Chapter seventeen

385 29 8
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
      AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*

*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah

*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU

*017*

         Washe gari da safe Mustapha ya kaisu tashar mota, ba yadda Zainab batayi dashi ba ya kaisu ya ce yana da uzuri, Zarah kuwa ko a gefan takalminta. Sai 3pm suka iso garin Kano. Kowacce ta dau kayanta ta tsari Napep ta kama gabanta dama ba magana suke ba.  Saude na karatun Alkur'ani mai girma Zarah ta shigo.. bayan ta kai karshen aya ta amsa sallamar da Zarah tayi tana sakin murmushi ta ce " Na dauka ai makaranta kika wuce" "A'a Inna bata nanne? "Eh, kinsan abunka da ƙaramar yar kasuwa, ta tafi saro kayyaki yanzu kayan suna saurin ƙarewa" Gyada kai Zarah tayi tana ajiye jakar hannunta sannan ta zauna kusa da Saude ta ce, "Saura wata nawa bikin? Ɗan bata rai Saude tayi tana fad'in " Dama jira nake ki dawo wai kinji Alhaji da neman fitina gida daya zan zauna da matarsa wai yana da wadatattun dakuna, zai ware min daya ayi min jere ni gaskiya bana so wallahi" "haka kika ce masa? Zarah ta tambayeta.. "a'a nace masa toh, amma banji daɗi ba, shikenan kayan kitchen ɗin da innata ta siya min munyi asara kenan? "Haƙuri zakiyi kuma ai da kayanki zaki tafi, waya ce miki da kayan girkinta zaki dinga amfani? "Duk da haka dai Aunty" Murmushi Zarah tayi tana riƙo hannunta ta ce, "Hakannan dai zakiyi hakuri tunda tun farko ke kika ce kina so, bani ruwa nasha" Ba yadda Saude ta iya haka ta tashi ta mayar da Alqur'anin sannan ta kawo mata ruwa.  Bayan Zarah tasha ruwan ta tashi ta shiga daki, bata dade ba ta fito ta wuce toilet.. ita dai Saude tana son mata magana akan halinta da Inna take fada amma tana fargabar abinda Zaran zata ce da ita.  Zara'u na kwance kusan magriba tana latsa wayarta Saude dake kusa da ita tayi karfin halin cewa " Aunty inaso muyi magana" sai da Zarah ta kalleta kafin ta ce, "Inajinki" Shuru Saude tayi dan bata ma san ta inda zata fara ba. "Ina sauraronki just feel free ni yayarki ce kinji ko? Gyada kai Saude tayi sannan ta ce " Dama akan ki ne da Yaya Mustapha, wallahi Inna bata jin dadin abinda kike yi, kuma Ummi ta kirata sun dade suna waya bansan dai me suka tattauna ba amma ga dukkan alamu innarmu bata ji dadi ba, kamar zatayi kuka, Aunty dan Allah ki manta da batun Ammar! Wallahi da ace Ammar yana sonki kamar yadda yake ikirarin toh bazai taɓa bari a rabaku ba! Ki rungume kaddararki, idan ma kyan Ammar ke rudarki ai Yaya Mustapha ya fishi, kawai fari Ammar zai nuna masa kuma Allah na tuba ai fari ba shine kyau ba, ta ko ina mijinki yayi sai dai san barka da ɗan abinda ba'a rasa ba! Kinata neman zabin Allah, Allah kuma ya zaba miki Yaya Mustapha amma kina misbehaving, This is unfair, Dan Allah Aunty ki gyara! "Barta! Kada Allah yasa ta gyara! Wanda beyi sharar masallaci ba ai zaiyi ta kasuwa wallahi Allah! Muna nan dake ba baki nake Miki ba Zara'u inhar bazaki bi mijinki ba toh wallahi kina tare da dakin wahala" Cewar Inna data Daɗe a bakin kofa tana jin maganganun Saude. Ita dai Zarah bata ce komai ba. "Tashi ga kaya chan a tsakar gida ki kai dakin zaure gobe a fito dasu idan Allah ya kaimu" Inna ta kuma faɗa tana kallon Saude. Da toh Saude ta amsa tana tashi ta fita daga dakin. "Sannu da zuwa inna! Banza Inna tayi mata tana cire hijabin jikinta. "Inna nace sannu da zuwa, baki ji ba? "Naji, banyi niyyar amsawa bane! Daga haka Inna ta fice. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya, tun bayan dawowarta daga ABUJA ko sau daya Mustapha be taba kiranta ba, a bakin Farida take ji wai yaje kasar waje yayi interview kuma yaci sunce zasu nemeshi.. Tsakaninta da Ammar kam babu abinda ya sauya, kullum shi zai kaita makaranta ya kuma daukota. Yanzu ta daina damuwa ma da sharewar da Inna take mata acewarta zata sakko ne idan ta gaji da fushi... Suna cikin shirin exams na 2nd semester ana shirin bikin Saude.. gaba daya abun ya haɗe mata, shiysa bata wani maida hankali akan bikin ba, duk abinda aka ce da ita toh ne kawai amsarta. Gyaran jikin sati biyu akayi wa saude, ta gyaru iya gyaruwa, bikin saura 5 days aka kawo akwatuna, maza ne kuma suka kawo chan gidan su Baffansu... 12box sarkar gold har biyu, masu Allah sanya alkhairi nayi masu gulma ma duk suna yi. Kwanan lefan biyu a gidan Baffa ya ce a kwashe su. 

MATANA ✓Место, где живут истории. Откройте их для себя