29

1.7K 50 0
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

        ✍️ M SHAKUR
free page
EPISODE 2️⃣ 9️⃣
Parking driver yayi awajen parking motoci yana kallonta ta glass haryau yakasa daina mamakin inda Hajiya tasamo kyakkyawan yarinya haka a jika, yasan Zainab(Mami) baka ce to kodai mijinta irin fararen yan shuwa arab dinnan ne, bude kofa tayi ahankali tafito sanan tajuya tadauki wayanta da jakanta screen din wayan dayay haske ta kalla ganin 15mins after 9 nasafe yasa taji jikinta nadan rawa dan bata taba latti ba kuma batasan ko boss din nada kirki ba karya mata fada, maida kofan tayi ahankali tarufe tace "thank you Uncle" dan haka take kiranshi sanan tajuya tafara tafiya zuwa entrance sanan tashiga ciki, Sharif tagani tsaye gaban kantan reception yana sanye cikin cooperate kaya ba suit ba amman wando da riga yay tucking ga belt dayasa mai kyau yana duba Rolex din dake daure a wrist dinshi kaman akwai abinda yake jira, kaman yaji ajikinshi kallonshi ake yasa yadago kanshi yakalli entrance hada idanu sukayi ajiyan zuciya yasauki sanan yasakin mata wani irin cute smile yana dumfaro ta, saida yakai gabanta ya tsaya ahankali yace "you look ahhhhh mema zance"? Yay dan shiru yana kallon sama yadaura yatsanshi daya kan kumatunshi kaman mai tunani saikuma yakalleta ganin yanda take kallonshi irin ta kosa taji mezaice dinan yasa cikeda tsokana da wasa yace "you look like indon kauye" gabaki dayan murmushin datakeyi bacewa yayi tai raurau da idanu kaman zata fashemai da kuka hakan yasa yay dan dariya yace "just teasing you" saikuma ya tsareta da idanunshi da for the first time tunda tasanshi suke shiri sosai tana kallonshi kaman yayanta taji wani iri hakan yasa tadauke kanta, murya chan kasa yace "you look damn cute Du'a kaman in saceki in gudu" murmushi tadanyi kanta akasa dan tasanshi da wasa still tana wasada yatsunta, for a moment yamanta inda suke tsaye all yake gani wasa her tsaye agabanshi, ahankali yadan waiga yabi wajen da kallo sanan yajuyo yakalleta yace "I've been calling you baki dauka maisa" dago kanta tayi takalleshi ita bamatasan tayaya yasami number taba, saikuma tanunamai wayannata dake hannunta  tace "anan ka kirani"? Wayan ya kalla yace "yes, I gave u about 3 to 4 calls I think" wayan tajujjuya takalla dan ko kadan bataji ringing ba ahankali tace "banji ringing ba" hannunshi yamika mata yace "let's see maybe kintaba wani waje ne" bashi wayan tayi yakarba yabude ganin ba key saikuma ya kalleta yace "bari zan miki setting nashi anjima wayan nason update, yanzu dai our Boss yazo he's in his office, maisa kikai latti, our Boss is such a wired dude fa" yay maganan kaman mai whispering din gulma da hakan ma yasa tai murmushi, tsayawa yayi yana kallonta yace "instead of kifara tsoro kinyi latti murmushi kike ko zaiyi deducting a salary ki sanan yau saikin biya bashi time din dakikaci by adding extra hours kan lokacin tashinki, oya let's get going" yay maganan yana tafiya tana biyedashi abaya yace "zai miki tambaya, so yanzu idan kinje as normal yanda any boss zaiyi he will ask u few questions ma sababbin staff nashi, yadan miki tambaya karkiji tsoro be very bold and answer him kinji" gyadamaikai tayi suna hawa stairs, yace "and idan yace maisa kikai latti me zakice? Uhmmm kuma banaso nakoya miki karya"? yay maganan yana tunani yadaura yatsanshi akai yana tafiya, dasauri tana kallonshi itama tana tafiya tace "zance mai nakone akafa" kwalalo idanu yayi ya tsaya yana kallonta, gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya tace "wlh dazu nadebo ruwan tea shine yazube akafana yay zafi sosai saisa nai latti" tunda take maganan yake kallonta saida tagama ahankali calmly yace "kinyi kuka"? Gyadamai kai tayi da zuciya daya tana raurau da idanu tana tafiya, chak yatsaya heart dinshi nawani irin racing he feels kaman yajawota ya rungumeta ya lallasheta, jin shiru yasa tawaigo ganinshi abayanta yasa tadan zaro ido tace "menene, ka manta dawani abu ne" dan murmushi yayi yataho da saurinshi yace "no, how's the leg now? Yadena zafi?" gyadamai kai tayi tace " yadena" daidai nan sukakai 5th floor, tsayawa yayi daganan yace "our Boss is a bit harsh but don't get scared okay" gyadamai kai tayi tanadan zaro manyan idanunta, dan yatsine fuska yayi yace "naaaay! I don't like that face, now smile and go you got this" 👍 yamata thumbs up da hannu dayasa tai murmushi sanan tawuce tafara tafiya mutanen dake wajen sai kallonta suke, gaban office dinshi da aka rubuta CEO taje ta tsaya, ga secretary dinshi awajen zaune gaban table tana aiki, ganin ta tsaya yasa tace "you can go in Mrs Du'a" gyadamata kai tayi batare datai magana ba sanan ahankali tadaura hannunta kan handle na kofan harwani kalan sanyi takeji sanan gently tabude kofan kanta akasa, wani irin kamshi da sanyi ne suka wani daki fuskanta dayasa tadan lumshe ido kadan sanan tabude idon kafin ahankali tasa kafanta tashigo sanan tamaida kofan tarufe ta jingina da kofan kanta akasa still hannunta duka biyun kan hannun handbag dinta data kankame gam gam tanajin wani irin sanyi tundaga kafanta har tsakiyan kanta dan sanyin office din yabaci kaman ankure AC gabaki, takai kusan 1min tsaye awurin tana kankame da igiyan handbag dinta kaman her whole life depend on it sanan ta daure still kanta akasa kaman wata munafuka tashigo har zuwa gaban hadadden table din office din ta tsaya gaban kujeran guest tana kara kankame hannun jakan tama rasa takamaimen mezatace a office din mai kamfanin nan, tunawa da maganan Sharif na kartaji tsoron yasa tahadiye tsoron ahankali tabude bakinta cikin muryanta data kara wani irin kankancewa sabida yanda ke faduwa tace "good morning Sir" takai kusan 30sec dagaidashi jin shiru yasa gently kaman wacce idanunta ke shirin fitowa sabida tsabagen rawan dasukeyi tadago kanta takalli kujeran zaman mai office, ido hudu sukayi da Asad dake zaune yana yasanya wani hadadden Italian suit white da blue, wanda keda wani monkey jacket da farin riga ke kasanshi, babu jacket ajikinshi ya rataya kan maratayan da ake ijiyewa a office dan hanging kaya monkey jacket da farin riganne kawai ajikinshi yana zaune kan kujeranshi hannunshi rikeda wasu papers dayake reviewing ga coffee agabanshi yana sipping, sai dayan hannunshi rikeda byro ko kallonta baiyiba, wani irin rawa jikinta yafara ganin Asad mutumin daya cirota daga rijiya a kano, mutumin  data gani a TV, mutumin datagani a hotel hall, same mutumin  da dazun nan taganshi agidansu shine kuma still take gani anan shine mai kampanin nan, the CEO boss dinta to kodai aljani ne, jitayi cikinta yawani irin murda kawai taji wani fitsari yataso mata yacika mata mara yana shirin  zubowa duka acikin yan sakannin data dago kanta ta kalleshi, daurewa tayi ta harde kafafunta gam but still jikinta rawa yake takara kankame jikinta, saida yagama reviewing document din hannunshi yay signing tsaf sanan ya yunkuro ya ijiye papers din kan table sanan ya gyara zama da kyau ahankali yadago kanshi yazuba mata mayun idanunshi akanta, dawani irin sauri tadauke kanta tana kallon gefe tana kara harde kafanta sabida wani irin fitsari datakeji dake neman fin karfinta, cikin muryan nan nashi dababu alamun wasa cikinshi yace "kinyi latti awa daya da minti biyar da sakan lalatin, bayan kinzo aiki latti  kika tsaya kina chatting da wani ma'aikaci anan did you know the gravity of laifin nan"? gizgiza mai kai tayi still kanta na kallon gefe, tsawa yadaka mata yace "nobody answers me with motion speak up" wanan karan batasan lokacin data saki hannayenta dake kan jakaba takai tadaura Ata wajajen abdomen dinta dan tana neman sakin fitsarin sosai, lips dinta narawa sosai tace "I am sorry sir......." yana kallonta still yace "well your salary will tell u if I accept the sorry or not, have a sit" gyadamai kai tayi saikuma da sauri tace "okay" kafin ahankali tasa hannunta taja kujeran gaban table din tazauna jikinta na bari.

Anatse yace "look up and introduce yourself" yay maganan bayabo ba fallasa as usual, gently tadago idanunta tadaura akanshi kaman yanda shima yake kallonta,  kasa jure kalan idanun dayake dashi tayi hakan yasa tana kallonshi ne amman tadan karkata kwayan idanunta gefe sanan ahankali tace "My name is Du'a, I am 21yrs old, an haifeni a kano, Babana nada mata biyu awajen Mama na I am the first child, nayi school from nursery zuwa JSS 2 a makarantan Royal, that's were I stopped a school".

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now