page 2

191 3 0
                                    

*_DEEN MARSHALL_*
_Mamuhgee_

2
Da wani irin kallo Hanifa kebin Naj dake tsaye bakin wardrobe daure da towel me kauri da girma brown color fuskarta fayau Kamar ko yaushe Babu wata damuwar abubuwan dake addabe da rayuwarta Kamar fitinar ummanta data su dattaji uwa uba ta Abaas datafi ta kowa zama abin baqin ciki da takaici.

Sake kallon fuskarta Hanifa tayi tana zaunawa kan gadon tareda ajiye wayarta gaban madubi tana cewa"

Nayi waya da Sarah dazu.

Batareda ta juyoba tana zare Yan kunnayenta tace"

Kada ki damu da abinda tafada Miki
Idan Akan Abaas ne zuwa yanzu kema kinsaba da halinsa,
Abinsa ya daina damuna yanzu saidai kawai yanda Naga kamar abin nasa kullum rikidewa yake zuwa ga zargi
Zarginma me muni Wanda nake dannewa Ina sharewa sbd Umma dasu Dattijo...

Sai alokacin Hanifa ta katseta da cewa"

Meyesa Zaki daure sbd su umma bayan su dinma da zasu bude ido da kyau su duba dabi'u da wasu abubuwan tako Ina Abaas Bai cancanta ba bama Haka ba yaushe Kika fara damuwa da abinda ake fada na cewan kece Kika qi aure da har Kika zabi auren Abaas lamido Wanda Ni kwata kwata baima kwantaminba
Gabaki daya Banga halayen maza masu hakuriba ko iya tattala mace atareda Abaas.

Ajiyar zuciya Naj din ta sauke Jin ran Hanifan yafara baci da zancen ta waiwayo ahankali ta kalleta tareda sakin wani irin lafiyyan murmushi Wanda kusan Arayuwarta tunda tazama budurwa cikakkiya kaf kannenta sukai aure aka sakota gaba tako Ina Hanifan ce kawai take iya ganin murmushinta me fidda asalin kyawunta Wanda yafito daga ainihin cikin zuciyarta sai kuwa Dr sa'id Wanda yake tamkar 'dan uwa Kuma aboki agareta shima idan tana tare dashi takanji nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ya fahimceta tareda sanin halayyarta fiyeda 'yan uwanta na jini duk da kuwa Bata hada komai dashi ba face kasancewarsa likitan Hanifa tun suna yara har yanzu dasuka girma.

Zama tayi gefen Hanifan tana kallonta tace"

Ba abun damuwa bane basai kin saka damuwan Abaas ba aranki
Mubar maganan ma sunan Harya fara sakamun ciwon Kai.

Hanifa Sam ko sunan Abaas din tafi kowa takaicin saurara sbd tun ranar farko da zancen Yana son Naj din ya sauka a kunnenta ta qarewa background dinsa da halayyarsa bincike bataga ta inda ya cancanta Naj ba kafin daga baya taji fara aikinsa da zuba hannun jarinsa a ALFA'S dinsu Wanda Sam bataso hakan ba Amma sbd zagayen da yayi akai Masa Hanya ya bullo ta gurin JALALUDDEEN qaninta Wanda dukiyarsa tafi ta kowa yawa acikin ALFA'S din hadda kuwa mahaifinsu da shine me asalin companies din na Nan portharcourt dama na wajenta.

Miqewa Naj din tayi tana cewa"

Bari nayi wanka nafito zamuyi mgna akan Isma'eel ya kirani dazu akan maganar zuwanki ganin likita A Jamaica.

Kallon kyakkyawar fuskarta Hanifa tayi tana murmushi tace"

Allah sarki Zawj.

Da yanayi na sanyi Naj ta kalleta zuciyarta na yin sanyi da dukkanin wata damuwar Hanifa ko ciwonta.

Toilet din dakin nata ta shige Dan dama wanka zatayi Hanifan ta shigo.
Bayan shigarta wanka miqewa Hanifan tayi ta sauko daga kan gadon ta zura flat slippers dinta na _Jimmy choo_ ta fita dakin ta nufi gurin umma dake zaune har lokacin tana aikin zuba wasu turaren wuta masu tsananin qamshi ta zauna gefen umman tun kafin ta qarasa zama umman tace"

Kun gamo shawaran yanda zaku fuskanci Dattijo da Dadah idan Maganar aurenta da Abbas ta fasu Dan nasan wannan doguwar fuskar da Kika shigo da ita bata lafiya bace Dole akwai abinda yake faruwa tsakaninta da Abbas.

Dan guntun murmushi Hanifa ta sauke tana Taya umman rufe kwalaben turarukan tace"

Umma meyesa kuka kasa gane irin taurin zuciya da qarfin imanin da Naj take dashi sbd ba kowane zai iya hadiyewa ba yakuma danne irin Gori da takura tareda cin fuskan da ake Mata akan rashin yin aure ba?

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now