Chapter fifty Three

804 54 23
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

: Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa, ga koyar da kayan mata najinna faɗa daga er mutan sokoto 👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM

*053*

*END*

           Ya kai 15min yana zaune wajen shakatawar da Amina ta turo masa da address amma bata zo ba, ga shi har yanzu batayi unblocking ɗin shi ba. Sunkunyar da kan shi yayi a jikin table ɗin.

   Jakarta ta ajiye a kan table ɗin wajen kafin ta zauna. Ɗagowa yayi yana kallonta "Meyasa kika daina saka mayafi? " Dama chan bana sakawa, haɗuwa ta da kai na fahimci kana son hakan ya saka nake sakawa yanzu kuwa I'm free" "u'r not free Amina, ko kin manta maganar da mukayi? Gyara siririn dogon gashinta tayi wanda ta yanko shi daga gaban gashinta ya sakko tun daga forehead ɗinta har zuwa kirjinta. "Bazan iya aurenka ba saboda bazan iya kishi da Maryam ba"  "Please Amina, nasan abinda kike ji a zuciyarki wanda be zama lallai bakin  ya iya furta wa ba, nasan kina sona Please ki bani damar da zan wanke kaina a wajenki" murmushi tayi me ciwo tana girgiza kanta ta ce, "Mustapha kenan, nasan ba sona kake ba zaka aureni ne saboda kar ince kayi betraying ɗina, even though I'm old enough ba hakan ne zai saka nayi auren da bazan ji daɗin shi ba, Karka damu na fahimceka sosai kuma ina maka fatan alkhairi" Daga haka ta ɗauki jakarta ta miƙe. Shima miƙawa yayi yana saurin faɗin "Ok stop ignoring me, moreover kiyi unblocking ɗina" Murmushi ta ɗanyi me kyau sannan ta ce, "Why? " Saboda ina so muyi zumunci yhv done more than enough for me and my family, Amina kina da mahimmanci a wajena" da kyar Amina take controlling ɗin emotion ɗinta. Juya masa baya tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta. Sai daya furzar da iska sannan ya kira sunanta yana fad'in " Boost out your anger please, Dan Allah karki ɓoye damuwarki" "Mustapha ya zanyi? Ta faɗa muryarta na rawa. hannunta ya riƙo yana fad'in "kiyi haƙuri nasan nayi breaking heart ɗinki" Zame hannunta tayi tana goge hawayen daya zubo mata a hankali ta ce, "Bakomai wallahi, dama duk abinda ya faru da bawa rubutacce ne daga Allah, haka Allah yaso kuma dama addu'a ta a kullum Allah ya zaɓa mana mafi Alkhairi, kuma this is the best in sha Allah" beyi tsammani ba yaji ta rungumeshi very tight. Runtsa idanunshi yayi da ƙarfi. "I will always love you Mustapha, however God knows the best" sakin shi tayi tana goge idanunta. Abinda take ta avoiding kenan shiyasa bata son long conversation da shi tasan bazata iya riƙe kanta ba. "Kiyi haƙuri" Mustapha ya faɗa kallonta. Murmushin dole tayi tana gyara gashinta ta ce, " Na haƙura har zuciyata Allah yasa hakane yafi zama alkhairi" "Amin, ina fatan Allah ya baki wanda ya fini" Da Amin ta amsa sannan ta wuce ta barshi. Amina zata iya cewa wannan ranar tana ɗaya daga cikin worst day in her life, kuka kuwa ba irin wanda bata sha ba bayan ta koma gida, kullum tana addu'a amma kullum ƙara son Mustapha take yi. Bayan Mustapha ya isa gida be tarar da Maryam ba, abun ya bashi mamaki, gashi ya kira wayarta bata ɗauka ba. Yana nan zaune a falo ta shigo. Tsayawa tayi daga bakin ƙofa ganin shi a zaune, sai kuma ta dake ta shigo ta wuce daki ko uffan bata ce masa. Tashi yayi ya bi ta cikin ɗakin, kaya ya tarar tana cire wa. Ko inda yake bata kalla ba ta sauya kayanta tana ɗaukar wayarta. "Ina kika je? "Inda kaje" Ta bashi amsa tana hura hanci. "Inda naje kamar yaya? "Eh inda kaje ka haɗu da Dr. Kawai saboda kaga ni yarinya ce sai ka dinga min yawo? Daga yin aure just 4months? Meyasa zaka rungumeta? Meyasa?! Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka. Tsayawa yayi yana kallon ta, shi kam be taɓa tunanin Maryam tayi wayon da har zata bishi taga inda zai je ba ballantana har ta saka masa ido akan abinda yaje yi" "Wallahi sai na kira Aunty Zarah" Ta faɗa tana shiga call logs. Ƙwace wayar yayi yana kallon ta ya ce, "I'm so sorry Dan Allah kiyi haƙuri" "Allah bazan haƙura ba sai na faɗawa Aunty Zarah, kawai sai ka fara rumgumeta daga haɗuwa? Ta ƙarashe maganar cike da wauta. "Allah ban rumgumeta ba, kinji na rantse, Please kar muyi haka dake" "Toh kana so kace min idona karya ya min? "A'a idanunki gaskiya suka nuna miki, Nima unexpected naji ta rumgumeni maybe baki zo a kan lokaci ba shi yasa baki ga abinda ya faru ba, amma i beg you karki faɗawa Zarah komai please Mine" harara ta ɓalla masa tana fad'in "Wallahi duk ranar dana ƙara ganinta sai na mata rashin mutunci inga uban daya bata full autonomy da zata rumgume min mijina! Daga haka ta fita ta barshi. Ajiyar zuciya ya sauke yana zama a kan gado. Shi kam bai san haka take da faɗa ba, gaba ɗaya ta rufe idanunta kamar bata san matsayin shi a wajenta ba. Maryam kuwa bayan ta koma falo kasa zama tayi, kishi duk ya rufeta da baƙin ciki, musanman yadda take hango yadda Dr ta rumgumeshi very tight, gashi ita aba komai ma sha Allah, saɓanin ita, dan dama already tasan babu abinda zata nunawa Dr shiyasa ma kishin yake ƙara harzuƙa. Fitowa yayi daga ɗakin ya ganta zaune tana karkaɗa ƙafafu. A kusa da ita ya zauna cikin kwantar da murya ya ce, "Ki daina fushin nan dan Allah" banza tayi dashi tana kallon gefe daban. "Magana fa nake" "Ni wallahi idan ban ja mata kunne ba hankali na bazai kwanta ba" Ta faɗa cike da masifa. "Ga nawa ki ja, amma na rokeki karki ce mata komai idan kingata for my own sake please" kallonshi tayi tana kumbura hanci ta ce, "Ok baka so ranta ya ɓaci amma ni ta ɓata min nawa? Shikenan" Daga haka ta bar masa falon. Dafa kanshi yayi shi kam daya san haka abun zai zama bazai ma ce da ita su haɗu ba. Har dare Maryam bata sakko ba sai dai ta daina masifar kawai dai tana amsa masa ciki². Bayan sallar Isha'i tana kwance tana waya da Ammar, Mustapha ya shigo. Kamar zatayi kuka yaji ta ce, "Wallahi yaya yau Yaya Mustapha ma ɓata min rai yayi" "Shi kam ya shiga uku" Ya faɗa a zuciya yana zama. "Lefi ya min kuma be ban hakuri ba" Yaji ta kuma faɗa. Bai ji abinda Ammar yace ba sai yaji Maryam ɗin ta kuma faɗin "Ina Aunty Zarah? Tana kallon Mustapha ta amsa da "Bata toh"  ƙaro volume ɗin wayar tayi dan Mustapha yaji. "Aunty Zarah ina yini? "Lafiya lau Maryam ya kike komai dai lafiya ko? "Yaya yana nan? Maryam ta faɗa tana kallon Mustapha. "Eh bari na kai wa Fatiman" Cewar Zarah da alama so take ta tashi daga in da Ammar ɗin yake. Chan Taji ta ce, "Ina jinki lafiya dai ko? "Yaya ne ya min laifi Allah ki kirashi kice ya daina" "Laifi kuma? Me ya haɗa ku? Cewar Zarah cike da damuwa. Sai data kalli Mustapha, ya sunkuyar da kan shi yana kallon tiles ɗin ɗakin saɓanin da da yake kallonta. Numfashi ta sauke kafin ta ce, "Aunty dan Allah kiyi masa magana, ya daina min laifi yana ɓata min rai bana so" Ajiyar zuciya Zarah tayi kafin ta ce, "Shikenan zan masa magana, ki kula da kanki dan Allah banda wauta yanzu ke matar aurece kinji ko? A hankali ta amsa da toh. "Yawwa kuma abinda na faɗa miki ki dinga yawan yi kina amfani dashi, take care of yourself and your husband karki bashi damar da zai ga wata mace ballantana yace miki zai ƙara aure da ƙuruciyarki da komai, take good care of him kinji ko? Sai data saci kallon Mustapha kafin ta amsa da toh. "Yawwa Allah ya cigaba da kaɗe fitina ya ƙara muku zaman lafiya da son jinanku, ki daina yawan nuna masa fushinki kinji ko? "Toh" ta kuma amsa. "Yawwa ƴar gari, take care bye" Ok bye" Ta faɗa tana ajiye wayar. "Ashe Aunty Zarah ce take koya miki kishi? "Babu wani kishi da take koya min gaskiya ce" "Ok shine daga mun samu saɓani sai ki dinga kai ƙarata? Shikenan bamu da privacy? Kai ta girgiza kafin ta ce, "Ai family ɗina ne kai ma kuma naka ne, gobe idan ka ƙara rumgumeta Ummi zan kira ko Daddy Allah" "Tab, kuma zaki iya kira din? Ya faɗa yana kallonta. "Ok kaje ka rumgumeta ka gani" Murmushi yayi yana Girgiza kai ya ce, "Ni dai dan Allah ki daina faɗawa kowa matsalar mu especially Zarah bana so tayi fushi dani Please" "Toh ka daina ɓata min rai" "shikenan" Ya amsa yana kallonta. Tasowa tayi ta shige jikinshi. Ji tayi yana khamshin turaren mata, turaren kuma me daɗi. Barin jikinshi tayi tana fad'in "Hubby wannan turaren fa? Kafin ya bata amsa zuciyarta har ta harbo mata turaren Dr ne ya shafeshi lokacin data rungume shi. Ƙaramin tsaki tayi a fili ta ce, "Mayya! "Mayya kuma? Cewar Mustapha dan ya gane abinda take nufi. Cire masa rigar tayu tana shinshina singlet ɗin jikin shi, ji tayi kamar itama tana khamshin. Cire masa tayi tana fad'in "Wanka zakayi ni wannan turaren amai yake sani naji" murmushi yayi yana fad'in "Tohm" Tashi yayi ya shiga toilet. Ko da ya fito riƙe da rigarshi ya ganta tana shinshinawa. "Na ɗauka kince turaren amai yake son saka ki? Da sauri tayi wulli da rigar tana kallon shi ta ce, "Ba ruwana" Bai ce komai ba ya fara shiryawa yana murmushi.  Yana fita daga ɗakin ta ɗauko rigar ta cigaba da shinshinawa ita kam ji take khamshin kamar a aljanna sosai take jin bata iya rabuwa da wannan khamshin turare. A haka ya kuma dawowa ya sameta. "Lafiyarki kuwa Mine? Ya faɗa yana kallonta. "Hubby ka siyo min irin wannan turaren inaso" Dariya yayi sosai kafin ya zauna yana karɓar rigar shi ya ce, 'Ya daina saka ki jin aman? Kamar zatayi kuka ta ce, "Dan Allah kaje ka siyo min khamshi ya fara tafiya" "Wai kina nufin yanzu? Rumgumeshi tayi tana shaƙar khamshin turaren shi. Ji tayi yawun bakinta ya tsinke, da sauri ta matsa tana miƙawa tsaye. "Menene? Toilet ta nufa ta tofar da yawu sannan ta dawo ɗakin tana kallonshi ta ce, "Wannan turaren naka ba daɗi dan Allah ka saka wannan rigar" shi kam ya kasa gane kanta cikin yan mintinan nan. Karɓar rigar yayi ya cire ta jikin shi ya saka. Murmushi tayi tana matsowa in da yake ta rungumeshi tare da lumshe idanunta sai shinshina shi take kamar wata police dog. "Maryam I'm not ready for that please" Ya faɗa yana kallonta dan sosai yarinyar take son kunce shi. "Ni bance ka kirata ba amma kayi mata text ta wayata ka tambayata sunan turaren gani nake kamar zan mutu idan na daina jin khamshin" "O..ok" Ya faɗa yana jan numfashi. Barin jikinshi tayi ta ɗauko masa wayarta. A gabanta yayi text ɗin, aikuwa within 2mins tayi masa reply da sunan turaren. Godiya yayi mata sannan ya ɗauko wayarshi. A online ya duba kuma ya ganshi, very expensive kuwa. Guda biyu yayi ordering yana ajiye wayar ya kalleta ya ce, " Anjima kaɗan za'a kawo" Sake rumgume shi tayi ta ce, "Ina ƙaunar mijina" murmushi yayi kamar ba ita ta gama masifa ba ɗazu. "Nima ina kaunar Matata, "Allah  yayi miki albarka" Da Amin ta amsa tana lumshe idanunta.

MATANA ✓Where stories live. Discover now