CHAPTER 1-2

66 5 0
                                    

☘️☘️NAZLAH☘️☘️

      *DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR  CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️

*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHENSHI, SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF), WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YARDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA KARA RUFA MIKI ASIRI, DUNIYA DA LAHEERA*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
       {R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
  *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
(DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI,YAH RAB YARDA NA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA, ALLAH KASA NA KARESHI LAFIYA, ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR'ANI)



*PAGE 1-2*



               Tafe nake cikin wata Unguwa mai suna Barhim Wanda Unguwar Qauters ce,hakan yasa Unguwar bata da wata hayani ko ina tsiiit kasantuwarta na Unguwar masu kuɗi, duk in da zaka jiyo sauti to sautin karene, cikin natsuwata nake tafiya, har na ƙaraso gurin wani katafaran gida mai kyau da fasali, hayani yaji, hakan yasa na karasa jikin gidan, tura kofar nayi, jin babu wani abunda ya tokare kofar alamar gidan ba kulle yake ba yasa na tura na shiga, kofar palon da na gani bude na tunkara gadan-gadan, hayaniya najiyo  hakan yasa na dan kara tsawon tafiyata,.........

.


              ina shiga naji ana burutun, da gudu duf-duf-duf, da sauri nabi inda nakejin sautin gudun,saman benen gidan na hau, kai tsaye dakin na nufa , cikin daga sauti naji tana cewa "Wallahi Hamid baka isa ka kusance ni ba, sai ka bani kuɗin da na fada maka, in ba haka ba kuwa sai dai kayi hakuri da buƙatar ka", ta fada tana tulla mishi harara................




                Dara-daran idanunwanshi farare tas-tas masu kyan fasali da girma, ya kara buɗewa tare da cewa "yanzu ke Sadiyya dan zan anshi haƙƙina shine zaki ce sai na biyaki kuɗi, mai yasa ke kwata-kwata baki da tsoron Allah, Sadaki fa na biya aka Auramin ke bawai zaman Dadiro mukeyi da ke ba da zakice sai na biya kuɗi zan kusanceki," ya fada yana kara daura mata rinannun idanunshi akan fuskarta.............




               Jijjiga jikinta tayi, tare da cewa "Ai Wallahi bari na fada maka ka gama kusantata ba tare da ka biya kuɗi ba, kama daina yimin wani wa'azi domin tanan yake shiga yana fita tanan", ta fada tana nuna kunnuwanta.............



                Mararshi da take mishi Azababban ciwon ya dafe, tare da cewa "yanzu haka kika zaɓarwa kanki, tunda hakane, nawa kike bukata yanzun ?", ya fada idanunshi na tara hawaye ...............



                  Wani murnushi ta saki tare da cewa, "Nairah Dubu dari biyar kachal nake bukata", ta fada tana wani ƙas-ƙas da Chewing-gum din da yake bakinta, wayarshi ya dauka, ya fara latsawa kallonshi ya yi tare da cewa "Na tura miki",  yatsina fuska tayu tare da cewa "Ni banji Alert ba", ta fada tana tura dan kwalinta gaban goshinta................




                  "Ai kinsan bazance na tura miki ba Alhalin ban tura ba", ya fada ranshi na dan ɓaci, ƙas tayi tare da cewa "na sani ko karya zaka fara min", ta fada tana wani yatsina, a harzuƙe ya mike ya nufota, ganin ya nufota gadan-gadan yasa ta zura da gudu ta fita a bedroom din, wani bedroom na kusa da wannan ta shige tare da sanya key, dukan kofar ya farayi, muryarshi a dishe yake cewa "ki sani zaki kwana a cikin fushin Allah da Mala'ikunsa, kin hanani Haƙƙina sai da na  baki kuɗi, na baki kuɗin kuma zaki gujeni, ki sani haƙƙina bazai barki ba, ki bude Sadiyya, ko kinfi son naje na fadawa halaka", ya fada yana kara dukan ƙofar.........




NAZLAHWhere stories live. Discover now