GARIN KALLON RUWA PAGE 6-7

109 9 0
                                    

💦 *GARIN KALLON*💦
*RUWA*💧


✍️
*AISHA GALADIMA*

Follow me on #wattpad@ Ayshagaladima666



_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_

*PAGE 6-7*

________________________________

Dariya billy tayi tace"habah mamanmu to mi kika yi yau?"

Mama shigewa falo tayi ta barta Nan tsaye

Dole ta dauki Jakarta da ta yarda ta bi bayanta
Tana shiga falon dakinta ta fara shiga ta aje jakar Jin ana Kiran sallar magrib yasa ta Mike taje ta dauro Alwala
Ta yi sallar maghrib

Bayan ta gama ne ta fito ta gaida mama , sannan ta je ta zubo abincin ta zo falo ta zauna kasa ma ta zauna Tana cin abincin

Suna firar su da mama har Abbah ya dawo

Ai ko cikin farin ciki ta shiga yi Masa sannu da zuwa , ya Amsa ta cikin jin dadin ganinta

Kafin yace "an zo muna weekend ne my daughter "

"Eh Abbah"

To ya karatun naki da fatan dai ana maida hankali ko?

"Eh Abbah"

" to Allah ya taimaka"

"Amin" tace ta tashi ta dauki plate din da ta gama cin Abinci

Ta nufi kitchen ta ajiye

Dawowa tayi ta zauna falon suka Dan taba Hira da Abbah ,mama na zaune gefe Tana Dan saka musu Baki

"Yawwa Na manta na fada Miki kawarki ta zo har gidannan ta kawo Miki invitation din bikinta "
Cewar mama

Dagowa tayi tace "mama wace kawata a ciki?"

"Safina"

"Lah ai ko mantawa nayi har ankon ta tura min ta WhatsApp Kuma wani sati ake bikin "

Abbah yace"nawane Ankon?"

Tace 5000 ne

Kudi ya Ciro 10k ya Bata yace "to gashi har na dinki ,gobe se kije ki sayo"

"Nagode sosai Abbah na Allah ya saka da Alkhairi ya Kara budi"

"Amin ,Nima Allah ya nuna min aurenki"

rufe fuska tayi da hannunta Tana murmushi ,Tana me Jin kunyar Abbah

Dariya Abbah yayi yace duk kunyarce haka bilkisu na ,ya fada cikin zolaya da sauri ta tashi ta nufi dakinta ,se da takai kofa tace"se da safe"

Duk dariya sukayi mama da Abbah ganin abun da tayi

Nan Abbah yayi gyaran murya ,mama ta maida hankalinta kansa Dan ta San duk yayi hakan to magana me muhimmanci ze yi da ita

" Tafiyar da nayi zuwa karakai, baba yayi min korafi akan lallai ama balkisu aure,duk da naso ace ta kammala NCE dinnan kafin tayi aure Ammah yace da ta samu me so a Mata aure,kinsan bazan iya musanta maganar sa ba, shiyasa Naga ya Dace na fada Miki tun da ke mahaifiyar ta ce ,sannan Ina so cikin hikima ki tambaye ta Wanda take kulawa a yanzu in har da gaske yake ya turo"
Cewar Abbah

Ajiyar zuciya mama ta sauke ,sannan tace " Alhamdulillah Ni hakan da baba yace ya min dama auren shi yafi dacewa da ita, Allah ubangiji ya sa hakan shi yafi zama Alkhairi"

Amin Abbah yace

"insha'Allah Zan Mata maganar gobe" cewar Mama

Murmushi Abbah ke tayi Yana kallon mama kafin yace "Nagode ma Allah da ya bani Mata kamarki wadda duk lokacin da nazo da magana take karbarta hannu bibbiyu"

GARIN KALLON RUWAWhere stories live. Discover now