chapter 1, The beginning

271 10 0
                                    

Chapter: 1 { The beginning}

Gida ne na siminti amma ba'a filasteshi ba bulalukan ma da gani sunga duniya dan duk sun tsufa har sun faraa kalar baqi dakuna biyu ne sai varender da d'an qaramin kitchen gefe sai toilet da rijiya a tsakar gidan.
Walida jeki taso min ita nagaji da wannan iskancin haka da gudu wata qaramar yarinyar da bazata wuce 3-4yrs bah ta qarasa d'ayan dakin "yaya Ihdat yaya Ihdat mommy tace kizo
Wacce ta Kira da Ihdat yarinya ce yar kimanin 17yrs Fara ce ba can ba kyakykyawa ta ajin qarshe daga ganin cikar gashin girar ta da yalwataccen sajenta kawai zai gaya maka cewar tanada yalwar gashin kai, da dimple d'inta d'aya a gefen hagun fuskar ta, ta juyo ta dubi walida sannan ta tashi suka fita tsakar gidan
Mommy gani tafada while sitting on the mat da mommyn ke zaune
Mommy ta kalleta tace Ihdat wai meye damuwar ki na gaya miki ki fawwalawa Ubangiji komi kinqi har yau is almost 7months fah amma har yau kuka kike koh Ihdat?
aah mommy am not crying kaina ne ke ciwo dazun amma yadaina yanzun
Kin tabbata
Eh mommy yadaina ,, toh ga abincin ki can ki dauko kici maza kar ku makara
Mommy nima zanci cewar walida
Hararanta mommy tayi
Ihdat tayi murmushi tace je ki dauko muci tare dagudu ta dauko abincin a wani plate din roba ta kawo loma uku Ihdat tayi ta tsame hannun ta
Yaya Ihdat kin qoshi eh na qoshi kici
Wai walida ba yanzun kikaci abinci bah
Mommy ay d'an fii neh kuma ban qoshi bah
Whatever nidai kiyi sauri kar muyi latti Ihdat da tagama alwula take fad'a lokacin da zata shiga daki.
Sun fito don zuwa islamiya dake nan cikin unguwar walida sai surutu take mata wani ta ansa ta wani ta mata banza
Lah ya Ihdat kinga andawo gidan kyau kuma turawa ne ma gashi ana shiga da kayan su shikenan mun zama turawa's neighbors banza Ihdat ta mata kuma bata daga kanta bah saima qara sunkuyar da shi datayi
5:30pm suka dawo gida walida sai labarin turawan gidan kyau take bah mommy lols, Ihdat kuwa zama tayi without saying anything tun gaida mommy da tayi bata qara cewa komai ba har aka kira magrib tana jin walida na bada labari amma tayi shiru tashi tayi ta dauro alwula tashiga d'akin ta ta tada sallah bayan ta gama tayi azkar dinta tana kan daddumar har aka kira Isha ta tashi ta gabatar da sallar kafin tayi adduoi ta shafa anan ta kwanta a takure
Tashin ta ake daga nauyayen baccin da kwashe ta gefen latsumammar katifar dakin bayan ta kammalla azkar dinta bayan sallar subh, bude ido tayi ahankali takai dubanta ga agogon dakin 10:12 am  zaro ido tayi duk d'aukar ta mommy ce kuma for sure fad'a mommy zata mata tajuyo eyyyah mommy..... Wata yarinya tagani wacce ta d'an girme ta amma baza muce ta wuce sa'artaba Fara ce sosai baturiya tanada da kyanta MashaAllah
Hey am sabyan we are new here I don't know anywhere and I want to buy pad pls sister will u help me and take me where to get it ta fad'a da murmushi a fuskar ta
Walida tace ya Ihdat sune wannan na gidan kyau
Ihdat ta Harare ta tace did I asked you?
Turo baki tayi sabyan na dariya tace come on friend ki qyale Ihdat kinsan in mutum ya tashi daga bacci ya cika zuciya
Murmushi kurum Ihdat tayi tana miqewa tace toh in ba damuwa Zaki jira ni inyi wanka
Kice shiyasa naji warin datti a dakin ashe baki wanka bah shiyasa dakin wari zo muje kar tasa Mana warin taja hannun waleeda suka fita, yanzun kam dariya Ihdat tayi sosai wai qarfin hali wannan wacece ne haka faram faram da ita itama tayi waje ruwa ta jawo a rijiya tana jiyo dariyar su cikin dakin mommy  tawuce toilet tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar yadi dukda bame tsada bane amma tayi kyau sannan tasa hijab har qasa tafito dakin mommy taje ta sunkuya tana gaida mommy
An tashi lafiya mommy
Lafiya qlw Ihdat y kan
Ya daina ay mommy
Ok Allah qara sauki
Ameenn tace tana murza y'an yatsunta
Sabyan ta tashi tace muje tafita
Kallon mommy tayi da alamar inje!?
Eh kije but pray before going out
Ok mommy sai mun dawo
Allah ya dawo daku lafiya
Yaya Ihdat kin min tsaraba
Hmmm tace tana fita daga gidan
Sabyan tagani tsaye kusada wata hadadan mota, yawwa muje ko ta bude tashiga itama shigar tayi
Ina ne za'a kaimu!!
Shiru tayi kad'an can tace HALAL MALL drivern dayake d'an garine yasan wurin tafiyar mintunan da basu wuce goma ba takai su can
Ihdat dai na tsaye tana kallon yanda sabyan ke kwasan kaya kamar ba gobe dogwayen riguna undes pads kayan kwalliya aranta tace kud'i masu gidan rana sun share kusan awa d'aya anan daga qarshe chocolates tasiya suka wuce mota Ihdat na taya ta kwasan kaya tace tana son siyan waya gashi Ihdat ma bata sani ba  koh nan d'in ma a bakin y'an class dinsu na islamiya taji wai sabon mall ne ya hadu sosai toh da batasan ina zasuje bah drivern yace muje in kaiku Hajiya don ya fahimci cewa Ihdat batasan wuri ba
iphone 11xpro tasiya da sim card suka wuce a mota sai zuba sabyan kema Ihdat ita dai nata murmushi
Tace Allah banason wannan shegen smiling d'in ki buda baki muyi fira in zakiyi, wait kodai bakisona friend ne?  Tafada tana maida duban ta da hankalin ta kan Ihdat
aah ina sonki kawai dai am...
Yawwa koke fah bari naje gida na fad'i ma Mahna da Yaya
Bayan sun iso gida taga driver na qoqarin shiga gidan kyau tace aah yatsaya ta sauka sabyan tace baza ki gaida Mah na ba!?
Zanzo wataran in gaishe ta worry not dear saby murmushi sabyan tayi cikin jin dad'in dear saby da Ihdat ta kira ta dashi tace toh ga wannan ki kaima waleeda tace aah mun gode
Haba Ihdat bafa ke nace ba waleeda nace ta karba tareda fad'in ta gode sannan tawuce gida daga gidan su sabyan sai nasu amma dayake gidan babbane sosai shiyasa akwai tafiya tsakani sosai
Sallama tayi ta shiga gida yanayin da ta iske mommynta da waleeda kad'ai ya isa kasan yunwa na dawainiya dasu qarasawa tayi tace mommy na dawo
Lumshe ido mommyn tayi tana hamdala a ranta tace toh sannu
Tab'a mommy ledar da akace taba waleeda
Ya Ihdat tsaraba nane?
Eh tace tanayi wurin randan su na ruwa da yay shegen sanyi ta diba ta sha
Da murna waleeda ta zazzage ledan chocolates ne da biscuits lah Yaya Ihdat Kinga wannan irin wanda Yaya ke siya mana
Eh nagani kici... Yaya Ihdat ke bazakici bah
Eh innaci zai samin ciwon kai
Tana murna ta fara cin chocolate d'in......

MAIDEN {A girl servant}Where stories live. Discover now