DABI'AR ZUCIYA NA HUGUMA

1.7K 18 0
                                    

01
*DABI'AR ZUCIYA*❤‍🩹❤‍🩹
_FREE PAGE_

*JANUARY!* *JANUARY!!* *JANUARY!!!*

*_A SABON WATAN JANUARY 2022_*

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

*DABI'AR ZUCIYA*
_FREE PAGE_ 01

        Rana ce sosai wadda ta qwalle daga kowanne sashe na sararin subhana zuwa fadin filin duniya iyakar hangen dan adam,wadda take bada tsananin haske da kuma zafi,irin zafin dake sanyawa kowanne mai rai wala mutum ko dabba neman mafaka da zai samu inuwa da zata hutashshehi ta kuma dauke zafi da radadin da ranar ta haifar tun daga gangar jiki izuwa qwaqwalwa.

        A irin wannan lokacinne ummukulsum ke tafiya cike da bacin rai da wani irin fushi,yarinya matashiya,wadda gaba daya shekarunta ba zasu haura sha biyar kacal a duniya ba.

         Baqa ce ita,ba irin wuluk din nan ba,saidai tafi chocolate colour duhun fata,tana da yalwar gashin kai dana gira,madaidaicin baki da matsakaitan idanuwa,tana da baiwar fararen idanuwa,haqoran bakinta milk colour ne masu qyalli,madaidaicin baki da matsakaiciyar haba wadda ta qawata shape din fuskarta,a taqaice ummukulsum na cikin mata masu matsakaicin kyau.

         Zafin da take ji a zuciyarta yafi wanda takeji a tsakar kanta sanda ranar ke kwadarta,idanunta cika yake da hawaye tana ta qoqarin maidashi,saboda sam batason tayi kukan,mutum ce ita mai jumuri da dakakkiyar zuciya,wanda wasu suka fassara hakan da tsananin taurin kai da kuma baqin hali.

       Tana tafe tana hadiye abinda ya dunqule mata a wuyan,tana kuma duban yadda hanyoyin layukansu ya dade qwal babu jama'a,da alama kowa ya nufi gona,wadanda kuma basu da gonakin zuwa ko basu da abinda xasuyi cikin gonar sun tafi sabgogin gabansu.

        Hannun hagunta ta kalla sanda take gab da gota wani siririn lungu,saita yanke shawarar tabi tanan din,don zaifi mata saurin isa gida,duk da ba kasafai ta fiya son bin lungun ba saidai dole,hatta da mahaifiyarta wani lokaci takan ce su haqura da bin hanyar,saidai a yanzun tana son isa gida da wuri ne,don ta baro mahaifiyar tata tana dakon dawowarta.

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now