SHAFI NA BIYU

732 11 0
                                    

*DABI'AR ZUCIYA*
_FREE PAGE_
02

*Zafafa biyar books 2022*🔥🔥🔥🔥🔥

*SO DA ZUCIYA* _miss xoxo_

*DEEN MARSHALL* _Mamuhghee_

*HALIM GIRMA* _Hafsat rano_

*TAKUN SAƘA* _Billyn abdul_

*DABI'AR ZUCIYA* _Huguma_

*KU TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN*

08184017082
KO KUMA
09134848107


       Saida habiba ta qara hanzari sannan ta cimmata
"Ga kudin yaaya" waiwayowa tayi ta dubi kudin sannan ta kalleta tana ci gaba da tafia
"Saura kadan na daina yiwa mutane da yawa kitso cikin qauyen nan" kai habiba ta kada tana sake matsowa sosai kusa da ita
"Kada kiyi fushi yaaya,indai kana sana'a dole ka sanya haquri"
"Na fara gajiya da wulaqancinsu da cin fuskarsu,ta yaya za'ayi ace kaida haqqinka sai an wulaqantaka sannan a baka,sai kace bara kayi ko roqo?"
"Kiyi haquri,komai mai wucewa ne,watarana sai labari" shuru tayi bata amsata ba,haka suka ci gaba da tafiya tana hadiyar bacin ranta,tana son ta cinye abinda ke ranta kafin su isa gida,don bataso ta koma wa ummansu a haka bare ta damu da sanin abinda ya faru.

        Kanti lawandi suka nufa da niyyar siyan garin kwaki da suger su isa gida dashi,saidai sun taras kantin nasa a rufe yake,saboda rana ta tasa,wala'alla sai wajejen la'asar kuma zaya sake budewa,tsaki kaltum taja
"Kinga,zo mubi ta gidansu wasila,baabarsu tana siyarwa saimu siya a can" da haka suka karkata suka bi wata hanya dake hannun hagunsu.

       Wasila itace qawa daya tilo wadda kaltum keda ita kaf fadin qauyen,kusan kowa ya sansu tare,kasancewar bata da tarin qawaye bare ta sanyasu a jikinta,shi yasa wasilan ce kawai za'a iya kiranta qawa ta sosai ga kaltume,akwai sauran 'yammata da take hulda dasu,saidai mu'amalarsu ta tsaya ne kawai iya gaisuwar mutunci,koma bayan wasilan da takanyi shawara da ita,kuma sukanyi musayar sirri a wadansu lokuttan.

         Kusan tare sukayi sallama ita da habiba a tsakar gidansu wasilan,gidan nasu su sassa uku ne,daya hada da nata sassan dana qannen babanta su biyu,babar wasila da daya matar qanin baban nata ta samu qarqashin rumfar da suke girki,an sauke tukunya ana kwashe abincin rana,a ladabce kamar yadda halayya da dabi'arsu take suka duqa suka gaidasu,suka amsa suna tambayar ummansu
"Hala kin biyo qawartaki ne,yau baki ganta ba ko?" Babar wasila ta fada tana dariya,murmushi kaltum tayi,sannan ta amsata
"Dama munyi magana da ita jiya,tace zata shiga talla yau har ɓaure,bata dawo ba kenan?"
"Wallahi,inata dai zuba ido,nasan tana kan hanya" kaltum din bata amsa ba saita miqa mata kudin hannunta
"Kwaki zaki bamu baaba na hamsin sukari na hamsin"
"To...to" ta fada tana karbar kudin,sannan ta miqe tana dosar sassanta.

        Tana shiga babu jimawa wasila ta kwada sallama farfajiyar gidan,kanta dauke da babbar kwalla wadda akw cika mata ita da awara kusan kullum kwanan duniya,abu guda daya tak da basu taba yiba tsahon rayuwarsu shine talla,ko kusa ko alama ummansu tace bata da sha'awar dora musu tallan koda tana da jarin yin abun sana'a,ta gwammace tayi koma meye a gidan,idan da rabo za'a shigo har inda take a siya,abinda mutane da dama sukewa kallon ba komai bane illa zallar girman kai da ganin tafi wani,ganin cewa kusan mafi yawa mafi akasari 'yammatan qauyen suna talla,kuma dashi suka dogara,don yawancinsu dashi sukewa kansu kayan daki kaf harda sauran canji da za'ayi shagalin biki dashi.

        Da sauri kaltum ta qarasa tana tayata sauke kwallar daga kanta,ta duqa suka ajjiyeta a qasa a tare,saita dago tana kallon wasilan cikin murmushi
"Sannu...yanzu muke zancanki da baba" gammon dake kanta ta sauke ta riqe a hannunta tana gantsarewa,alamun bayanta ya riqe,fuskarta a yatsine tace
"Wallahi wahalar abun hawa,sai da muka sha wahala yau kafin mu samu abun hawan daya qaraso damu cikin qauyen nan".

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now