chapter 4

100 5 2
                                    


Tun da ta gama sallar subh bata koma kwanciya ba ta tashi ta share tsakar gidan ta wanke y'an kayan su kafin ta janyo ruwa a rijiya ta shiga wanka sauri sauri tayi tafito saboda karta yi latti ya zabga mata maruka ko mai bata shafa ba tasa kaya tafito zuwa d'akin mommy
Mommyn na zaune saman sallayar da tayi salla ta shigo, good morning Mommy
Morning how are you
Lfy Alhmdllh Mommy y kika tashi tafada tana shafa kan walida da ke bacci
Lfy Alhmdllh
Mommy zan tafi ayki saina dawo
Da mamaki Mommy ta d'ago tana kallon ta tace lafiyar ki kuwa zaki fita tun yanzun!!? Tambayar da mommy tayi wa Ihdat kenan
Zama tayi kusa da mommyn tace mommy da wanda nake wa ayki ne bai dawobah shiyasa nake fita duk lokacin da naso amma yanzun kuma yadawo kuma yana fita ayki by 7:30 shiyasa zanje yanzun
Amma kam....
Mommy babu komai kimin addu'a nidai kinji bakomai fa
Murmushi Mommy tayi tashafa kan Ihdat tace Allah ya tsare min ke a duk inda kike Allah y bayyana Abbanku da Yayan ku ki kula sosai and pray before leaving the house
Ameenn Mommy InshaAllah sannan ta tashi ta kuma shafa goshin walida sannan tafita

Dakin sabyan tayi direct tasamu tana bacci tashin ta tafara yi ahnkli hey saby wake up wake up get up ina uniform ina suke
Bude ido tayi kad'an tace ki duba a wardrobe and let me sleep in peace please
Wardrobe d'in ta bude ta gansu harda ironing sabyan ta bayar an mata rigar tafara sawa don wandon irin wanda ake sawa saman riga ne tasa sannan tasa hijab d'in ganin gashin ta yafito sosai har kan mazaunanta tsaki tayi haka ta nannade tasa hijabin sai yayi kamar acuci tasa tombs din suma tayi kyau sosai ta tattara wanda ta cire tasa a wardrobe d'in tana dariyar shaqiyanci tazo kusa da sabyan da a lost in sleeping island ta saita cinyar ta ta d'ana mata duka a firgice ta tashi zaune daga baccin kiss tamata a cheek sannan tafice da gudu tana dariya har ta isa sashensa zaro ido tayi ganin 7:00am a agogon da ke kitchen d'in nashiga ukuna  da hanzari ta dafa ruwan shayi ta soya qwai tayi toasting bread ganin da d'an lokaci ta fere irish ta soya da qwai koda ta gama 7:28 ta jere komai dining ta wanke kayan da ta bata ta fara gyaran falon
Tana tsaye gaban plasma tana kakkabe kayan kallo ya sauko yana waya kallon sa yakai kanta within 3 secs ya dauke idonsa yacigaba da wayarsa yana zuba slangs English gwanin ban sha'awa
Tace toh sannu wanda ya yaye Obama batasan afili tayi maganar ba dafe baki tayi tana fad'in Allah kasa baiji ba kar ya kuma zabga min mari
Ganin ya zauna a dining tasan meyake nufi saboda haka taje da sauri don serving din shi dustern da take dusting kayan kallo riqe a hannun ta dauki serving spoon
You  fool marinta yayi sosai taji marin take hawaye ya balle mata
What type of insanity is this da wannan abun a hannu zakiyi serving d'ina come on go wash ur hands ya fad'a da tsawa

Ajiye dustern tayi akan dining zata wuce
You unbalanced creature, You suffers in mind bah! Will u take this shit away from here or... tun kan yaqarashe tazo da gudu gudu ta dauke tabar wujen
Kallon ta yake kafin ya girgiza kai yace dolty being
Wato shi daukar marar hankali yake mata ko bayan ya shata mari Allah y isana kai d'an qanqanin abu kamari mutum ko Abba da Yaya da mommy bana tina when last suka mareni amma kai jiya iyau kamin mari uku ta fashe da kuka so inhuman
Wanko hannu wanta tayi tazo tayi serving din shi kan ya Fara ci yace mata go and clean my room kallon sa tayi taga kamar bashi yayi maganar bah aranta tace iyayin banza kana wani abu kamar mace sannan ta juya ta hau stairs din da zai kai ka bedroom d'in shigarta cikin dakin tace

OMG!! What kind of filthiness is this oh Allah help me from this dirty fellow ya qware wurin cema mutum qazami alhali ga asalin qazantar anan bedroom kamar wanda mutum goma suke Zama aciki kuma akayi wata ba'a share ba kaya duk koina ga yagaggen takardu gaba d'aya komi na dakin ya canza kuma ahaka yasiya kayan daki this color dan tsabar qazanta ni wallahi dama black yasiya don shine matching color perfect colorn da zai dace da shi tana gyaran tanacewa qazami kawai qaton banza anji kunya duk wannan qaqubewar da yake yi ashe a waje ne kawai mttssww taje sanya kayan da ta ninke a wardrobe tana budewa gaba d'aya kayan cikin suka zubo kanta sai gata qasa duban kayan tayi innalillahi yanzu dan Allah meye wannan mtssw dole ta tashi ta fara sabon ayki harta gama ta fara shara aykin banza tana sharar taga hoton ranar tayi tsaye still a ranta tace induba ko kar induba no Ihdat karki duba it's not good, taci gaba da sharar ta  har ta gama gyaran ba abunda take sai zaginsa ta wanke toilet sannan ta fito falo koda tazo taga bayanan abincin ta bude taga bai wani ci da yawa ba ya rage sosai  tace kuma dan almubazaranci yace sai anyi wani girkin ta turo baki ta zauna tana imitating d'in cin abincin sa da yanda yake taba waya can kuma hawaye ya taru idonta tace nidai banaso kadai na mari na, bakada kirki ne meyasa ba haka y'an gidan ku suke bah tana shafa in da ya mareta dazu kan ta kwashi kayan tayi kitchen unknown to her duk abunda takeyi a kan idanun cctv camera don kaf gidan dakin mah da sabyan sai toilet d'in sa ne ba cctv camera amma har bedroom d'in shi akwai Saidai he's not use to watching it

Tana cikin kitchen d'in sabyan tazo dai dai zata fito suka gware
Auucchh kin fasa min kai saby
Ay so nake yafashen Allah kin cuceni dazu ina bacci na mai dad'i zaki wani dirka min duka azzaluma kawai
Dariya Ihdat keyi kamar zata shide dai dai sun shigo falon Mah dagowa yayi yana kallonta tace ke kinga yanda Kika tashi kamar wacce aka tsoma a ruwa Allah kin ban dariya dazun
Ay dole zaki yi dariya tunda kingan mugunta kuma wallahi sai na rama kuma karki qara yimin magana munyi fad'a
Yaushe kuma
Yanzun
Toh Saidai fa kiyi haquri cos I don't use to fight on Tuesdays had it been Monday ne
Mah kingan ta ko
aah ba ruwana don't put me inside anjima inganku a hade, kuma bangan komai bah
Turo baki tayi daman nasan kinfi son Ihdat ni baki sona
Zatayi magana sukayi ido biyu lokaci d'aya dariyar da take da maganar da zatayi ta tsaya sanadiyar had'a ido da sukayi ta tsaya cak tana wasa da yatsunta shiko tunani yake yaushe suka saba har haka
Mah zanje gida ne indawo ya tsinkayo muryan ta na fad'i
Mah tayi murmushi tace toh sai kin dawo ki gaishe min da mommyn ki tace toh
Dakin sabyan tashiga qaton hijabin ta tasako a kan uniform dinta tace sai na dawo saby
Sabyan tace jirani zanje
Tom and jerry inace yanzu kuka gama fad'a
Sabyan tace bazan biye ta wannan bah Mah ba sanin mutum yayi fushi tayi ba
Murmushi Ihdat tayi Mah tace toh sai kun dawo daga haka suka fita Dan wake suka tarar mommy ta dora waleeda zaune gefe tana zuba zance sabyan ma zama tayi Ihdat ko daki tawuce dan wani gajiya take ji tana shiga ta kwanta sai bacci
Baccinta take sha a nutse ba ita ta farka bah sai bayan zuhr zaro ido tayi na shiga uku na ni Ihdat da sauri ta miqe ta fito Mommy tagani zaune
Mommy shine ko kitadani ko
Ina ce kin tashi ne sai yanzu nake shirin zuwa ingani yi sallah kizo ga dan waken ki
Turo baki tayi banaci ta dau buta tayi hanyar makewayinsu
Ke lafiyar ki kuwa zaki shiga toilet da hijabi zululum zululum haka
Mommy sanyi nakeji shiyasa
Sanyi kuma da ranar nan
  Batace komai bah ta shiga ban dakin bayan ta fito tayi alwula ta shiga dakin don yin sallah
Mommy dai da ido tabita kawai bayan ta gama ta tada sabyan tayi sallah sannan ta fice daga dakin mommy dai kallonta kawai take tace mommy zan tafi sai na dawo ......🖋️ 🖋️️ 🖋️

MAIDEN {A girl servant}Where stories live. Discover now