24

1.7K 49 6
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

             ✍️ M SHAKUR

Free Page
EPISODE 2️⃣4️⃣
yauma kaman kullum suka tashi suna breakfast malamin su yazo ta tafi wajen nata su Razika ma haka, as usual by 1 yatafi, daki takoma ta kunna TV tunani kala kala aranta, wanan sanarwan nan na iya tasake saurara rasa abinda zatayi yasa tabude kofa tafice daga dakin, dakin Hajiya tabude tashiga dake meeting a zoom na retired lawyers, ita kebada report din ga glasses akan idanunta, kallon Du'a dake kallonta tayi hakan yasa Du'a tashigo wani book dake kusada ita tadauka rubutu tamata sanan tabata kallon rubutun Hajiya tayi ta gyadamata kai tareda daukan purse dinta ta zaro 10k tabata, karba tayi cikeda jin dadi tafito daga dakin sanan tasauko kasa da sauri tana murna tai wajen Razika dake dakinsu tace "Grandma tace kirakani saloon jeki shirya nima bari na shirya" gyadamai kai Razika tayi tace "kinbar wayan ki a dinning tun jiya" murmushi tayi tace "zan dauka nasan Su Aneesa ne bari naje na shirya" sama tayi, shiryawa tayi cikin wani black abaya mai kyan gaske, sanan tazauna tai rolling veils dinta dayay kyau shima ta feffesa turare tafito rikeda handbag, a falo tasami Razika tace "yauwa kin shirya muje to" gyadamata kai Razika tayi suka fice, driver Hajiya ya kwashe su zuwa wani saloon daba na ranan nan ba dantace dagaske bazata wanan ba, tsife mata kalaban akayi sanan aka wanke mata kan sai murmushi take ta kosa agama, gamawa akayi aka mata blowing hair din yabushe tass sanan matan tace "Hajiya wani style za'a miki" dasauri Razika tace "asake mata kalba amman yan kanana kanana this time" dasauri Du'a tace "a'a ayi manya manya" dasauri Razika tace "please amiki kanana Du'a ai tanada sauri" dagakai Du'a tayi takalli matan tace "idan kikai kanana zaki gama kafin 4" kasa magana da kyau matan tayi sabida idanun da Du'a ta zubamata yarinya kaman ita tai kanta. "eh bakice komiba zaki gamamin kafin 4" kasa magana matan tayi sai kawai gyadamata kai datayi murmushi sosai Razika tayi tace "kingani na gayamiki za'a gama, afara to amata mai kyau mai style" fara mata kalaban matan tayi tana mamakin yawan gashin Du'a dakeda tsayi, tsayin shikecin lokaci ma ba asalin kitson ba, wajajen 3 Du'a takalli uban tulin gashinta da ba'ayi ba tace "3 yayi sai yanzu mukai rabi" kallon fuskanta matan tayi ganin Du'a tayi kaman zatai kuka yasa dasauri tace "yakuri gashinki nada tsayi sosai ne gashi robber hair, I am going as fast as I can, zan gama dawuri" gyadamata kai kawai Du'a tayi matan tacigaba da kitson da saurinta, tanaji tana gani 4 yayi ana kan kalaban ba'a gama gamaba sosai taji hawaye yazo mata amman ta daure tahana kanta wuraren 5 matan tagama, tashi tayi tsaye da sauri tana parking kitson da ribbon dinta tadau gyalen ta ta tafa wanan karan batama tsaya rolling ba duka kudin da Hajiya tabata tabama matar sanan takalli Razika tace "muje" tashi Razika tayi suka fito tace "wai ina kike sauri zakije ba gida zamuba" girgixa mata kai tayi suka shiga mota, tace "dan Allah transcorp  hotel zaka kaimu" sanan tajuya takalli Razika tace "program liyafa akeyi na matasa kan fara sana'a tun karfe hudu aka fara" gyadamata kai kawai Razika tayi dan batasan wani program bane ba akeyi ba but yanda taga Du'a tasan it must be something very important to her.

Tunda suka shiga hotel din gabanta ke faduwa sosai parking yayi hakan yasa suka bude suka fito suna kallon kofan dazai sadasu to asalin cikin hotel din da wani security guard dake sanye da uniform ke tsaye yana kallonsu, kallon Du'a dataga ta tsaya sakakau Razika tayi yanda take kalle kalle tace "a ina akeyin abun" dan zaro idanu Du'a tayi irin na asalin wanda doesn't have any idea akan abu tayi tace "nima bansani ba" ganin haka yasa  Razika tadan matso kusada ita murya chan ciki tace "to ki tambayi  wanan security daman gashinan yanata kallonki" dan zaro idanu tayi saikuma tajuya takalli mutumin dake kallonsu har lokacin kafin Du'a tai magana yace "are you here for the program"? Gyadamai kai Du'a tayi batare datai magana ba, yace "to ku shiga hall din ma 8th floor" gyadamai kai tasakeyi sanan tawuce tafara tafiya tana kama hannun Razika suka shiga ciki tare, tunda taji 8th floor yasa tasan akwai elevator hakan yasa sukai hanyar stairs suka farabin bene, da sauri sauri gudu gudu take hawa stairs din, sosai sukai nisa dafa bango Razika tayi tana nishi sosai tace "wayyo Allah na kafana, Du'a nagaji wlh" kaman zata fashe da kuka tace "nima wlh nagaji kinga ankusan gamawa dan Allah muje" tashi Razika tayi tana nishi suka cigaba dabin stairs din ita karan kanta Du'a daurewa tayi kaman kaman kafafunta zasu tsinke, ahaka suka kai floor din tundaga tsayin corridor wajen sukaga mutane sunyi layi hadaddun yammata da maza anyi layi har zuwa hall din da cikin hall din da ake asalin abun, ganin anbisu da kallo yasa Du'a tabi Razika da kallo saikuma takoma tabayan Razika tana sussunar dakai kaman mara gaskiya dan wani iri takeji idan ana kallonta, murya chan kasa kaman mai whispering tace "Razika tambaya mana inane hall din me akeyi anan" dan Jim Razika tayi saikuma ta kalli wata mata dake tsaye alayi tana sanye da hijabi tace "dan Allah inane hall din" hall din dake gabansu matan ta nuna mata tace "ga hall dinan" ahankali Razika cikeda tausasa murya sabida karta gaji da ita tace "angama ne me kukeyi alayi dayawa haka"? File din dake hannunta matan ta nunama Razika tace "anriga angama liyafan, layin nan kuma na masu son irin su email dinshi ne sanan muna using opportunity din muna submitting CV dinmu akwai possibility na zaiyi recruitment koma baiyiba tunda gwamnati sunsan da zamanshi zaya iya sama mana aiki kingane, long layi ne about 100 people naciki duk sunata bashi kuma ya karba" gyadamata kai Razika tayi tace " nagode sosai, sanan tadan matsa baya still Du'a na labe abayanta tace "kinji ko, ina zamu iya jiran this plenty mutane dasunkai 200, Hajiya tasan kinzo nan" girgixa mata kai tayi alamun a'a, hakan yasa Razika tace "to gaskiya ki wuce mutane tunda anriga angama bazamu kafin akawo kanmu goman dare tayi" gyadamata kai Du'a tayi asanyaye Razika tace "muje" juyawa tayi ahankali suka fara tafiya saikuma ta tsaya Razika takalleta tace "menene?" ahankali tace "I want to say thank u" bata jira amsan Razika ba tawuce wajen da saurinta tai gaban hall din tana sussunnar dakai batai wata wataba kawai ta danna kanta ta kutsa tacikin mutanen dake layi tashiga hall din, tana shiga yan waje sukahau ihu chaaa barinma matan wasu suka biyota ciki ganin haka yasa tawani irin kwasa da gudu dan hall din nada makeken girma sunachan kan stage, dagudu itama Razika tashigo tana kwala mata kira. "Du'a, Du'a, Du'a ina zaki".....

Chak ya tsayar da rubutun dayake ma wata a littafin data bashi, yau yana sanye cikin wani gray suit dayafi na kullum mai kyau, yana zaune yadaura kafa daya kan daya agaban wani hadadden table, both sides dinshi bodyguards ne tsaye rike da gun, sai wasu manyan mutane dake kan stage din suma a zazzaune da suit, tsayar da rubutun chak yayi batare daya dago kanshi ba jin ana ihu da hayaniya a hall din amman suna daya kunnenshi ya iya karba Du'a!

Dawani irin gudu Du'a takaraso gaban hall din daidai inda mutum zai fara hawa yan kirgaggun stairs din dazai sadaka to stage din wanda anan line din yafara duk wanda yazo kanshi xaihau stage ne yaje yasauko, wani irin tsayawa Du'a tayi tana nishi sama sama kaman kirjinta zai fashe sabida gudun datayi tana kallonshi ganin yes yes tabbas shine, daidai lokacin matan dasuka biyota suka karaso cikeda fada sukace. "ke waye dazaki baromu alayi ki gudo ki shigo ciki" juyawa tayi tasake kallonshi cikin muryanta mai shegen zagin nan da dadi dake rawa kuma sabida tsabagen tsoro dakuma gudun datayi tana kallonshi still tace "thank u" duk binta akai da kallo ganin yanda take kallonshi tacemai thank you, wani mutum dakebinta da kallo ne dakekan stage din yace "Pretty lady ki koma kibi layi idan akazo kanki then you now tell him thank u, as it is so many people sun cemai thank you yours is not first kinga he is busy" yanuna mata Asad dayama cigaba da attending to mutane kaman ma baisan something is going on ba, gyadama mutumin kaitayi hawaye na neman zubomata amman ta daure tana kallonshi ahankali tace "thank you for saving my life" daya daga cikin matayen dasuka biyota ne tawani finciketa tace "dalla malama kizo kifita" dasauri Razika takama hannun matan tace "kisaketa dalla kema ai tafiya zamuyi, muje Du'a" kasa daga kafa daga wajen Du'a tayi tana tsaye kaman an dasata tana kallonshi, muryanta wanan karan narawa sosai hawaye yacika idanunta sosai tace "thank you for saving my life" fincikanta matan tasakeyi hakan yasa Razika tace "malama dalla kisaketa, Du'a let's go" kin motsi Du'a tayi kaman ba ita akeja ba, nan hall din yadau hayaniya, ahankali ya sallami guy din dake gabanshi sanan yajuyo da kanshi ahankali yadaura fararen idanunshi akan na Du'a da akeja taki tafiya tana kallonshi, faduwa gabanta yayi yanda yanda ya kalleta, wani irin yatsine fuska yayi sanan yadauke kanshi daga kanta yajuya yakalli security dake gefen damanshi batare daya kalleta ba yana jiran next person dake kan line yanuna Du'a da yatsanshi a wulakanci yace "fitarmin da yarinyar nan daga hall dinan please and throw her outside this premises".

wanna talk to me no problem just click on this link wa.me/+2347012181461

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now