanmu yau dai ayi ta a gama kirawo ta."

"To shi kenan."

Ya fita ita kuma ta shiga cikin dakinta. Ta tarar da Rauda a zaune idanuwanta biyu a kan cilin din dakin sai hawaye ke bi mata kumatu na kishi da bakin ciki.

"Rauda ki daure ki danne damuwarki na san babu dadi amma ki daure kar ki sake ki nunawa makiyinki gazawarki ko da a fuska ne hakan na fusata shi kinji ? Ki nuna musu ke tattaura ce ki bi bayan mijinki ko a bayan idan shi ne duk wani abu da za ki yi na rayuwa tsakaninki da mijinki ya kasance sai daga ke sai shi ne kar wani ya ga lagonku har ya shiga tsakani ina fata kin fahimce ni?."

Gyada kai kawai Rauda tayi dan kuwa abin da ta fada hakan ne.

"Ki tashi zamu je falon kasa."

*

Aliyu da ke cikin tashin hankali tun bayan kiran da ya yiwa Rauda ta gaggaya mai magana ya kasa sukuni gashi yana ta kiransa amma wayarta a kashe take, ya rasa dalilin fadan nata wani zubin Rauda kamar mai aljanu. Tsaki kuwa ya yi ba adadi. Wayarshi ya zaro ya kira nambar Sadeek.

Sadeek na dakinsu yana kallo a laptop din shi yaga kiran yayyan na shi da sauri ya daga.

"Hello!".

"Hello Sadeek kana gida ne?."

"Eh ina gida Yaya."

"Kai wa Rauda waya."

"Rauda na falon Abba anyi baki."

"Baki?."

"Eh! Wannan yarinyar ce ta dawo da iyayenta yau."

Tuni Aliyu ya gano bakin zaren Keenan Amira ce ta dawo dan ta hada mishi bomb shi yasa Rauda ta gaya mishi maganganu bai ga ta zama ba wannan karon ya kamata ya kawo karshen wannan abin haka yana ji yana gani baza a cuce shi ba Wallahi.

*

Alhaji Ibrahim na shiga falon ya ci karo da fusjar Hajiya wadda sai da gaban shi ya fadi da ganin ta wani irin abu ne ya tsaya mishi a kirjinshi wanda be san sunan da zai kira abin da shi ba. Cikin kamewa da dakiya ya karasa ya zauna amma baza ka iya fadar ainihin abin da yake a fuskar ta shi ba.

"Sannu da zuwa Alhaji."

"Yauwa Firdausi sannu da gida."

"Sannu Alhaji."

"Yauwa Sannu Hajiya sai dai ban gane ki ba."

"Eh! Suna na Hajiya Fauziya ni ce mahaifiyar Amira wadda danka Aliyu ya yi ma ciki kuma ya ki ya saurareta."

Ba Abban kadai ba hatta su Mami da suka shigo a lokacin sai da kalmar tayi musu banbakrakwai babu dadin ji.

"Hajiya kiyi hak'uri wannan yarinya Amira tazo min kwanaki kuma mun yi magana da ita bayanin da nayi mata shi zan kuma yi miki tunda na tuntubi Ali kuma ya fada min tabbas ya santa kuma har wani abu ya shiga tsakaninsu a bisa kuskure da kuma sharrin shaidan sai dai bai yarda da cikin ba domin kuwa sau daya aka samu akasin ya musa da zancen cikin. Ni kuma na yi mata alkawari daman tun da can in ta haihu lafiya sai a gwada jininsu kamsr yadda Aliyu ya bukata ma'ana DNA test in dai dan shi ne zai aureta. Saboda haka muyi hakuri zuwa lokacin da Allah zai sauke ta lafiya mu gani."

"Kenan dan ku da ku kan ku kuna nufin yata Amira bin maza take harda sai an nemo uban dan cikin ta ko me?". Hajiya ta fada a fusace da bacin rai.

"Ba nufi na haka ba Hajiya ina gaya miki abin da yake akwai ne. Ba a yin shari'a ta fuska daya yanzu Aliyu baya nan yana Adamawa sai dai in zaku yi hakuri ku jira shi to. Ni iya abin da na ga zan iya na gaya muku tunda baki gamsu ba shi kenan sai ki jira mai gayya mai aikin."

Umma tayi tsalam ta ce "Yo ko sau daya ne ai za a iya samun ciki kawai yarinya ta haihu ayi musu aure a wuce wurin."

Wani wawan kallo ya jefa mata da sai da bakin ta ya ladaftu bai san wacce iriyar uwa ce Firdausi ba.

In kin yarda za ki jira Aliyu to shi kenan zan sa Sadeek ya kai ku masauki gwanda muyi maganar mu gama tunda ga ki kin zo kema.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce shi kenan zan jira saboda wannan maganar ta rayuwar yata ce.

Shi kenan. Rabi kira Sadeek ya kaisu gidan Gwagwo.

To Abba.

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.Where stories live. Discover now