GARIN KALLON RUWA PAGE 3

68 8 0
                                    

💦 *GARIN KALLON*💦
            *RUWA*💧

          

                ✍️
        *AISHA GALADIMA*






_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_

__The greatest lesson you can teach your self is to be patient_

__Be patient when you're happy because happiness ends,_
_and Be patient_  _when you're sad because sadness too ends__

__Nothing is constant everything is temporary, except ALLAH the eternal_ , the everlasting



*Page 3*


_______________________________

Tana fitowa daga ajin anan harabar department din su na maths/computer taga Affan ,shima Yana hangota ya taso  Yana zuwa suka sakar wa juna murmushi karaf idanunta suka hadu Dana malam Aliyu wani mugun kallo ya watsa mata, ita ma hararsa ta yi ta juya ta ci gaba da kallon Affan gaisawa sukayi yace "ya lecture din"

"Hmm lecture ko mugunta daga shigar mu aka muna test din daukar Alhaki"

Karaf a kunnen malam Aliyu da yazo giftawa ta kusa da su

Wucewarsa yayi a wurin ya barsu

"Habah bestie wace mugunta Kuma ai gara a dinga muku test din ze fi ko"
Cewar Affan

"Naji abar maganar to ya kake ya lectures Dinka ?"

"Alhamdulillah dear"

Yace Yana murmushin sa me Kara masa kyau

"Yawwa bestie na kusa barin makarantar Nan fa kin San final exam din mu kara matsowa take yi"
Cewar Affan

Nan take fuskar billy ta canza, neman wuri sukayi suka zauna kafin tace"Ni fa har bana son na tuna zaka bar makarantar Nan fa " ta fada Tana me kallon sa ,fuska dauke da damuwa

" na San Dana tafi mantawa Dani  zakiyi  kiyi auren ki kibar Ni"

Ya fada Yana kallon ta

" Idan na manta da Kai Ashe Zan  iya mantawa da Kaina,So nawa Affan nake fada ma Ni ba zancen Aure a zuciya ta yanzu,karatu nake son nayi ,kaga yanzu Dana gama NCE , degree nake son na cigaba da yi
Kafin nayi Aure,  "

Shiru yayi Yana kallonta, yana sauke wata boyayyar ajiyar zuciya ,zuciyarsa na bugawa Yana binta da wani sanyayyan kalon 

Jin shiru yasa ta dago Kai ta kalle sa da sauri ya dauke kansa

Kallon sa tayi taga duk yanayin sa ya canza,take gabanta ya Fadi kar dai ace zancen Khadija gaskiya ne fa, A'a in gaskiya ne ai da ze fadamin ne wata zuciyar tace mata da sauri ta kawar da tunanin tace "kayi shiru besty"

Boyayyiyar Ajiyar zuciya ya sauke kafin  yace "Ahh ba komai hakan ma na da kyau Bari naje Ina da lecture yanzu"

Tashi yayi ita ma ta Mike ta masa sallama tace" Nima Ina son naje gida week end"

Cewa yayi" An yi kewar su mama ko?" Yana murmushi

"Eh Mana ai nayi kokarin zama hostel ma bayan muna gari daya "

"Haka ne fa to ki gaida min da ita insha'Allah Zan kawo Miki ziyara ,Dan ba Zan jure rashin ganinki ba har na kwana biyu"

"To yayi se ka zo"

Sallama suka yi ta wuce hostel shima ya wucewar sa, Koda taje hostel Bata isko su Fatima ba

Jaka ta dauko ta dauki wasu kayan Amfaninta, sannan ta fito ta rufe dakin a hanya ta hadu da su ta masu sallama se tsokanarta suke sannan ta wuce.

_______________________________

Bilkisu  Ahmad sambo shine cikakken sunanta ,mahaifin ta mutumin wani kauye ne da ake Kira karakai, su biyu ne ga mahaifin su Hafsa ita ce babba sannan Ahmad da suke Kiran sa sambo , mahaifiyar su Ahmad Kuwa ta dade da rasuwa, se malam Abubakar baban su da kenan, cikakken malamin Addini ne a garin na karakai, Dan har Almajirai yake dasu wadanda yake karantarwa Ilimin Addini


Ya ba yaran nasa tarbiya me kyau, tun bayan rasuwar mahaifiyar su Ahmad malam ya dade be yi aure ba se daga baya ya samu wata Halima da mijinta ya rasu ya aura, ita ma Tana da kirki sosai Dan Bata dauke su a matsayin 'ya'yan miji ba ta dauke su a matsayin 'ya'yanta ne

Hafsa kasancewarta mace se girma yazo Mata a lokaci daya, ba jimawa kuwa malam ya aurar da ita ga wani Dan Amininsa da ke gusau , aka Sha biki aka kaita gidanta

Kasancewar mijin hafsa Yana da rufin  Asiri sosai yasa taji sha'awar Dan uwanta ya dawo kusa da ita , da ta fadama mijinta da kansa ko yaje ya roki malam da kyar ya amince Masa kuwa

Gaba daya zaman Ahmad ya koma gusau ,makaranta me kyau aka sashi yayi karatunsa cikin dinbin nasarori, har yaje, Usman danfodiyo University ya karanci Engineering  ya kammala ya dawo

A lokacin Anty Hafsa Tana da 'ya'ya kusan uku ,na farkon shine Bashir se Abubakar da Kuma Khadija

Bayan ya dawo ne ya hadu da Aisha wadda lokaci daya yaji ta kwanta Masa a Rai ,iyayanta a cikin gusau suke se dai talakawa ne sosai, ba'adau lokaci ba kuwa Akayi bikin su Amarya ta tare

Shekara na zagayowa ta haifi Da namiji me kama da mahaifinsa sosai ranar suna na zagayowa ya ci sunan kakansa wato Abubakar Sadiq ,suna kiransa da Amir

Akwana a tashi ba wuya wurin Allah ,Abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda samun aiki me kyau da Ahmad sambo yayi , yayi ginin sabon gidansa me kyau  Anan  Wata sabuwar unguwa da ake gada biyu  ,Nan ya nemi Malam Abubakar da ya baro karakai yazo ya zauna da su Ammah fafur yaki ya yarda ,hakura yayi  ya  komawar sa shi daya 

Aisha tun bayan haihuwar Sadiq ,se haihuwar ta tsaya Mata se bayan shekara bakwai sannan ta sake haifo kyakyawar 'yar ta Ranar suna yarinya taci suna bilkisu, Haka yayanta Sadiq ya ta jin dadi yayi kanwa se ji da ita yake kamar kwai ,haka ma sauran yayyunta 'ya'yan Anty Hafsa kowa se son yarinyar yake

A haka ta taso 'yar gata se dai bilkisu tun Tana yarinya ta ke da tsiwa ,ba ta da tsokana Ammah Bata daukar raini ko kadan ko a makaranta duk wadda ta shigo gonar ta Bata raga mats

Tun mama na fada har ta Bari se dai tace "Allah ya shirya min ke"

Yaya Sadiq kuwa tun Yana dukanta har baban su ya Hana sa dukanta ,Ammah duk da haka shi Yaya Sadiq Tana shakkar sa

Tayi primary school dinta a Ansar-ud-deen Nursery and primary school, tazo tayi secondary school a Muslim student society Academy

Yaya Sadiq shima ya gama karatun sa yanzu haka aiki yake pilot ne be cika zama a gida sosai ba

Fatima da Khadija kuwa kawayen ta ne Suma duk cikin garin gusau suke kusan tare suka taso,akwai shakuwa  sosai a tsakanin su

Da farko da ABU zariya suka so su tafi bayan sun gama secondary school Ammah iyayen nasu suka ce su tsaya suyi FCET In da suke ganin su da Kuma kula da tarbiyar su wannan kenan.................✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

GARIN KALLON RUWAWhere stories live. Discover now