✨ *MATANA*✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*
*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*
*Whatsapp group females only please*
https://chat.whatsapp.com/Ib3gwXORbTB1GxcVr0FdAw
*004*
Kusan 3am ya shigo gida, babu kowa a falon gidan fitulu ma duk an kashe, banda fitilar dake dining area wadda ta ɗan hasko falon, dakinsa ya wuce, bathroom ya shiga yana sakarwa kansa ruwan sanyi, a duk lokacin da yayi spending time da Zarah yana samun kansa cikin nishadi ne, haryanzu bai daina jin dumin jikinta a tare dashi ba.. ruwan ya dade yana zuba a jikinsa sannan ya kashe yana daura towel a waist dinsa, alwala yayo sannan ya fito. Bai kwanta ba sai da yayi sallar asuba.. cikin duvet yashige yana jin zuciyarsa cikin nishadi dandanan bacci ya dauke shi. Tun daren jiya Mami ke kiran Wayarsa amma switchoff, ranta a matuƙar ɓace yake, Umar na kwance yana sharar bacci yaji wayarsa ta fara ringing, ganin Mami ke kiransa yasa shi dan Runtsa ido dan yasan bazai wuce zancen Ammar ba, tun kafin yayi sallama ta fara faɗin " Ammar a gidanku ya kwana? Shafa sajensa yayi yana fad'in " Eh Mami" "Amma dan wulakanci bazai iya kirana ya sanar dani ba? Bashi wayar! Zaro ido Umar yayi kafin kuma ya ce " Ya shiga toilet" "idan ya fito ka ce ya kirani! Daga haka ta katse wayar.. da sauri Umar ya shiga kiran layin Ammar amma a kashe. Kashe wayarsa yayi ya ajiye dan baya son fadan Mami. Sai 11am sannan Ammar ya tashi daga bacci. Wanka yayi ya shirya cikin shirt da wando yayi kyau sosai. ATM da makullin mota ya dauka yana fitowa daga ɗakin. Fatima ya gani zaune a falo tana tsifa. Wani kallo yayi mata yana haɗe fuska ya ce " Ban hanaku tsife kai a falo ba? Duk girman cikin dakinku bazakuyi tsifa a ciki ba sai kunzo falo? A tsorace ta rufe gashinta dan tayi zaton baya gidan kamar yadda taji Mami ta fada dazu.. Tsaki yayi yana nufar dakin Mami. Tsaye ya ganta gaban closet tana fito da atamfofi wanda ba'a dinka ba.. "Mami ina kwana? Kallonsa ta tsaya yi fuska a tsuke ta ce " Me ya hanaka zuwa wajen Bilki jiya? "Ciwan kai! Ya fada in short. Tasan karya yake amma ta rabu dashi ta cigaba da abinda takeyi.. tashi yayi ya fice daga ɗakin.. banki ya nufa, ta account din gidan ya turawa Mami kudin Event ɗin dan maganar gaskiya bazai iya kashe wannan kudin ba akan auren Bilki, lefan ma da yake haɗawa dan babu yadda ya iya da Mami ne. Gidansu Umar ya wuce.. a falo ya tarar da Umar din yana kallo, zama yayi a kujerar dake kusa dashi yana furzar da iska.. "A ina ka kwana jiya? Umar ya fada yana masa wani kallo. "Hajiya Babba bata nanne? Karamin tsaki Umar yayi yana fad'in " Ina tambayarka kana tambayata? Dariya yayi kaɗan yana cewa "Easy man! A gida na kwana wallahi, yawwa inaso kacewa friend dinka ya kawo min waya irin waccan wadda ya kawo min 2weeks back" "Me zakayi da waya? Kodai Bilki zaka siyawa? Wani kallon tara saura kwata Ammar yayi masa sannan ya ce , "Idan ina zancen arziki ka daina sako min zancen yarinyar nan" "Ok sir! Umar ya fada yana dariya. "Seriously me zakayi da waya yanzu? Ko wanine yake nema? Sai da Ammar ya dan sosa kai sannan ya ce " Ni nake so, na bawa Zarah waccan" "Zarah kuma? "Yeah ita! Jiya wajenta naje a Abuja shiyasa ban dawo gida da wuri ba Mami tayi tunanin ban kwana a gida ba" Gyada kai Umar yayi yana kallon sa ya ce " Shiyasa naganka wasai yau din nan babu haɗe²n rai. Dariya Amma yana yana kallon Umar ya ce " Ɗan umarii kenan, yanzu idan free kake muje wajensa Please sannan kofar falon gidana handle din yana da matsala sai muje a gyara but everything is perfect" "Ok, muje daki ku gaisa da Hajiya sai mu wuce" Da ok Ammar ya amsa masa sannan suka nufi dakin Hajiya Babba.
Bayan sun fito wajen abokin Umar suka fara zuwa, wayar ya karba yayi payment sannan suka biya wajen kafinta, tare da kafintan suka je gidan Ammar din, Duplex ne me dan karan kyau, wanda ya gina musanman dan shi da Zarah gaba daya tsarin gidan irin na turai ne har equipment din da yake ciki.. basu dau lokaci ba aka gyara komai, anan gidan ya jona chajin wayarsa.. Umar kuwa duba gidan ya tafi yi dan ya kwana biyu bai zo ba.. sai bayan la'asar suka baro gidan.. "Kaga gidan dai -dai na mata biyu" Umar ya fada yana kallonsa. "Yeah mata 2 zasu iya zama amma bazan iya hada Bilkisu da Zarah ba" "Me kake nufi? Cewar Umar yana kallonsa. "Abinda kaji mana, na saka Bilkisu a sabon gida ma ballantana Zarah? Itama nata daban zan gina mata insha Allah! Murmushi Umar yayi yana kallon danuwan nashi ya ce, " Allah ya tabbatar da alkhairi! Da Amin Ammar ya amsa yana cigaba da tukinsa.... A chan gidansu kuwa Aunty Sadiya ce da Mami a daki suna ta zuba kaya cikin akwatunan dake gabansu.. "Wai ni kuwa Yaya, Ammaru ya turo da kudin Event ɗinnan kuwa? "Ba dolensa ba ma! Yanzu ma jira nake ya dawo naji dalilin daya hanashi zuwa wajen Bilkin! Cewar Mami tana kallon Sadiyan "Gaskiya dai dan bamu ganshi ba, da ace ma shi zan jira ai da ba'a fara gyare min ƴa ba, dubu fa dari uku na biya matar kudin gyaran jiki sati biyu kawai kinsan yar Sudan ce matar ta iya sosai, ko bikinsu Fatima ne ya tashi ita zatayi musu har kunshi da kitso duk yana cikin kuɗin, karkiso kiga yadda Bilki ta dawo kamar balarabiya dama ga ta fara" Murmushi Mami tayi tana kallon ƙanwarta ta ce " Ai nasan ma dole ya sota idan akayi auren nan, yarinya dai babu abinda ta rasa, kyau dai sai dai ace Masha Allah dan duk tafi su Maryam kyau, wannan fari farin dake rudar samarin yanzu gashi Allah ya bata, jajir da ita, ni wallahi banga ma abinda ya gani jiki waccan baƙar yarinyar ba! Shegia mummuna da ita kamar takashin jaki, baki kamar na tsuntsu! Bilki ce dama dai² da shi jinin larabawa tunda dai babanta dan Sudan ne ai Balarabe ne" Dariya Aunty Sadiya tayi tana kallon yayarta ta ce " Aikuwa dai! Mami bata kai ga yin magana ba Ammar ya shigo yana yin sallama kansa a ƙasa. Ganin Aunty Sadiya a dakin ya saka shi tsuke fuska yana tsugunnawa ya gaidasu.. Aunty Sadiya ce kawai ta amsa tana fad'in "Ango kasha khamshi" Bai ce da ita komai ba ya maida dubansa ga Maminsa ya ce " Za'a iya fara jeran! Daga haka ya miƙe zai fice yaji Maminsa ta ce " Bazan kara maimaita kaina ba Ammar! Ya gane me take nufi a hankali ya ce " Sorry Mami! Daga haka ya fita. Maryam ya gani a falo tana raba wasu materials.. "Wannan kayan waye? Ya fada yana kallon gowns din da take ninkewa dan ta gama warewa kowa nashi.. "Kayan mu ne, ni, Fatima da Fa'iza na dinner! Karamin tsaki yayi ya wuce bedroom dinsa, shi ko ɗinki ma beyi ba kuma bazaiyi b!
Layin Zarah ya fara kira yasan dai by now tayi shirin kwanciya, he pity her dan k'anwar mamanta ta iya loda mata aiki kamar ta samu maid! Har ta gama ringing bata dauka ba, sake kira yayi.. lokacin Zarah ta fito daga wanka dan tun safe bata samu tayi ba saboda aiki. Hasken wayar ta gani. Bata dauka ba duk da tasan shine. Riga mara nauyi ta saka ta kwanta.. sai lokacin ta samu damar danne² a wayar. Babu abinda ya goge komai nashi yana kai. Call logs, pictures da chats dinsa.. wani kiran ne ya sake shigowa sai data kusa tsinkewa sannan ta dauka tana yin shuru.. "Zarah! "Uhmmm! Ta fada chan ƙasa... "Ya kike? Da lafiya ta amsa ba tare da ta kara cewa komai ba. "Zan kiraki vd call yanzu please! Da ok ta amsa masa tana katse wayar.. Kashe wayar tayi gaba daya ta ajiye ta a gefanta ta kwanta tana lumshe idanunta. Ammar kuwa jira yake yaga ta hau online amma shuru har 11, sake kiran wayarta yayi yaji switchoff, yasan kashewa tayi amma hakan be saka shi yin fushi ba, shima kwanciya yayi cike da tunaninta. Washe gari ta kama Wednesday wanda yayi dai dai da saura 2 days daurin aure. Yana zaune a daki, Umar ya shigo rike da bag na kaya me kyau.. ajiye masa jakar yayi a kan gado yana fad'in " Kayan daurin aure, reception da kuma dinner sako daga Hajiya babba idan kaga dama kar ka saka! Ya ƙarashe maganar yana zama a gefansa. "I was waiting for you dama, inaso ka rakani wajen yarinyar nan! Mami ta dameni" Kwanciya Umar yayi yana juya masa baya ya ce " Babu inda zanje na gaji, akan kayan nan sai da Hajiya ta min faɗa, Baffa ma haka anjima da yamma za'a kawo takalman! Ka tashi kawai ka tafi minti nawa ka dawo" Ammar bai ce komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin. Gidan har ya fara cika da jama'a bai bi takan kowa ba ya fice abinsa.. a kofar gidan Aunty Sadiya yayi parking, saukowa yayi daga motarsa ya karasa cikin gidan.. shima akwai jama'a amma ba kamar gidansu ba.. daga kofar falo ya tsaya ya ciro wayarsa yana dialing number Aunty Sadiya, har ta gama ringing bata dauka ba.. ko sake kira beyi ba ya juya ya bar gidan yanzu kam yana da abin fada idan aka ce baije ba idan sunga dama kar suka mata takalmin, tayi yawo a haka wannan kuma ruwanta... Yadda ya bar Umar haka ya dawo ya tarar dashi.. "Ina kaje? Cewar Umar yana kallonsa.. "Wajen Bilki kuma ni banganta ba, na kira number Aunty Sadiya bata dauka ba" "Meyasa baka kira ita Bilkin ba? Kallon tara saura kwata Ammar yayi wa Umar kafin ya ce " Sai na ce maka inada number ta? Taɓa baki Umar yayi bai kara ce da shi uffan ba.
A chan bangaren Zarah kuwa bata dawani lokacin kanta, a kallah tana yin girki kala biyu da safe haka ma da rana, bata da time din tunani kamar da, shine kadai advantage din aikin da takeyi.. yau ma tun tashinta take kitchen wai saurayin Farida zaizo da abokansa anjima.. tana cikin wanke nama Zainab ta shigo tana fad'in " Aunty Farida ta ce kiyi musu harda leman kwakwa da abarba" "Babu Kwakwa ai" Zarah ta fada idanunta kan aikin da takeyi. Taɓa baki Zainab tayi ta fita. Zarah kuwa aikinta ta cigaba da yi. Sai bayan azahar ta kammala komai. Daki ta wuce dan tayi sallah. Bayan ta fito daga toilet Farida ta shigo dakin tana kallon ta ta ce " Zarah sannu da aiki" "Yawwa" Zarah ta amsa tana murmushi. "Gashi chan an kawo kwakwar kiyi sauri ki hada dan sun kusa karasowa" "Toh bari nayi sallah" da ok Farida ta amsa tana fita. Sai da Zarah ta idar da sallah sannan ta nufi kitchen... Har ta gama hada komai basu zo ba. Daki ta koma tayi wanka tana kwanciya a kan katifarta tare da lumshe idanunta. Wayarta ce ta fara vibrating, kin dauka tayi dan bata sonyi magana dashi a yanzun.. sau uku yana kira bata dauka ba. Ammar be gaji ba ya cigaba da kira dan dole Zarah ta ɗauka, "Bakya kusa ne? "Uhm" ta fada a sanyaye. "Ok, ya kike? "Alhamdulillah! Ta amsa masa. " Bakya dai tunani ko? Cikin takaici ta ce " Eh" "Yawwa haka nake so, keep ur self busy please karki bar tunani ya samu damar ziyartan ki, ki kwantar da hankalinki kinji ko? Hawaye taji sun zubo mata, muryarta na ɗan rawa ta ce " Toh" "kuka kikeyi? Ya fada yana saurarenta. Shuru tayi tana Runtsa idanunta kaɗan zuciyarta na bugawa da ƙarfi.. "Zarah dan Allah ki daina kuka plssssss kina saka zuciyata cikin damuwa, Dan Allah kiyii hakuri" "o..ok! Ta amsa tana goge idanunta. "Yawwa, insha Allah next week zanzo kinji ko? Wani kukan ne ya kufce mata tunawa da next week din fa yayi aure har anyi sati! "Zarah Please mana! Kukan ya isa haka nima fa ba daɗi nake ji ba, kuma kina kara min damuwa da damuwarki ne be patient insha Allah komai zai wuce kinji? Bata iya amsa masa ba ta kashe wayar tana kife kanta a jikin katifa ta fara kuka.. "Tabbas data san haka soyayya take da ɗaci da bata fara ba! Da tun farko bata bawa Ammar damar shiga rayuwarta ba! Ita kanta bata san tayi zurfi a soyayyar Ammar ba sai yanzu, bata da wanda zata fadawa damuwarta ya bata shawara a yanzu, kuka taci sosai daga baya kuma ta rarrashi kanta.. a bangaren Ammar gaba daya rasa nutsuwa yayi, sau biyu yana kara kiranta amma bata dauka ba. Bayan sallar isha'i yana zaune a kan sallaya Mami ta shigo, akan sofa ta zauna tana jiransa ya idar da addu'o'in da yake yi.....
08142904255
Autarmama ce
