12

1.6K 56 2
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

            ✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣ 2️⃣
Sosai Hamad  ke zuba gudu akan titi, har cikin ranshi he is happy for Du'a na barin gidansu datayi, bini bini yake kallonta yanda saibin hanya da komi take da kallo kana gani kasan bata saba fitowa ba, dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take kalle kalle yasa yay dan murmushi yace "iyye basaban ba yau anfito waje" juyoda kanta tayi takalleshi washemai baki tayi tana murmushin nan mai tafiyar da imanin mutum tace "Ya Hamad rabon dana fito waje wlh harna manta nafi shekaru" murmushi yamata yace "this is a chance da Allah yabaki, remember abinda nafada miki duk wanda yadogara ga Allah to Allah ya isar masa, cikin sauki tashi daya Allah yacireki daga kuncin gidan mu, so babu abinda yagagari Allah muddin ki kayi imani, just always thank Allah kinji and be a good girl" gyadamaikai tayi kaman mai tunani tace "Ya Hamad nifa nama manta kamannin Maman Mami fa Grandma, tun ina karama da Mami ta taba zuwa dani ban kara zuwa ba, saidai muyi magana awaya, su Aneela ne suka santa" dan murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace "grandma dinki is one of the nicest person I know in this world, tanada kirki gatada son mutane, duk naje Abuja sainaje na gaidata, you are so lucky to have her as grandmother" shiru Du'a tayi kaman tana tunanin maganan shi saikuma chan ta kalleshi tace "Ya Hamad maisa kai u are different agidan mu? baka biyema su Mum da Ya Nana, kafisu kirki duka" yana kallon hanya still yace "let's say sabida ni namiji ne I see life differently daga yanda mata keganin life, and Abba yabani tarbiyan da nakan iya banbance right from wrong" murmushi tayi takalli kulan kan cinyarta tashiga budewa name ne soyayye da Irish da plantain. "bani nama naci" turo baki tayi tadauko nama daya takai tasamai akan hannunshi dayake bata, murmushi yayi ya wurga abaki yana taunawa yace "wow girkin Mami always taste different" nama daya itama ta dauka tamaida kulan tarufe sanan tahauci tanamai hira kadan kadan harta cinye sai bacci, kallonta yayi ganin yanda take bacci yasa yay murmushi gabgarawa gefen hanya yayi yay parking Sana yadan taso yasaukar mata da kujeran sanan yakoma mazaunin shi yatada motan yana bata wuta.

Wuraren 1 suka kai Abuja, tadata yayi ta hanyar kiran sunanta. "Du'a, Du'a" bude idanunta tayi kadan, hararanta yayi yace "duk uban baccin dakikayi jiya bai isheki ba yarinya saison bacci" tashi tayi yace "gyara kujeran" gyara kujeran tayi yataso sanan takalli hanya yace "kinga yanda Abuja keda kyau kalli titi ba irin na Kanon Kuba" murmushi tayi tace "mun kuwa kaiwa gidan" gyadamata kai yayi yace "takirani yafi sau uku duk kina bacci" shiru tayi tana kallon ko'ina kaman zata hadiye garin da idanunta saiwani irin sanyi da shauki takeji har sukakai wani estate mai suna Presidential Estate. zaro ido tayi tana kara kallon ko'ina ganin gidaje masu suna gidaje ba muna gidaje ba, tasha ji idan su Mum na gulman su tana yawan cewa ai Abba sabida ya rainata yar gidan masu kudi yaje ya auro mata, itama yarinyar kaman mayya itace kawai ta auri talaka mahaifiyarta tabarta ne sabida ita kadaice yarta mace, ita bazata iya tuna gidan dasuke zuwa a dan memory dinta na Grandma sonta lokacin tana yarinya akazo kuma aka dena zuwa da ita saidai su Aneela da Muhammad da Mudasir.

Shiga Estate din yayi yana tafiya ahankali ganin yanda Du'a is enjoying the view din, agaban wani lafiyayyen gida Hamad yay horn, wani security yafito ganin Hamad yasa yace "barka da zuwa yallabai Hajiya ta sanar dani zuwanka" gyadamai mai kai Hamad yayi yana murmushi shikuma yakoma ciki yabude musu Gate din, Jan motar ciki yayi Du'a ta kwalalo idanu tace "nan ne gidan Grandma Ya Hamad" murmushi kawai yamata yana karasa parking motansu acikin jerin motocin dakenan gidan wanda babu mate din seinna su, bude motan yayi yafito sanan yamata alamu data fito gyadamai kai tayi daidai security yagama kulle gate yazo yace "akwai akwati ne Yallabai" "oh yeah" Hamad yafadi yana budemai booth daidai lokacin Du'a takaraso wajen tsayawa chak security yayi yana kallonta ganin haka yasa Hamad yace "ga akwatin" dasauri yajuyo yakalli Hamad hannu yasa yadauki akwatin yawuce Hamad kuma yarufe booth din yajuyo daidai lokacin wata hadaddiyar mata wacce kana ganinta kasan ba yarinya bace dan ta ijiye jikoki tafito, tana sanye da bubun atampa ajikinta gatanan black beauty da akalla zatakai 70.

"oyoyo oyoyo, su maigida an iso" jin muryanta yasa dasauri Hamad yajuya washe baki yayi yace "Hajiya wanan kwalliya haka, bazaki barma yara ba" dakuwa tamai tace "kaci gidanku, yanzu dani dasu idan akaje gasan kyau basai akwasheni sau dari baza'a kwashe suba" karasawa yayi har inda take sanan cikeda girmamawa yadan runtsuna yace "ina yini Hajiya" hannu tasa tashafa kanshi tace "kasha hanya Soja na maigida, jekai wanka kahuta kaida komawa kano sai gobe" tai maganan tana kallon Du'a dake bayan Hamad kanta akasa tana wasa da hijabinta kunya yahanata dago kai. "Du'a" matar takirata ahankali, ahankali Du'a kaman wacce ke tsoro tadago kanta takalli kakanta fess tagane ta danga kamanninta da Mami nan, black beauty abinta yar gayu, ganin takasa magana yasa dasauri tabude mata hannu tace "zonan zoki rungumeni, taho taho" ahankali Du'a taje dasauri tashige jikinta takankameta kankameta Hajiya tayi tace "Alhamdulillah Alhamdulillah, Du'a sannu, sannu kinji, akwai abinda ke miki ciwo"?girgizamai kakan nata kai tayi, dagota Hajiya tayi tasa hannu tai cupping face nata tana kallonta kaman yanda Du'a me kallonta ahankali rasama mezatama yarinyar tayi hakan yasa ta manna mata kiss a goshi sanan takama hannunta tarike tace "muje nakaiki dakinki kiyi wanka"

Ciki tashiga da Du'a falon wani irin hadadden gaske gashinan Duplex sai yan aiki guda biyu dataga suna gyara dinning suna ganin Du'a duk suka bitada kallo suna gaidata. "welcome Du'a" murmushi Hajiya tayi tace "kingan su suke tayani aikace aikacen gida, wanan sunanta Shema'u, dayan kuma sunanta Razika, duk sun sanki, jeki musu sallama" gabansu taje ahankali sai kallonta suke kaman basu taba ganin mutum ba, hannu tamika musu cikin muryanta mai dadi tace "Assalamu Alaykum, nice to meet you" dasauri suka karbi hannunta suna murmushi Razika tace "you are so beautiful" tsayawa tayi turus tana kallonsu Hajiya dake kallonsu tace "tell them thank u sunce kinada kyau" ahankali tace "thank u" sakinta sukayi itakuma Hajiya tasauke ijiyan zuciya sanan tace "taho mutafi" dasauri tajuyo kaman jira take dama stairs sukayi sukai sama saitaga ashema kasan baida kyau wani daki tabude dakin mai kyau sosai saiga hoton ta datana yarinya tana rarrafe kusada Hajiyan dasauri tashiga dakin tana kallon hoton, murmushi Hajiya tayi tace "lokacin kina yar tatsitsiya keda Mamanki kunzl ganin gida, little Du'a, jeki yi wanka kizo kici abinci zan baki labarin anjima" gyadamata kai tayi sanan tacire hijabi ahankali tawuce zuwa kofan datagani wanda ta tabbata bathroom ne saida tashiga sanan Hajiya tafita daga dakin.

Saida tayi wanka sanan tafito daure da towel, akwatin ta dataga anshigo dashi tabude tadauki wata doguwan riga wanda yawanci kayanta dogayen riguna ne daidaikune riga da skirt, saka rigan tayi sky blue ce mai kyau sanan tasaka hijabi salla tayi sanan tazauna tana tunanin maganan Hajiya datace tasauko, tashi tayi ahankali tacire hijabinta ta ijiye  sanan tabude kofa tafito, ahankali take sauka daga stairs tana karabin gidan da kallo, daga sama sama takejin maganan Hajiya da Hamad saikuma takarasa suna ganinta sukai shiru. "kin idar tahonan" tauna mata kusada ita akan dinning hakan yasa ta taho zama tayi wajen Hajiya tace "debi abincin ki kici" dasauri Hamad yace "kafin namanta banfada mikiba kuran nama tazo gidan nan ba" turo baki tayi Hajiya ta harareshi tace "karkaga kana maigida kanemi samin jika kuka sama zamu hau nidakai, ci abinci ki kinji kome kikeso" gyadama Hajiya kai tayi sanan tadebi rice da stew da plantain da fish tanaci, bini bini Hajiya ke kallonta hartaci rabin abincin sanan tasha ruwa haka

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now