GARIN KALLON RUWA page 4-5

78 6 1
                                    

💦 *GARIN KALLON*💦
            *RUWA*💧

          

                ✍️
        *AISHA GALADIMA*

__Follow me on #wattpad@Ayshagaladima666_





_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_



*Happy Anniversary dear*

_@ Aysha Bashir galadima, may Allah bless ur union now and forever_

*Allah ya raya muna*

_Waleed nura_ _wambai_

_Khadija nura wambai_









*Page 4-5*


________________________________

Tafe take ahankali ta nufi hanyar fitowa da ga makarantar, Tana fitowa titi ta nufa ta tsaya a gefen titin Tana kallon gefen ta na dama, Tana kallon motocin dake wucewa , Adaidaita take jira ta samu Ammah shiru har yanzu ba giftawar ko daya ga yamma tayi
Wata mota ce har tagifta  ta se kuma aka yo baya da motar ,ganin motar ta tsaya ta gabanta ya sa ta mata kallo daya ta dauke Kai Tana Shirin matsawa taji kamshin wani turare me dadin gaske ya daki hancinta tare Kuma da wata zazzakar murya ta Mata sallama da kamar ta share ,se Kuma ta Amsa
Mutumin ne ya ci gaba da cewa"be kamata kyakyawa kamarki ba ta tsaya anan jiran abun Hawa ba bayan dirobi irin mu Na nan ,ki taimaka ranki ya dade ki shiga na karasa dake gida"

Dago wa tayi ta kalle sa daga sama har kasa ,ba makusa a jikinsa ko kadan ,daga ganin sa ma zaka San mutum ne Wanda Allah ya rufa Masa Asiri , Dan black beauty da shi dogo ,Yana sanye da wata shadda gizner milk colour wadda daga gani ansan naira tayi kuka wurin sayenta ,gani tai kamar Yana Mata kama da wata fuska amma fuskar ta kwanta mata

"Am bawan Allah nagode" tace tare da yin gaba  ta tare wani me adaidaita Yana tsayawa kuwa ta shige Bata tsaya saurarar sa ba

Tana shiga ta fada Masa inda ze kaita

Me motar komawa yayi ya shiga motar sa shima ya biyo bayan me Adaidaitan

******************

"Ummee sannu da zuwa"
Cewar  jidda

Wata kyakyawar Mata ce ta shigo gidan sanye da hijab Tana rike da hand bag dinta ,daga Ni ta dawo daga wani wurin ne , Tana matukar kama da Aliyu sosai ,duk da jidda na kama da ita Ammah Bata Kai kamar Aliyu ba da komai nata ya dauko

"Yawwa jidda ya gidan"
Cewar ummee,Yana ganki ke daya Ina Amrah take?"

"Yanzu ta shiga daki"

"Ok"
Ummee tace sannan ta nufi kafar bene zuwa sama

Ita ma jidda mikewa tayi ta shiga dakinta da Amrah ke ciki

Kwance ta iskota Tana kallo a laptop
Cewa tayi  "Wai ni Kam ba Kya gajiya da kallon Indian series?"

Dagowa tayi ta kalle ta take"hmm ba Zaki gane ba Dan dai ba Kya kallon ne shiyasa "
 
Jidda cewa tayi"yawwa ummee ta dawo fa kina Nan kina kallo "

Dirowa Amrah tayi daga Kan gadon tace "Ammah dai Baki kyauta min ba shine Baki kirani nazo mu gaisa ba "

Rike Baki Jidda tayi Tana kallon ta kafin tace "wanna duk zumudin gaida uwar miji ne kike haka, ahh lallai na hadu da surukar zamani "

Hannu ta daga zata dake ta da sauri ta goce ta shige bathroom ta rufe Tana Mata dariya

Ita ma Amrah dariyar take tana me Jin dadin furucin da jidda tayi ji take Ina ma ace ayi auran na su Nan kusa

Arwala ta dauro Dan maghrib tayi ta fito ita ma Amrah mikewa tayi ta shiga bathroom Dan dauro arwalar

Bayan sun gama sallah fitowa suka yi falon Nan suka ga har ummee ta sauko , da fari'arta tace "Amratu kinzo Baki tarar da Ni ba ko"

"Eh ummee Ina wuni ya gida har da su dukawa tayi ,jidda Kam boye dariyar ta take tayi har ta fito fili, dakuwa ummee ta mata tace" miye abun dariya a Nan

ko Dan Kinga ta duka ai haka ake gaida manya se ki gyara yadda kike gaida manya Dan na San a tsatsaye kike gaida mutane"

Fakar idon ummee Amrah tayi Tama jidda gwalo

Bayan sun gaisa ne Nan ummee ke tambayar Amrah mutanen gidansu tace duk suna lafiya

Suna Nan zaune har aka Kira isha'i sallah duk suka tashi suka gabatar

Zuwa 8:30pm ummee tace ma Jidda "je ki Kira yayanku ya fito ayi dinner"

Mikewa tayi ta nufi hanyar dakinsa knocking tayi taji shiru ,se ana ukku ya zo ya bude Tana ganinsa tace"Yaya kazo ayi dinner"

"Ok"
Kawai ya ce

Ta juya ta koma

Dakin sa ya koma , wardrobe ya bude ya dauko wata gogaggiyar jallabiyya fara ya saka,se da ya Dan fesa turare sannan ya fito

Koda ya shigo falon duk sun zauna akan dinning shima nufar dinning din yayi

Gaida ummee yayi ,sannan ya gaida Abbu

Neman kujera yayi ya zauna ,abincin Jidda ta zuba kowa

.daga Nan dinning din ya dau shiru kowa naba cikinsa hakkinsa

Se dai Amrah Bata da sukuni kasancewar kujerar data zauna Tana kallon ta Yaya haidar ,se satar kallonsa take duk ta kasa cin abincin A nutse ,jidda data kula da halin da ta shiga se zungurarta tayi da kafa Dan kusa suke zaune

Wannan karon Kam Tana dago Kai suka hada Ido ,dama tun dazu ya kula da irin kallon da take masa

Suna hada Ido da sauri ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa

Mikewa yayi yama iyayen nasa seda safe ya wuce dakin sa

______________________________

Me adaita na aje ta ta bashi kudinsa ta tura gate din gidan nasu ta shige

Da sallama ta shigo ta na kwala Kiran "mamah  mamah!!

Da sauri mama ta fito daga falon na su ,da gudu ta ruga ta rungumeta tamkar wata yarinya

Ita ma mama tayi kewar 'yar tata shiyasa ma Bata ce komai ba se murmushi da take yi kafin ta dago ta daga cikin jikin ta tace"habah me gadon zinari har yanzu dama Baki bar wannan kurciyar ba,Zaki zo da gudunki ki wani rungume Ni,yanzu da yaron Na Nan fa "

Tana nufin Yaya Sadiq Dan Bata fadar sunansa saboda kunyar Dan fari

Turo Baki gaba tayi kafin tace"mama na fayi kewarki ne"

"To ai se kiyi murnar hankali Mana Baki gudun ki Fadi kiji ciwo"
 
Murmushi billy tayi tace "to na Dena ,me kika girka muna yau mama, Allah yasa danbu kikayi"

"Bashi nayi ba ja'ira .....  .... ✍️

*Aysha galadima ce*


Vote
Comment
Share

GARIN KALLON RUWAWhere stories live. Discover now