27

1.8K 52 1
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

           ✍️M SHAKUR

Free page
chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461
EPISODE 2️⃣7️⃣
Fadawa kan gadon yayi batare dayacire daidai da takalmin kafanshi ba balle kuma ayi maganan kaya, sosai kanshi kewani irin sarawa, he's so tired and everything and anything, he's working damn hard to keep his whole family happy, shi baida matsala idan da Dad zai natsu yace aure zai kara yasan Ammin shi she won't object to that dan tasan yafi mata alkhairi, but wanan wulakanta Ammi dayake yi yafi komai bakantamai rai, shi bawai yasaketa ba kotamai wani laifi ba amman saiya kauracemata dasu yaranshi for months kuma bawai yaje anywhere bane yana nan Abuja tareda matan banzan shi, yasan once Zinariya takarbi komi dazai bata gobe ta tafi zai dawo gida he hopes from there shi And Ammi can work something together, wani zubin he understands his Dad in the sense that auren hadi aka mai da Ammi but that doesn't zama excuse nashi dazaije yana Zina up and down, Ammi is very very sick low BP takeda shi ita ba high BP ba, and low BP yafi dangerous da high BP mutum can yanke jiki yafadi at any time yamutu, akanme Dad zai dinga wulakanta Ammi eh yamaida ita kaman trash his mother is very sick dudda bata nunawa, but yaga tanashan drugs aboye, gashi sai ramewa takeyi, she's depress dan yasan Ammin shi nason Dad sosai kodaga yanda take luradashi ma zakasan hakan he just wish yanada power to change things arayuwanshi, he wish ana iya chanza mahaifi, hannunshi yakai ahankali ya share wani dan gajeren hawayen daya zubomai ta gefen ido sanan ahankali ya fuzar da iska waje mai zafi, ko minti biyu baikaraba bacci yay awon gaba dashi mai nauyi gaske yana sauke ijiyan zuciya daman ance behind every thought face akwai thousands of weakness aciki.

Wuraren 5:30 nasafe Grandma tabude kofan dakinta tafito, hanyar dakin da Asad keciki tayi, ahankali tasa hannu tabude kofar tashiga yana bacci har lokacin baitashi ba ga takalmi nan baicireba kayama haka, maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna abakin gadon, ahankali takai hannunta taciremai takalman ta ijiye sanan tajuyo da kanta takalli fuskanshi tana kallonshi, harga Allah tana bala'in son Asad samada kowani d'a agidan nan, why because Asad might look harsh kana ganinshi zakaga bakin halinshi but he's weaker than any other person agidan nan dan abu yafi damunshi kan kowa, gashi da zuciyan nema dudda Asad baitaba nunawa ba ita tariga tasan yasan komi gameda halin Baban shi saisa yana gama school yanemi jari daga CBN batare daya karbi kudin Babanshi ba yabude kampanin kanshi cikin ikon Allah kuma kampanin sai albarka yake, yay wayon nanne sabida duk ranan da mahaifinsu zai juyamusu baya he will be able to take care of his family, bambamcin shi da Sharif kenan, Sharif is very nice but Asad yafishi hankali da hangen nesa dudda  idan angansu kowa will go for Sharif dan physically yafi kirki and more welcoming, Asad is just a small boy daya Goya responsibility alot abayanshi saisa yake bata tausayi, she just wish zai natsu ya nemi mata ya aura koyasami natsuwa amman tsoron yanemi mace ma yake sabida baiso yagaji irin halin mahaifinshi beside ance blood is thinker than water, saisa gashinan ne kawai bakowa ke ganeshi ba. Hannunta takai ahankali tashafa tattausan sajenshi tace "kai tashi kayi salla" da kyar yabude ido, ahankali yace "okay Grandma " tashi tayi tawuce tafita daga dakin, dakin Du'a ta shiga tabitada kallo yanda take baccin ta hankali kwance, karasawa tayi gaban gadon zama tayi tashafa fuskanta ahankali tace "yammatana atashi daga bacci, Du'a Du'a" da kyar Du'a  tabude idanunta takalli Grandma cikeda bacci a ido batare datai magana ba, kumatunta Grandma taja tace "da ace yanda kikeson bacci haka kikeson cin abinci danaji dadi saisa kullum cikinki kaman ana diba ayi biyan bashi dashi tsabagen yanda yake ashafe kaman cikin jinjiri" dan murmushi tayi saikuma ta jinkirto tadaura kanta akan cinyan ta takama hannun Grandma dake kan fuskanta ta rungume ajikinta sosai ahankali tace "Grandma agidan ki kadai nasami farin ciki haka tunda aka haifeni, Grandma please karki bari Abba yakomar dani gidanshi I am so happy anan da I don't wanna leave, da kullum sainai kuka Ya Hamad kadai ke lallaahina da Aneela" fadada murmushin dake kan fuskanta Grandma tayi tana kallonta tace "bazaki komaba ai nagayamiki sai inda karfina yakare babu wanda zai kara wahalar min dake, yanzu addu'a na shine Allah yakawo miki miji nagari" murmushi tayi sosai saikuma ta tashi tazauna takalli Grandma tace "Grandma nina isa aure ne? Ya Nana da Ya Hawwa fa duk basuyi aure ba, kumama ai sai mutum ya iya girki akemai aure ko nikuma ban gama iyawaba tayaya zanyi aure to"? sosai Grandma ke kallonta yanda take maganan saida tagama maganan sanan taja hancinta tace "har wayauma baki gamayiba dan Aneela zata iya sayarda ke agaban idanunki baki saniba, tashi kiyi salla ki shirya yau akwai office" gyadama Grandma kai tayi tana tashi ta sauka daga kan gadontai hanyar bayi kananun kalaban da aka mata sun zubo har waist dinta suna lilo kaman wata balarabiya  tabude kofa tashiga bayi, ajiyan zuciya Grandma databita da kallo ta sauke sanan ta tashi ahankali tafice daga dakin.

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now