23

1.8K 56 5
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

                 ✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 2️⃣3️⃣
Lumshe ido kawai tayi looking so somehow da bazaka tabace ga asalin yanayin datake ciki ba, ahaka bacci yay awon gaba da ita saida Hajiya tashigo ne ta tadata taje tai salla sanan ta sata agaba aka kawo mata wani abincin aka tafi danada dan bataci ba sanan tabarta ta kwanta dan akwai baccin sosai a idanunta.
******

Ahaka tai good five days a company from Monday to Friday Sharif has always been there for her, yanada kirki mara misultuwa, he's very nice and generous kaman ba boss dinta ba at all, yamaida ta kaman wata sister dinshi hakan yasa itama tadaukeshi kaman wanta Ya Hamad, itadasu Rahima kuma kaman sunsan juna tuni suka koya mata watsapp suka sakata group dinsu na yammata inda ake hiran samari da heart break ita saidai ta karanta taita mamaki, kullum 4 nayi take fitowa driver Hajiya ya dauketa tana dawowa gida zata gudu dakinta tasaka channels television news but kodaa yaushe ending din program din Asad take samu wani zubinma bata samin takalla kafin takai gida an gama barin ma ranakun da holdup yakamasu, har kasan ranta she wish zata iya ganinshi tace mai thank u for saving life dinta dan ko kadan takasa manta da fuskanshi da idanunshi dasune tagani da kyau danhar kasan zuciyanta takasa mantasu.

Yau Saturday su Rahima sunso sujata yawo Grandma tahanasu dan malamin ta zaizo, wuraren 10 malamin bayerabe  yazo, Hijab tasaka har kasa tafito karatu yamata both na boko da islamiyya dan irin genius ustazan malaman nanne, karfe one suka gama yatafi, dakinta takoma ta kwanta yau kawai she's so happy koba komi tana gida zata kalli program dinan daga farko har karshe yau, salla ta tashi tayi jin ankira sanan takoma ta kwanta sai bacci, wuraren 3 Hajiya tashigo dakin tadata tayi. "ke Du'a oya tashi" bude ido tayi ahankali ganin Hajiya yasa ashagwabe ta daura kanta kan cinyarta murya chan kasa tace "Grandmaaa nagaji" smooth kumatunta Hajiya tashafa tai murmushi tace "oya tashi sonake ki shiga kitchen tareda su Razika kema kisoma iya girki, tuwon shinkafa zakuyi da miyan taushe sai farfesun kifi" ahankali tabude idanunta dahar sunyi dan ja sabida  baccin datayi takalleta, tashi tayi zaune sanan tamike tsaye tace "grandma dakaina zanyi girkin ni kawai su nunamin yanda zan dinga yi" gyadamata kai Hajiya tayi tana murmushi tace "to gimbiya Du'a hakan za'ayi" wani kalan murmushi tayi cikeda murna tawuce tafita daga dakin dan tafi kowa so ta iya girki dan girki na burgeta, shiga kitchen sukayi aiko su Razika sun sha dariya dan targen tuwo bata iyaba haka suka dinga koyanata suna dariya gabaki daya ta manta da abinda takeso tayi, saida suka gama tuwon sanan ta kalli agogo dake manne abandon kitchen din, dawani irin gudu tafita daga dakin ta sama dakinta tashiga, TV kawai ta kunna dan decoder a kunne yake dama tana kan channels din, ganin angama program din yasa taji wani abu yatokare mata wuya, wata matace ta bayyana agaban TV tace "to jama'a ni karan kaina bakin cikin sanar daku nake cewa a yau ne wanan program din da gwamnatin Nigeria takawo muku sabida tallafawa Matasan kasa wanda wanan shahararen matashin  nan dan kasuwan nan wato business  Mr Asad Abdullahi Kitse ya gabatar muku yazo karshe, ku saurara kuji" matan tayi murmushi tace "channels television news tasami sakonni da dama kan shafukansu na sada zumunta da emails kan Mr Asad cewa mutane naso sugana dashi, toga wata sanarwa, gwamnatin Nigeria tashirya kyakkyawan liyafa wato dinner nagama wanan program din agobe karfe 4 na rana inda star dinku Mr Asad zai hallata, ana gayyatan marasa su fito duk kuzo dan Mr Asad zai sake bayarda jawabi wato speech awajen dazai taimakawa marasa wajen fara tasu sana'ar, za'ayi wanan taro ne ababban hall din transcop hotel, a huta lpy" daidai nan suka shiga talla kuma, zama tayi ahankali kan gado tai shiru, kwala mata kiran da akayi yasa ta tashi tafita daga dakin da sauri suka daura miya, suna gamawa ta debi nata tafito ta tafi dakin Grandma dinta dake waya hakan yasa tai zamanta tanacin tuwon. Gama wayan Hajiya tayi tace "iyye manyan mata anyi mana girki yau" washe baki tayi tace "grandma abincin nan dadi wlh sosai" hararanta Hajiya tayi tace "nidai tashi kikai plate dinan kitchen ki wuce kije kiyi wanka, haka akeso mace tadinga yi idan tagama aikace aikacen gida ko girki, wuce daganan sai kiyi salla" tashi tayi tadau kwanon tafito saida taje ta ijiye a kitchen sanan takoma dakin ta wanka tayi tanajin dan ciwo ciwon ciki kaman MP dinta zaizo, fitowa tayi ta tsaya gaban madubi ta kalli kanta tawani kara haske fatar jikinta na kyalli sabida man da Hajiya tasaimata mai bala'in kyau ne, tamadanyi kiba, wanan kumburin kukan da idanunta keyi a gidansu duk babu yanzu, gama shafa man tayi batabi takan kalaban kanta dake lilo ba dan batai parking nasu ba tawuce wardrobe dinta wani dogon riga tadauka na kanti mai kyau pitch color ne tasaka kawai ajiki batare datasaka bra ba sanan tasa hijabi tai salla, tana zaune kan dadduma tana biya karatun da aka mata aka kira isha'i tashi tayi tayi sanan tamike tsaye cire hijabin tayi ta ijiye  kan kujera tadauki wayanta dake gaban madubi tawuce tafito, kasa ta sauka, ganin babu kowa a falo yasa tawuce dakin su Razika dake nan akasa, zaune suke su biyun suna assignment dinsu dan malamin su yabasu assignment, suna ganinta duk suna dagokai suna kallonta, murmushi tayi tace "kuma anbaku assignment" dukansu gyadamata kai sukayi, fadawa kan gadonsu tayi tace "to kugama bari nai chatting dasu Aneesa" saida suka gama sanan Razika tarufe book din ta ijiye tana kallon gashinta tace "yaushe zaki kwance kannan gashinan harya soma kwance kanshi sabida gashibki nada santsi" yatsine fuska tayi tace "ni bazan kara zuwa saloon dinan ba suncika kallon mutane wlh" dariya daga Razika har Shemau sukayi dan yanda tai maganan zaka dauka yarinyar ce harda dan turo baki She looks so cute, matsowa gaban gadon Shemau tayi tace "ai sabida kinada kyau ne saisa ake kallonki Du'a mu ana kallonmu ne Razika"? Girgizakai Razika tayi alamun a'a, yatsine fuska Du'a tayi tace "wlh ko bansan kyan nan, uhm, bari naje na kwanta" tai maganan tana tashi daga kan gadon tamike tsaye, hannunta tasa tadauki wayanta sanan ta musu murmushi ganin yanda suke kallonta tace "saida safe" "Allah tashemu lpy, Du'a gobe kezaki break" bude kofan tayi tajuyo cikeda murna tace "dagaske?" gyadamata kai Razika tayi tace " eh" fita tayi tana murna, Shemau ta kalli Razika tace "Razika daman haka takeda nono ni wlh nadauka breziya ce ke sa nononta yay girma a riga irin push up dinan sai yanzu naganta da ba breziya ajikinta" tashi Razika tayi tana gyara gadonta tace "haka takeda su harda bombom ma kaman ita tai kanta, wlh inason yarinyar sosai Shemau mugun burgeni take, dan she's so simple, batada wani ji da kanta sabida tanada kyau kaman yanda masu kyau keyi dinan kiga suna daddaukema mutane kai sabida sunga sunada kyau, Du'a ga kyau ga kamun kai ga natsuwa bakiga ko saurayi batada shi ba" Gyadamata kai Shemau tayi cikeda  gamsuwa tace "hakane, Allah yabata miji kyakkyawa irinta, ni wlh daurewa kawai nake dabana tsareta da idanu dan wlh bangajiya da kallonta" murmushi Razika tayi tace "bacci nakeji".

Fitowa daga dakin Du'a tayi tana murmushi tana tattaba wayanta dan Aneesa ce kebata dariya tana kawomata karan Mariya waita sace mata zobenta, typing yakuri tayi sanan ta ijiye wayan kan dinning tawuce tana tafiyan nan ahankali takarasa gaban fridge din dake dinning din tabude dan kishi takeji sosai, wani karamin bottle water mai sanyi taciro tana kallon goran, maida kofan fridge din tayi tarufe kafin ahankali tashiga bude marfin goran sanan takafa ahankali abaki tawani lumshe ido tanasha.

"you know cold water is not good for the body" kaman daga sama taji murya kaman na Sharif akanta, dawani irin sauri tabude idanunta tareda juyowa, yana zaune kan dogon kujera shi kadai a falon yana sanye da 3quater na sojoji da farin t-shirt yana rike da system dake kan cinyanshi, dudda taga ba kallonta yakeba amman saida taji wani irin kunya dasauri ta ijiye ruwan sunnar da kanta kasa tayi amugun kunyace tace "Ya Sharif ina yini" batare daya kalleta ba still yana aikin dayakeyi ne yace "hope u good" gyadamai kai tayi ahankali tama rasa mezata ce tace "uhmm kaga Grandma dina? Tana sama bari nakira maka ita" tai maganan tana fitowa daga dinning tai stairs dasaurinta harda dan gudun ta, wani irin turgudewa tayi kafanta ya lankwashe dayasa tasaki wani irin wawan ihu. "wayyo Allah na kafata" tashi Sharif yayi daga kan kujera dasauri yawaigo daidai lokacin Grandma datagama wayan datakeyi tafito kenan taji ihun ta tazo stairs din dagudu tace "subhanallahi maiya faru? Muga kafan" Hajiya tafadi dasauri tana karban kafan da Du'a takasa ijiyewa kasa tsabagen azaba tana dan kuka mara sauti dan yamugun mata zafi, cikeda tausayinta Hajiya tace "sannu ijiye kafan nagani" gyadamata kai tayi tana kokarin ajiye kafan akasa wani irin ihu tayi saikuma tafashe da kuka sosai wanan karan mai kara tace "dazafi Grandma" cikin dan fushi Hajiya tace " kinsan wajen nan bene ne akan wani dalili zaki dinga gudu akai eh" cikin kuka sosai tana kokarin kama hannun Hajiya dake liliyamata kafan tace "zan kiraki ne naga Yaya Sharif yazo" cikin fada Hajiya tace "Sharif da tuntuni muke tare muna hiranmu har tuwo yaci, sama nazo nayi waya, koma bansan yazo ba gidan nan ba Bakin Sharif bane har sama zai iya zuwa wajena, Sharif zo dan Allah kadubamin kafarta kotasami targade ne, kosu Razika basu kadai ba duk wanda zaizo gidan nan hanashi gudu nake akan bene dan hatsari ne da bene yanzu jibi", karasowa wajen Sharif yayi dawani irin sauri takai hannunta ta share hawayen daya bata fuskanta, Hajiya data matsa gefe tace "au uban kukan dayagamaji kinayi dan yazo nanne zaki wani goge hawaye" turo baki tayi ta dauke kai, Hajiya tace "kaji Sharif dubamin kafan kagani" ahankali yakai yatsunshi biyu yadaura kan kafar datai ja sabida turgudewan yanabin dogayen feet dinta da kallo yace "does it hurt" yadan dagakai yana kallon fuskanta, hadiye zafin tayi tagirgiza mai kai alamun a'a hakan yasa Hajiya tace "kafan dakika gamawa kuka ne kike cewa baya zafi"? Murmushi yadanyi yace "buguwace kawai tashafa man zafi zai daina mata zafi" yay maganan yana sauka kasa abinshi, hararanta Hajiya tayi tace "wuce kije kishafa robb akai Allah kika karamin gudu agidan nan saina saba miki Du'a, kidena guje guje kinji" gyadamata kai tayi ashagwabe tace "tom" "wuce kitafi dakin ki, wani aiki Sharif ketayani yi" gyadamata kai tayi tawuce ta tafi tana tafiya ahankali Hajiya tabita da kallo saida taga tabude daki tashiga sanan tasauko tace "Allah kyauta" karasowa tayi tazauna kusada Sharif tace "wai shi gogan bazaizo yagaidani bane" dariya Sharif yayi yana abinda yakeyi yace "finally kinyi admitting kinyi kewan Asad" hannu tadaga kaman zata dakeshi ya kyalkyace da dariya yace "wlh aiki sosai ne aikin nan dayakeyi shi kanshi yagaji kinsan Asad ya tsani takura shida yasaba saidai yatakurama mutane shi baiso atakuramai Allah Allah yake gobe tayi yagama, da sassafe fa yake fita kullum" murmushi Hajiya tayi tace "Allah sarki Asad, kana ganinshi haka akwai kwazo da zuciya" murmushi Sharif yayi yace "nidai idan yazo kicemai wlh yafito da mata yay aure inba hakaba dudda ina kanninshi aure abuna ni zanyi na barshi" yay maganan yana batarai, wani irin baki Hajiya tasaki tana kallonshi tace "ohhh jama'a yauni naga takaina, kaiwai mara kunyan inane Sharif, yoo dan kaniyan kama duka duka da wata nawa ya girmeka wata uku ne fa tsakaninku haka Amminku tagayamini, Asad nada wata uku aduniya aka haifoka" dan dariya Sharif yayi yaturo baki cikeda rashin kunya yace "nidai gaskiya nafadi muku aiko Ammi nagayamata ni wlh aure nakeso kuma shi Asad banga alamun ya shirya aure ba Hajiya wlh yaron nan kaman aljani shi yama tsani mata, basa gabanshi the only matan dayakema murmushi yayi hira yay wasa dasu aduka fadin duniyan nan guda biyu ne daga ke sai Ammi, kinsan ko Anty Turai kanwar Abban mu bayama murmushi cewa ma yake he hates her, to ina zan tsaya jiran irin wanan saiyay aure zanyi ai namutu tuzuru hakanan Hajiya wlh a'a" wanan karan hannu Hajiya takai ta dakamai duka abaya dayasa yakusan sakin laptop din yace "aashhh" dauke laptop din tayi tace " naga alama kwana biyu ban jibgeka ba saisa bakada kunya, mugama aikin dakakemin Allah sa ba shirme kakeba dan naga hankalinka baikai" tai maganan tana saka glasses a idanunta tana kanne idanu danta karanta report din daya rubuta mata, karban system din yayi yace "ni dai tsaya na karanta miki natafi gida nai waya da budurwa ta kuma saina gayamata kece duk kika cinye mata time" dariya tayi tace "kagaya mata hala tamadan soka sabida yanda ba'acin kudinka at least ni Kakar ka ina moreka" dariya yayi sosai sanan ya shiga karantamata.....
wa.me/+2347012181461

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now