GARIN KALLON RUWA PAGE 2

90 6 0
                                    

💦 *GARIN KALLON*💦
            *RUWA*💧

          

                ✍️
        *AISHA GALADIMA*
_
_Follow me on Wattpad# @Ayshagaladima666_


_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_


_No one in this world is pure and perfect if you avoid people for their little mistakes you will_ _always be alone ._ _So judge__




*Page 2*

________________________________

Suna shiga cikin hostel din Naga sun nufi wani daki, Fatima ce ta Ciro key a Jakarta ta bude dakin, kamar jira Billy take ta fada dakin da sauri Tana shiga hijab ta cire ta fada kan gadon dake kasa Tana fadar"waih"

Kara sa shigowa suka yi Khadija tace "Ahhh Billy ba dai ragwanta ba ,ke da tun safe lecture daya Kika yi kece ke kwanciya"

Daga kwancen ta ce Mata "waya fada Miki banyi karatu ba maths din da besty ya koya min fa "

Khadija tayi wani murmushin gefen Baki kafin tace "hmm Zaki gama iyayinki ne malama ki Fadi gaskiya besty ko sweetie dinki"

Tashi  zaune tayi ta kalli Khadija dake hada kayan miya zata dafa musu taliya tace"Wai ni kam so nawa zan fada Miki ba soyayya muke ba da Affan,Ammah ko yaushe se kice saurayi na ne" ta kare maganar Tana hararar Khadija

"Kya ji da shi dai , ammah ko wa ya kalli irin yadda kike sakewa da mutumin Nan ai dole ace soyayya kuke"
Cewar Khadija

"Kanki ake ji dai" tace tare da mikewa ta dauki buta ta fita dakin

Fatima da ta sauya kayanta ne ta matso Tana Taya Khadija girkin , kasancewar taliya ce suka dafa Nan take ko a ka gama girkin suka zubo ta a babban tire a tsakiyar dakin ,Da sauri Billy ta sauko suka zagaya suka fara ci se santi billy ke yi suna Mata dariya🤣

________________________________

Around 3:00pm malam Aliyu ya fito daga Office dinsa  Naga ya  nufi mota kirar Benz Ash colour ya shiga ya fita daga makarantar , A hankali yake tuki har ya Iso wata unguwa da'ake Kira Unguwar yarima ,wani katafaren gida Naga yayi horn Mai gadi ya wangale masa gate ya shiga, parking yayi ya fito gaisawa suka yi da me gadin Naga ya nufi cikin gidan da sallama ya shiga gidan wasu 'yan mata ne guda biyu a falon fuk farare ne kamar sa ,se dai dayar ko ba'a fada ma ba kasan kanwarsa ce saboda kamar da suke sosai, duk dago Kai sukayi suka ce "sannu da zuwa Yaya"

"Yawwa" yace musu
Ya ci gaba da tafiyar sa daga gefen hanyar kitchen akwai corridor tanan naga ya bi se ya bullo Dan fili ne kadan kamar baranda ya Sha tiles se kofar daki dake tsakiyar wurin ,kofar Naga ya bude ya shiga wow dakin ya hadu ba karya komai na ciki sky blue ne, kuryar dakin Naga ya shiga se na fito na dawo falon ,Aliyu na wucewa dayar ta bisa da Ido har ya bace ,dayar ta dafa ta tace " habah Amrah wannan kalon fa da aka bi Yaya na da shi fa" ta kare maganar Tana murmushi ,kallonta dayar tayi

sannan ta sauke ajiyar zuciya tace"jidda kin fi kowa sanin kallon da nake ma yayanki ,kulum da shi nake kwana nake tashi ,ban taba tunanin Zan fara son wani namiji ba,ke Ni a da ma cewa nake so karyane Ammah lokaci daya Allah ya Dora min son Yaya Haidar ,Wanda shi har yanzu Banga alamar ma yasan da halin da nake ciki ba" ta kare maganar kamar ta yi kuka

Dafa ta jidda tayi tace"ki kwantar da hankalinki insha'Allah ma baze ki ki ba, saboda kin hada Abubuwa da yawa da duk namijin da yayi Ido biyu da ke baze kushe ki ba,se dai Ban Baki shawarar tunkararsa da maganar ba Kodan kada ya ga rashin kunyarki da Kuma zubewar ajinki a wajansa ,Ammah dai yanzu ki bar komai a hannuna Zan San yadda Zan fara"

Murmushi ne ya subuce a fuskar Amrah ta rike hannun jidda tace "nagode darling sis"

Ita ma murmushin tayi tace"don't mention sis"

Daga Nan tashi sukayi suka nufi dakin su Suma.



Washe gari ta kama Wednesday ,tun Asuba su Khadija da Fatima suka tashi sukayi wanka

Ammah Billy Tana kwancen ta a gado kasancewar Bata sallah, se kusan 8:00am ta farka Koda ta tashi duk su Fatima sun wuce ,ganin har 8 tayi da sauri ta tashi ta shirya a gaggauce ta fice a dakin ,sauri kawai take kasancewar mutumin nata ke gare su ,tafe take tana tsaki cikin ranta

shima yau Malam Aliyu ya danyi lattin zuwa ,Yana akan hanyar sa ta zuwa ajin ,suka buga wani irin karo da Billy ji kake kum kanta ya daki kirjinsa ,wani irin shock suka ji shi da ita ,duk takaddun da ya riko a hannunsa suka zube a kasa tare da iPad dinsa

Da sauri ita ma ta ja da baya Tana taba kanta saboda ba karamin buguwa yayi ba a kirjinsa , kallonta ya ke daga sama har kasa kafin yace"ke makauniyar ina ce da Baki kallon gabanki iyeeh" ya fada cikin tsawa ,gunguni ta fara kasa kasa tace Kaine makaho,be ji mi tace ba Ammah yaji gunguninta

Tsaki yayi yace "kwashe min kayana ki biyo ni"

Wucewa yayi ya barta a Nan ya shige ajin da ze masu karatu

Harara ta bi bayansa da ita kafin ta ce"Allah ya saka min mugu kawai"

Dukawa tayi ta fara tsince kayan har ipad din ta fashe,sannan ta nufi class din Tana kara hade Rai ,Tana shigowa idanu suka koma kanta nufar inda yake tsaye tayi ta aje kayan akan dogon table dinnan na tsaye da lecturer ke tsayawa ta aje kayan ,ko kallon sa taki yi , shi se mamakin karfin halinta ya ke
sannan ta juyo ta nufi wurin zama



"get out of my class" ta tsinkayo muryar sa

Juyowa tayi ma Tana murmushi ta nufi hanyar fita se da ta kawo daf da shi tace"daga an hutar da mutum da zama, a cika Masa kunne" 

Sarai ya ji me tace ,se Jin ta yi Kuma yace"go back to your sit"kamar ta ficewar ta se dai Kuma ta dawo ta nufi inda take zama ta zauna 'yan class se kus kus suke kasa kasa

Lecture din sa ya ci gaba dayi billy ko dago Kai Bata yi ba ballantana ta maida hankali Kan abinda yake koyarwa yana gamawa kuwa yace test ze yi

Ai ko Ido ya Rena fata Dan maths ne yake yi Kuma Bata maida hankali ga lecture din ba ballantana ta fahimci calculation din,duk Yana lura da ita ,se cewa yayi cikin ransa  ga tsoro ga rashin kunya

15minutes test ya musu ,ita dai tayi Wanda zata iya ta bar saura ..................✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

GARIN KALLON RUWAWhere stories live. Discover now