Chapter fifty one

492 43 17
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

: Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa, ga koyar da kayan mata najinna faɗa daga er mutan sokoto 👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM

*051*

        *ABUJA*

       Mustapha na durƙushe gaban Daddy kan sa a sunkuye da alama magana Daddyn yake masa. Ummi ce ta shigo hannun ta rike da tray na abinci, a kan rug ta ajiye tana zama kan cushion idanunta a kan Mustapha ta ce, "Da rabuwa kayi da shi, ban taɓa ganin sakaran yaro irin shi ba! Wacece Zarah da har zata zaɓa maka wadda zaka aura? Ita lokacin da aka zɓaa mata ta zauna? Shuru Mustapha yayi yana ɗan runtsa idanun shi. "tambayarka nake ta zauna? Ummi ta sake faɗa tana kallon shi. "Ina son Maryam kuma zan aureta ne saboda ina sonta ba wai dan Zarah tace min na aureta ba, tabbas nasan Zarah ce ta haɗa mu amma bata ce min dole na aureta ba, ni nayi ra'ayi kuma ina son yarinyar, just permit me Dan Allah" Ya ƙarashe maganar yana kallon su. "Amma ita Aminan fa? Cewar Daddy. Kafin Mustapha ya ce wani abu Ummi ta fara faɗin "Wai su biyu zai haɗa ya aura dan hauka! Ga yarinyar da kuke tare tun fil'azal yarinya me hankali da sanin ya kamata, ni bansan me yaje ya gano a wajen yarinyar chan ba wanda Amina bata dashi" Numfashi daddy ya sauke yana kallon Mustapha ya ce, "Ka faɗa mata komai? "Eh Daddy, amma bata amince ba" "Yo ta ina zata amince? Ko kaine zaka yarda? Wannan dai kaci amanar ta kuma ban tsanmaci haka daga gareka ba Mustapha" kallon Ummi yayi yana fad'in "Dama ban taɓa sonta ba kuma na faɗa miki tun ba yanzu ba, meyasa bazakiyi farinciki da zaɓina ba? Kullum fa burinki kenan amma yanzu na kawo zaɓina kin nuna bakya so? Why Ummi? "Ni fa ba wai bana so bane, kawai Amina nake ji, me kake so ta dinga daukar mu? Sau biyu ana abu? Sai kace wasan yara? Ita Maryam ɗin daga yin kwana hudu tare a asibiti shikenan ta fara sonka dan gulma? "Mun daɗe muna magana da ita" Cewar Mustapha ba tare da ya kalleta ba. "Kai toh a nufinka a tare za'a aura maka su? Sai daya sunkuyar da kanshi ƙasa sannan ya ce da Daddy, "Amina bata amince ba har yanzu, ni kuma inaso na koma da matata zuwa USA, so zan auri Maryam first in sha Allah, idan yaso ko daga baya ne idan ita Aminan ta sakko Shikenan idan kuma Allah yayi ni ba mijinta bane shima is okay" "Shikanan ta shi kaje, ina dai fatan ka sanar musu goben zamu zo ko? Da Eh ya amsawa daddy sannan ya miƙe ya fita. Yana zaune a ɗakin shi Ummi ta shigo. Iska ya furzar yana gyara zaman shi dan yasan magana tazo yi. Zama tayi tana kallon Mustapha ta ce, "Yanzu kayi wa Amina adalci kenan? Yarinyar nan tana ƙaunarka tana kuma ƙaunar ɗanka tamkar ita ta haifeshi, sakayyar da zakayi mata kenan? "Ummi ba haka bane, wallahi da Amina zata fahimceni zata gane bazan cutar da ita ba, bazan bari tayi dana sani ba " "Ai kai ka kawo wani sabon batu wanda tun asali bata san dashi ba, yaushe zata yarda ka haɗata kishi da wannan jaririyar ƴar? Yarinyar da ko Zainab ta girmeta! "Shikenan Ummi, tunda bakya so, Allah yasa hakane yafi min alkhairi" "Kaga kar ka haɗani da ubanka! Ni bance bana so ba, na faɗa maka Amina nake ji ba wani abun ba" ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta da kyau ya ce, "Kiyi min addu'a kawai, Wallahi ban taɓa tunanin zan iya son wata ƴa mace ba bayan Zarah, amma cikin hukuncin Ubangiji sai gashi na fara son Maryam kuma a shirye nake na aureta, meyasa ba zakiyi murna da hakan ba Ummi? Addu'ar ki ce fa ta amsu" Jikin Ummi a sanyaye ta ce, "Toh shikenan, Allah ya shige mana gaba" murmushi ya ɗanyi kafin ya amsa da Amin. "Toh yanzu idan su daddyn sun je har lokacin aure za'a saka? "Haka dai nake so domin itama zata fara lectures a chan Oxford University this week Kuma nima kinga ba wani long holiday suka bani ba, inaso a ɗaura auren kafin nan, na rigada nayi wa Ammar maganar kafin na baro Kano" "Toh ita zaka barta a chan hostel ne? Kaga ai Oxford ba'a  America take ba, kasan dai yarinya ce ƙarama ga rayuwa ta turai ita kadai a hostel"  "Hakane amma in sha Allah babu wani matsala zan barta a chan ɗin tunda choice ɗinta ne dana yayanta, weekend sai na dinga zuwa ganinta ko kuma lokacin da bata da lectures" Kai Ummi ta girgiza alamar a'a sannan ta ɗora da faɗin "Yafi dai ka samar mata wata makaranta a nan inda kake ko wadda Zainab zata fara zuwa ce" "Kuɗin da Ammar ya kashe fa? Zai tafi a banza ne fa, kawai ki kwantar da hankalin ki, ko da ace first year tayi lokacin za'a sake biyan kuɗin makaranta sai na dawo da ita ta su Zainab ko? "Shikenan Allah ya shige mana gaba" Da Amin ya amsa.

MATANA ✓Where stories live. Discover now