chapter 2

99 1 2
                                    

Nagode sosai thanks alot Mah Allah y qara girma da tsawon rai
Ameenn
Sabyan ki kaita wurin Nanny toh Mah ta tashi taja hannun Ihdat zuwa kitchen wurin Nanny tace wallahi let me make this clear to you in Kika ce Zaki canja min Allah zamu samu gagarumar matsalar da alqalin da zai sauraremu ma ba'a haifosa ba tohm
Dariya Ihdat tayi tace easy mam easy
Tace kingan abinda nake magana akai ko ba mam ba wallah mamo u work for my bro ni wannan ba matsala na bane that doesn't mean keba abokiyata bace, ina damuwa da banda abokiya amma yanzu nasamu
Ihdat tayi murmushi lokacin suna shiga cikin kitchen d'in
Nanny ga qawata wacce zata na yiwa Yaya abinci da gyaran part d'insa
Nanny ta dubi Ihdat da murmushi a fuskar ta tace madallah sannu y'ar nan
Sunkuyar da kai tayi qasa tana gaida Nanny ta amsa da fara'a sabyan ta dauko plate  tace nanny kizuba mana nida Ihdat sake baki Ihdat tayi tana kallon ta abincin da ke kan gas shi za'a zuba miki
Nanny tayi dariya tace ay yanzun ma zan sauke ta amshi plate d'in ta zuba musu shinkafa ne jallof da yaji kayan lambu da kifi yayi kyau ga qamshi sai tashi yake matsowa sabyan tayi kusada Ihdat tace toh malama sa hannu kuma bazan yarda da bazakiciba
Shiru Ihdat tayi tana tunanin taci ko kar taci  tana jin yunwa sosai amma yanzu in taci Mommynta da waleeda fa su me zasuci she can't stand to see them in hunger while ita ta qoshi ta bude baki zata ce aah sai sabyan tarigata tace nanny kisamin wani a cooler waleeda have to taste this yayi dad'i sosai idan mun gama sai in kai mata da sauri Ihdat ta kalleta idanunta duk sun ciko da hawaye murmushi sabyan tayi tace Allah yayi dad'i ci kiji ta diba qaton loma takai mata a baki dariya Ihdat tayi haka sukaci abincin har suka gama
Yanda sabyan taga waleeda nacin abincin kad'ai ya sanar da ita halin da suke ciki sallama ta musu ta koma gida tana shiga falon ta fad'a kan Mah tana kuka taba Mah labarin halin da tagane su Ihdat na ciki ta roqi Mah da ta taimaka musu
Mah taji tausayin su qwarai tace  toh kiyi shiru je ki kiramin malam idi tashi tayi ta Kira shi ATM mah ta bashi tare da yimai baya nin kayan da zai siyo mata ya amsa ya fita

Suna zaune Mommy na gyara wa Ihdat gashin ta sai kaya sukaga ana shigowa dasu indomie buhuhunan shinkafa kayan tea jarkan man Ja da man kuli oats cornflakes katon d'in taliya da dai sauran su
Lafiya kuwa bayin Allah mommy tace da yaran dake shigowa da kayan
Hajiya cewa akayi mu kawo nan
Kai Amadu waya saku?
Kafin ya amsata saiga sabyan ta shigo tace daman Mah ne tace sukawo na fara aykin Ihdat taqarasa kusada Ihdat ta bata wani envelope tace gashi inji Mah karba tayi jikin ta yayi sanyi tace kimin godiya sabyan amma kayan ko basuyi yawa bah!?
Mommy tace yawan ma kam maza sa hijabin ki kije kice mata sunyi yawa
Sabyan tace mommyna dan Allah Mah bazataji dad'i bah after all wannan na aykin ta ne please Mommy taqarashe maganar tana turo baki murmushi Mommy tayi tace toh angode Allah y qara bud'i
Ihdat taje tayiwa Mah godiya tace ba komai ay haqqinta ne

Haka taci gaba da zuwa aykin ta though Wanda zatama aykin bai dawobah abotar su da sabyan ta qara qarfi wani lokacin tana bata labarin Yayan ta itama sai ta rinqa tunawa da nata Yayan
Tana son sabyan matuqa dan bata dauki rayuwar da zafi ba duba da yanda take sata a jikin ta bata qyanqyaminsu kasancewar su talakawa yanzu ay da wasu ne da ko gefen gidansu bazasu kalla bah unlike her da har baccin rana take a can taci abincin su
Yanzun ma atare suke dakin sabyan tana bata labarin Yayan ta he is so handsome dukda namiji ne but he is so beautiful kefa kar yazo ingan akasin haka.... Allah ba wasa nake miki ba , who is the handsome man you ever know?.... Ihdat tayi alamar tunani kafin tace hmmm Abbanah.... sabyan tace you idiot bada iyaye ba
Dariya Ihdat tayi tace toh Yayana ....oh no sabyan tafadi tana sa hannun ta saman goshi 🤦 you idiot exclude the relatives mtssw mu daina ma maganar....🖋️🖋️🖋️

♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦

Tafito daga gida zuwa wurin aykin ta tun a wajen gidan taga securities Toh yau kuma baqi zasuyine ta tambayi zuciyar ta dan ganin securities d'in cikin gidan ma sun qara yawa kowannen su sanye da kayan sojoji riqe da bindiga sai zarya suke a compound d'in gidan taqarasa kusada mai gadin gidan tace sannu baba yawwa sannu hidatu tace wai baba shugaban qasa ne zaizo ko kuwa naga duk an qara cika gidan da masu baqin rai
dariya yayi yace aa nima dazun ne naji suna qus qus din yaron gidan zai dawo
Ohh I see toh baba nagode sai anjima tawuce cikin gidan tana fad'in toh shi kuma don zai dawo shi zaisa a cika gida da wad'annan mutanen da basuda kyan kallo kitchen ta wuce direct dan ba kowa a falon a can taga har masu ayki ma ankaro wai duk kan mutum d'aya
Y safiya Nanny
Lfy Alhmdllh Ihdat Kinga mu munata ayki ko Yayan sabyan ne zai dawo shiyasa
Kusan abinci kala biyar taga suna yi ta sauke ajiyr zuciya haka kawai saitaji gaban ta na faduwa
Toh ni me zanyi Nanny?
Kan Nanny tayi magana sabyan tashigo tace da Ihdat zo muje Mah tace in tayaki gyaran part d'in Yaya
Ta cikin falon suka shiga wata qofar dazakayi tunanin wani dakin ne amma saitaga glass stairway ne har zuwa wani part d'in dake sama in a circular shape wanda ya qawatu da flowers and bulbs nan taga sabyan ta hau tayi sama itama hawa tayi tareda mara mata baya wata qofar sabyan tabude suka shiga wani qayataccen falo wanda ya qawatu da setin kujeru biyu  masu kala d'aya tun daga kan welcome plasma stand kujeru center tables mini side tables komai dai na falon ya kasance grey color ne stairs suka kuma haurawa sai second falo wanda yakasance navy blue color sai bedroom da komai is white with a slight line of milky cikinsa hakama toilet da ya wadatu da big jacuzzi tub da shower room acikin da ke zagaye da glass duk wani shower gel na wanka dana wanke kai akwai shi a cikin toilet din
Sabyan tace ki gyara toilet da bedroom ni kuma in gyara two falos d'in
Sanda ta gyara toilet tsab sannan tazo ta gyara ta share bedroom d'in tayi mopping tasaka turare a burner taje dagowa taga wani frame mai dauke da hoton mutum biyu duk kayan soldiers ne ajikin su jayowa taje yi taga fuskokin su sai kuma ta maida tayi waje,,, second falon tafito ganin ba sabyan yasa tawuce 1st falon dariya ya kufce mata ganin yanda sabyan take ta sauke ajiyr zuciya amma ke kam anyi raguwa ta qarshe anan
Fad'a ki sake fad'a abun haushi ma Yaya yazo yace baiyi masa ba. Zaro ido Ihdat tayi tace duk wannan abun
Hmmm bakisan Yaya bane duk wannan shagwabar dakikaga inayi don baya nan ne amma inya dawo yana can ina nan da naga ya motsa qafa zan ranta ana kare dan nasan me zai biyo baya
Murmushi Ihdat tayi tace kedai ba'a iya miki dai dai
Zaki ganine da idonki ni muje yunwa nakeji
Acici kawai

3:30 dai dai motoci biyar suka kunno kai a gidan  da gudu sabyan tafito waje tana tarbonsa amma sai da ya kwashe kusan 10 minutes kafin ya fito a motar ga securities duk sun fiffto sun tsaya jiran sa duk sun wani zagaye motar da yake ciki
Sabyan kam ta suqu  har zata koma taga an bude mai ya fito da waya kare a kunnensa saurayi dan kimanin shekaru talatin  a duniya sanye da kayan sojoji sun matuqar karbarsa sun qara fito da haibarsa tareda kyawunsa farine fat zan iya cewa ma yafi sabyan fari dogo mai faffaden qirji I can say six pack ne dashi curly hair d'insa sai sheqi yake  ya gyara shi irin gyaran Mr kurana his cute red lips pin pointed nose , his wayfarer eyes with a brown cornea   gashin girar shi harya soma hadewa saboda cika gashi baqi sidik  yanada tsayin da baza musa shi cikin gajeru ba haka bazamu kirashi giant ba jikin shi d'an dai dai oh wow!!! Cuteness overload 
Dagudu sabyan ta isa wurin shi Yaya Naseeb welcome
Bude mata hannuwa yayi tashiga yayi hugging dinta how are you sabyan? M fine Yaya aw was ur trip ?
Weary, exhausted yafada yana yamutsa fuska 
Dariya tayi tace sorry Yaya muje in kaci abinci sai ka huta
Hmmmm how was our new home! ?
Ba dad'i Yaya I only have one friend but she's more than one to me
Hmmm yace dai dai suna shiga falo rungume mah yayi tana Masa welcome son how was ur trip?
Alhamdulillah Mah how are you and ur health? Hope you are taking ur medications ?
Yes sau uku a rana..... yayi murmushi tace je kayi wanka ga abinci
Ya wuce part d'insa wayoyinsa ya zube kan sofa dake first falon sannan yawuce zuwa bedroom lumshe ido yayi yana shaqar kamshin dakin gyaran yayi Masa sosai wanka ya shiga inda ya dauki tsawon mintuna ashirin a wurin wankan kan ya fito ya shirya cikin wando dark blue da Riga sky blue ya fesa turaruka sharp sharp ya shirya don yasoma makara salla anan yay sallah yayi adduoinsa sannan ya fito don cin abinci .....🖋️🖋️🖋️

MAIDEN {A girl servant}Where stories live. Discover now