TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.
Khairat Up.
Vote @wattpadkhairi_muhd.
Karamci writers association.
[karamci tushen mu'amala tagari.]015.
Aliyu kuwa a Zaria bai san abin da ke faruwa ba zan iya cewa ma yayi wani irin sabo da Amira cikin kankanin lokaci bayan lecturers zaka gansu tare suna hira ko a farfajiyar makaranta ko a cafeteria suna cin abinci suna hira sosai suka yi sabo da juna.
Kasan ranshi kuwa na makale da son da yake yiwa Raudat kwanan nan kawai tunanin ta yake yawan yi kuma gida na fado mishi babu halin zuwa saboda bai san ya fadi exams dinshi ta karshe dake yana semister din karshe ne final year yake.
*
Washe gari juma'a duk muna tsakar gida muna hira dasu Gwagwo tana ta bamu abin dariya na kuruciyar su Abban da Mammi . Mamin ma saidai tayi dariya kawai samarin gidan sai hada hadar tafiya masallaci suke yi kowa ya sha kwalliyar juma'a ni kaina raina fes nake jina kuma wasai sai dai kullum ina kewar Yaya Aliyu dan ina son shi so nake in gan shi in yi mishi albishir da cewa babu auren Kabiru a kaina kuma ni tashi ce shi kadai martabata na tare dani har yanzu. Tunanin irin farin cikin da nake ciki kawai ma abin dadi ne.
"Salamu alaikum."
"Amin wa alaikum salam lale...." inji Mami saidai maganar makalewa tayi kasancewar Umma da ta shigo anci sa a ma tayi sallamar.
Harara ta zabgawa Mami sannan ta tsuguna gaban Gwagwo Rabi ta saki kuka babu wanda ya ce tayi shiru ko tayi hakuri har saida ta gaji dan kanta tukuna ta fyace majina da shassheka sannan tace "Gwagwo dan Allah kuna ganin dacewar wannan al'amarin tayaya Aliyu nasan auren Rauda shi ma uban shi na son auren Uwarta ai babu dadin ji ma Wallahi ni dai Gwagwo ki dakatar da Alhaji Iro Wallahi Allah in ya yarda aka yi auren nan Wallahi ni kaina ban san irin abin da zan aikata ba."
"Toh naji ki Firdausi uwar Ibrahimu in an daura auren ki hada yanaki yanaki ki bar masu gidan daman su jininsu guda ne ke yar karo ce ke ni fa Wallahi bari kiji tun abin da kika aikata fa kika fita daga kaina naji na tsaneki dan dai bana son in raba aure ne ko kuma in shiga hurumin ubangiji da tuntuni fa kin san nayi dan Wallahi ba dan alkawarin da nayi wa Baffansu ba da baki haifi yaran nan ba Wallahi da saidai a wani gidan."inji Gwagwo Rabi.
Jikin Umma yayi mugun sanyi ta sani duk gidan babu mai son ta kuma basa kaunarta amma bata son Gwagwon na wulakanta ta a gaban Mami ba.
"Nidai Gwagwon ki taimaka mini ki sa a fasa wannan sabgar dan Allah."
"Aiko saidai in ki mutu Firdausii , "ya fada yana zama kan sallaya tsugunawa yayi ya gyada iyayenshi sannan ya kuma kallon Umma yayi tsaki ya dauko wata leda da ya shigo da ita ya ajiye gaban Gwagwo Fatu sannan ya dauko rafar kudi ya ajiye gaban Mami yana ta sakin far'a ni kaina saida gabana ya fadi da na gan rafar kudi da kuma damin goro da alawa sai naji ina jin tausayin Abbana ina so ma na gan shi na tallafeshi na rarrasheshi nasan irin son da yake yiwa Mami amman kaddara........ tsinke min tunani na suka yi da naji Abban na fadawa su Gwagwon ai yanzun nan aka daura mishi aure da Mami.
Suka sona hamdala suna godewa Allah "Alkawarin Allah Ya cika yau Hemmu Ya zama angon Khadija kai Ma sha Allah. Allah ubangiji Ya baku zaman lafiya Ya hada kanku ya kawo zuria gaskiya naji dadi." Inji Gwagwo Rabi.
Mami kuwa tashi tayi ta koma dakinta tana jin kunya.
Gwagwo Fatu kam adduar ita ma tayi sannan ta zage ta zangada guda mai kyau.
Yayinda naji hawaye sun sauko mini.
Umman kuwa banjin ma tana cikin hayyacinta.
Tashi yayi da zummar fita daga cikin gidan gaba daya fuskar nan tankar gonar auduga tsabar fara'a.
Tashi Umman tayi da gudu kamar zararriya jiki na bari sai waige waige take yi da alamu abin bugu take nima niko da sauri na tashi daga inda nake nayi cikin daki da gudun bala'i ina haki bina da kallo Mami tayi nasan bazata yi magana ba karin bayani dai take nema daga gareni in kuna jin ana miskilanci asalin miskilanci da rashin son magana ka sami Mami na ka gama a rana dai bai fi tayi magana sau goma ba dalilin kenan da yasa na dawo gidan Gwagwon mu dan ina shakkar Mami akwai ta da tsade gida Abban namu ma shakkar ta yake yi balle ni.
"Wallahi Mami Umma ta haukace fa kinga abin da take yi a waje."
Tsaki tayi ta gyara zamanta ta cigaba da abin da take yi.
A waje kuwa cakuma ta kawo mishi tana ihu karya yake bazai yuwu ba bazata yarda ba sam bazata taba yarda ba gwanda ma ka warware wannan banxan auren da kayi dan bazata shiga min gida ba ko kunya bazaka ji ba ka hau uwarta danka ya hau yarta?."
Wani irin wawan mari ya zuba mata jikin shi na rawa dan bacin rai wani irin tsanarta yaji da haushin abin da ta fada wanan ai gidaddanci ne da rashin hankli a kullum ke bazaki dinga fadar alkhairi ba kullum zancen ki na iskanci ne to an daura sai kiyi abin da zaki yi min in gani , bazan sakentsn ban kuma sai na aura wa Aliyu Rauda in yaso daga ranar da muka tare a gidanki ki fadi ki mutu mu kai ki kabari.
Tsugunawa tayi ta saki wani irin kuka mai ban tausayi shi kuma ya fita rai a bace.
Gwagwon ko cewa tayi "Kin dai ji kunya Wallahi."
*
Alhaji Iro daga nan fita yayi direct gidan Alhaji Umaru ya nufa ran nan a hade yayi mishi sallama da kyar ya amsa dan labarin auren shi da Mami ya zo mishi sai kumburi yake yi kamar wani miciji.
"Na sani Iro asiri kayi mini dan ka auri matata kuma gashi kayi nasara amma ka sani sai na yu duk yadda zan yi na rabaka da matata."
Dariya Abba yayi sannan yace "Da zan yi maka asiri da tuntuni nayi maka asirin da bazama ka haihu da Khadija ba. Saboda haka ba wannan ne ya kawo ni ba illa maganar yaranmu ce ta kawo ni ka sani Aliyu na son yar wajan ka Rauda. Ina son ka amince min yau bayan asar a daura musu aure."
Wani irin kallo ya watsa mishi ranshi a dagule yayi wani irin tsaki sannan ya tashi tsaye "Ko Rauda zata mutu bazan bari ta auri Aliyu ba ai dukan sai ya yi min yawa, sai ayi min dariya ka aure min mata danka kuma ya auri yata to sam ban yarda ba bazai yuwu ba Wallahi."
Dariya Abban yayi irin dariysr nasarar nan sannan yace "Umaru kayi hakuri ka yarda da ikon Allah ka kuma gode mishi da ya wadataka da ni'imomi ta ko ina , ka manta da baya mu rungume yanzun mu kasan ni na san abin da baka son kowa ya sani a kan wannan maganar zan iya tona maka asiri kowa yaji abin da ka ke aikatawa duniya ta san cewa Alhaji Umaru wane irin mutum ne shawara ce ka rufawa kan ka asiri ka yarda ayi abin nan in ba haka ba..... ya karkade babbar rigar shi ya tashi zaune zai fita.
Da sauri cikin kidima Alhaji Umaru ya tashi ya ce "Shi kenan na yarda amma ka sani zamu gauraya ne."
Dariya Abban ya yi ta samun nasara sannan yace "Nagode hakan ma. Sai mun hadu a massallaci anjima Allah Ya tabbatar da alkhairin sa Amin."
Wani irin tarniki ne ya turnuke Abban Rauda ta ko ina bashi da mafita ji yayi ya tsani kan shi kuma tsanar da ya yi wa Iro sai ta dada nunkuwa yaji ma duk Umma ce ta ja mishi wannan abin da bai biye mata ba da bai yi sanadin da zai saii khadija ba balle yanzu yazo yana yi mishi barazana kawai sai ya saki wani irin kuka.
*
Ba tare da kowa ya sani a cikin gida ba bayan sallar la'asar aka yi sanarwar daurin auren Aliyu da Rauda bayan sallah aka yi gabatar da daurin auren tare da shedun dubun mutane da kuma amincewar mahaifin Rauda.
Toh fa yanzu zamu fara shiga kanun labarin yaya wannan abu zai kasance?.
Ga dai Aliyu da Amira.
Ga kuma Aliyu da Rauda.
Ga Umma ga Mami.
Ga Abba iro ga Abba Umaru.
A gefe kuma gs kudirin Kabiru.
Ya kuke ganin za ayi. Ku cigaba da bin labarin Tun Ran Gini Tun Ran Zane.Daga taskar........
Khairat up.

YOU ARE READING
TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.
RomanceLabari ne akan masoya guda biyu wayanda suka taso cikin kaunar junansu saidai iyauen su sun dauki alwashin babu a aure a tsaksninsu. Ga dai jini daya na yawo a jikinsu na zumunci amman wani shudaddan alamari ya yi musu katsnga da samun junansu.