PAGE 8-9

16 2 0
                                    

*GARIN KALLON*💦
*RUWA*💧


✍️
*AISHA GALADIMA*


_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_


*DUBUN GAISUWA A GARE KU*

*HASSAN ATK*

*RUKAYYA I IKRA*

_Alkhairin Allah ya Kai gare ku har gadon bacci_

*PAGE 8-9*

________________________________


Takowa ya ke Yana nufo su ,duk da saurayin ya basa baya Ammah ita Billy Tana ganin sa ta gefen Ido, zuwa yayi kamar ze gifta ta gefen su ,se ya bi ta tsakiyar su Yana kawo wa tsakiya ya yarda kwalin turaren da ya dauka dukawar da zeyi garin dauka yasa kafa ya take Mata kafa da talkamin shi wani irin azaba taji ta ratsata ,Dan mugunta har da su murzawa Aiko ta saki Kara Tana Shirin faduwa , kasancewar hill shoe ne da ita ,saurayin na kokarin ya ga me ya same ta Yana Mika hannun sa ganin zata fadi , dama Aliyu na tsakiyar su ,ganin zata Fadi da gaske yasa ,ya taro ta da hannunsa ta fado ,shikam saurayi se cewa yake "me ya same ki pretty?" Ganin ta a jikin Aliyu hakan ba karamin Kona Masa Rai yayi ba, ita Kam billy matse fuska take saboda Azaba,Aliyu ji yayi kamar ya kwada Masa Mari gani yadda ya miko hannun sa da nufin riketa
Billy Jin ta fada jikin mutum ga wani tattausan kamshi me dadi yasa ta fara kokarin mikewa Tana rike gaban rigar tasa ,se ji tayi yace ke wane irin iskanci ne wanna Zaki wani kwanto min a jiki haka har kike kokarin ja min Riga ,tuni har hankalin wasu ya fara dawowa kansu,duk kunya da bakin ciki sun cika billy ganin yadda idon kowa ya dawo kansu duk da ta tashi a jikin nasa se wani yamutsa fuska yake Yana kallonta ,juyawa yayi gun saurayin da yayi tsaye Yana mamakin abunda Aliyu yayi ,billy wani banzan kallo take watsa Masa ita ma ta rasa me zata ce masa ganin rainin hankalin da yake neman mata, maida kallon sa yayi Akan saurayin yace"Kai Kuma kasan irin 'yan matan da kake kulawa,ka nemi masu tarbiya a gabanka dai kaga yadda ta nuna maitarta a fili a Kaina yayi tsaki ya wucewar sa ,mutane wasu har sun fara nuna billy ji tayi duk ta muzanta ba shiri ta fito daga jifatun gayen na biye da ita har suka fito ,Yana cewa " please kiyi hakuri" Dallah malam ka kyale ni nace ko Kai maye ne" ta fada cikin tsawa ta wucewarta Aliyu dake cikin mota duk Yana kallon abunda ya faru dariyarsa kawai yake a mota harda su buga staring a fili yace "gobe ma ki sake shigar banza ki fito" ,. su Amrah ne suka fito daga jifatun su duk wainar da ake toyawa Basu da labari ,se sayayyar su suke hankali kwance bayan sun gama ne suka neme sa suka rasa shiyasa suka fito waje su diba ko Yana Nan be tafiyar sa ba se suka ga motar sa a waje ,jidda tace" Allah ya taimake mu be tafi ba,yawwa Ina gift din da kika sawo Masa?"
Ga shi Nan cewar Amrah "to kiyi kokari ki basa Yana aje mu Zan fita da sauri ke Kuma se ki basa ,ki dai yi duk yadda na fadamiki fa" cewar jidda ,dai dai Nan sun kawo motar ko yanzu jidda ce ta zauna baya Amrah ta shiga gaba,suna shiga suka zauna tada motar yayi ya fara tafiya ,satar kallon sa Amrah tayi taga kamar fuskar sa a sake take, se ko ta saki murmushi Tana me Jin dadin yadda taga fuskar tasa ba kamar sadda suka fito ba suna Isa ko kamar yadda jidda tace ne ya faru Dan ficewarta tayi daga motar ta rufe ,juyowa yayi yaga ita Amrah me ya tsaida ta ne bata fita ba,se yaga ta dauko wata jaka me kyau karama daga cikin kayan da ta siya tace "Yaya ga naka" muryarta na rawa,kallonta yayi na seconds biyu yaga yadda duk a tsorace take,se yaji ta Dan basa tausayi karba yayi yace "Kanwa ta menene a ciki " Yana Diba jakar ,irin turaren da yake so ne ,take ya san cewar jidda ce ta shirya hakan,ya kudurta a ransa ze Bata mamaki kuwa Dan ya ga Alamar raini ya fara shiga tsakanin su,dagowa yayi karaf suka hada Ido da Amrah da ta kafe shi da Ido Tana son ganin yadda fuskar sa zata nuna,Amma bata gano komai ba,sauke idonta tayi a kasa gabanta na faduwa suna hada Ido ,kallonta yayi na 'yan dakiku yaji duk ta basa tausayi Dan ya dade da gano sonsa take Ammah ze samu lokaci ya fada mata ta bar wahalar da kanta ,cewa yayi "Nagode kanwata"
Murmushi kawai tayi ta fita daga motar, Tana fita yayi tsaki ya jefa ledar bayan motar sa ,ya tada motar ya fita
________________________________

Billy na fitowa daga jifatun ta nufi titi ta tare Adaidaita ta shige ji take kamar kafarta bazata dauke ta ba,Tana zama a ciki ta zare talkamin kafarta Tana me runtse idanunta ,a ranta se Allah ya Isa take ja ma malam Aliyu tare da alkawarin daukar fansa fiye da abunda ya Mata,ko Ina ruwansa da ita ma Dan shishigin bala'i ,da kyar ma idan ba karya Mata kafa ya so yi ba,Ammah wallahi bashi yaci Zan Rama ne mugun mutum kawai ,suna iso wa gida ta Ciro kudi ta bawa me napep ta fito a hankali da kyar take daga kafa ta nufi cikin gidan, Tana shiga mama tace"lafiya kuwa Naga kin cire talkami?"...... "Faduwa nayi mama " inalillahi wa'ina ilaihi rajiuuun cewar mama , tasowa tayi da sauri tazo ta riko Billy ganin da kyar take dago kafarta da har ta Dan fara kumbura"garin Yaya hakan ta faru shiyasa ban cika son kina saka Dogayen talkamin Nan ba ga shi yanzu kamar ma kinji ciwo ,rikota tayi a hankali suka shiga falo ta zaunar da ita Akan kujera Tana Mata sannu duk ta hada zufa , fita mama tayi ta dauko roba ta zubo ruwan zafi ta dauko karamin towel ta zo inda Billy ke zaune ta matso towel din daga cikin ruwa to Dora towel din a kafar,Kara billy ta saki Tana cewa"Dan Allah mama ki Bari bana so, Tana sauke ajiyar zuciya ,kallonta mama tayi tace"to jimuwa kikayi kuwa Bari na Kira Abban naku a turo me gyara a Diba kafar taki,ita dai billy matse fuska kawai take tana Jin zafi a kafar ,mama dauko wayarta tayi ta Kira Abbah ta fada Masa abunda ke faruwa,cewa yayi ze turo wani da mota ya kaisu wurin da ake gyara to tace Masa ta ajiye wayar matsowa tayi kusa da Billy Tana Mata sannu,daga Kai kawai tayi ,cikin ranta Tana tunanin kalan rashin mutuncin da zata ma malam Aliyu, ba a dau lokaci ba Wanda Abbah ya Aiko ya zo ,shiga daki mama tayi ta dauko hijabinta ta fito da wani ta saka ma billy kamata tayi suka fito a hankali suka shiga motar , cikin gari suka shigo har suka je wata unguwa ,mutumin ne ya fita yayi sallama a kofar wani gida ba'a dau lokaci ba wani magidanci ya fito Wanda Akallah zeyi shekara 45 bayan sun gaisa ne ya sanar Masa abunda ya kawo su,cewa yayi to kace su shigo ciki ,zuwa yayi Yama mama magana fitowa sukayi suka shiga cikin zauren ,zauren na shimfede da babbar tabarma kasancewar sa me Fadi zama suka yi, me gyara ya matso yace "wanna ce kafar naga tayi fushi ma kokarin taba kafar yake ,billy ta matsar da ita gefe,kallonta yayi yace " 'Yar Nan ki tsaya a dubaki Mana". Dan Allah Karka min da zafi, murmushi yayi yace a hankali Zan Miki. Kafar ya rike ta fasa kuwa Tana kokarin sa hannunta mama ta rike ta da kyau ,me gyara ya shiga aikinsa ,ba Karamar Azaba take ji ba har da su hawaye ,me gyaran se da ya lunde kafar sosai ,sannan ya dauko magani ya shafa tare da dauko kyalle ya daure kafar,zuwa lokacin Billy duk ta hada zufa ga hawaye na zubo mata tun Tana kuwa ta dawo kalmar shahada, bayan ya gama ne ya dago yace targade ne ta samu insha'Allah Nan da kwana biyu za'a iya warware daurin,Allah ya Bata lafiya,Amin mama tace ,sannan ta dauko kudi ta bashi ,mama ta rikata ta Mike se dai taki saukar da kafar kasa,mama tace" ki sauke kafar Mana mu karasa mota,kin saukewa tayi me gyaran ne yace"Bari nazo na Kara taba kafar, da sauri tace"Dan Allah ka kyale Ni Tana hawaye,ta sauke kafar ,dariya mama tayi ,haka shima me gyaran kafin yace ki dinga sauke kafar Mana ki na takawa ,in ba so kike nazo har gida na sake gyara ba

"To " tace, sallama suka masa suka fito suka nufi mota suka shiga...........✍️

*Aysha galadima ce*





Wannan littafin na kudi ne duk me bukatar ci gaba ,ze tura #300 a wannan account din 3118088470
Aisha Muhammad galadima first bank see turo shedar biya ta wannan number 08064933819 ko Kuma katin MTN na 300 a wannan number 08064933819

GARIN KALLON RUWATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang