HALIN GIRMA NA RANO

333 5 0
                                    

*HALIN GIRMA!*

©®Hafsat Rano.

FREE PAGES!

(1)

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

(1)

***Komai na rayuwa na tafiya ne bisa tsari da kudurar ubangiji, komai ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin kaddarar sa, Wala kaddara mai kyau ko kuma akasin ta. Yarda da Kaddara me kyau ko mara kyau na cikin Imani!

   A tsaye take gaban sink din cikin toilet din tana wanke kananan kayan da ya kasance mallakin Maama da Zeenat, lokaci zuwa lokaci tana cire hannun ta tana yarfe shi saboda sanyin da ake zugawa kasancewar karshen December ne a lokacin da ake zuga sanyi. Dauraye kayan tayi ta yi saurin fitowa ganin haske ya hudo ta window din toilet din. Karfe shida da rabi agogon falon ya nuna, tayi saurin karasawa kitchen din domin dora abin karin kumallo kafin ahalin gidan su tashi.
  Tun kafin asubah take fara ayyukan gidan wani lokacin har karfe tara na safe bata kamalla wa, duk kuwa da tana iyakar kokarin ganin bata wuce taran ba saboda karatun ta na islamiya da take zuwa duk weekend, tana ganin shine kadai gatan da zata yi wa rayuwar ta a halin da take ciki a gidan mahaifin ta. Bata fatan wani ya shiga irin rayuwar da take ta kunci da tsantsar makirci, babu wanda ya san halin da take ciki balle ya kawo mata dauki, bata isa ta bud'e baki ba saboda kowa ganin kirki da karamcin Maman yake, mace ce me masifar kirki, me haba haba da saka duk wani abu nata gaba da na duk sauran yayanta a idon ahalin gidan,a badini kuwa bata da maraba da bola.
   Kowa kallon mara dadin zama yake mata ko kuma mara godiyar Allah saboda rashin walwalar da take fama da har ya shafi kaso mafi rinjaye na rayuwar ta, zaka dauka bata dariya ko doguwar magana sai dai bata da sukunin yin kamar sauran yan matan gidan nasu.
  Kowa kallon wadda tayi sa'ar uwar riko yake mata, ayi ta sakawa Maman albarka da yabo a gabanta tana amshewa amma a bayan idon mutane! Bakar wahalar da take sha ba zata misaltu ba.
   Da tunanin ta kammala aikin ta dauraye hannayen ta sannan ta fito ta jera musu a saman dining ta dauko nata a dan plate ta wuce zuwa dakin su.

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now